✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkalin da ya soke zaben Abiola ya rasu

Allah Ya yi wa Mai Shari’a Dahiru Saleh rasuwa ranar Alhamis a garin Azare da ke Jihar Bauchi. Mai Shari’a Dahiru Saleh, wanda tsohon Babban…

Allah Ya yi wa Mai Shari’a Dahiru Saleh rasuwa ranar Alhamis a garin Azare da ke Jihar Bauchi.

Mai Shari’a Dahiru Saleh, wanda tsohon Babban Jojin Abuja ne, shi ya soke zaben 12 ga Yunin 1993 da ake ganin Cif MKO Abiola ne ya lashe shi.

A baya-bayan nan ya ce kada a zargi tsohon Shugaban Kasa Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) game da soke zaben.

A lokacin da yake kare kansa kan soke zaben, ya dora laifi kan gazawar Cif Moshood Abiola ya daukaka kara don tabbatar da zabensa a matsayin wanda ya yi nasara.

Ya ce ya soke zaben ne saboda tun farko wani alkali, Mai Shari’a Bassey Ikpeme, ya ba da umaenin dakatar da zaben ranar 11 ga Yunin 1993, amma hukumar zabe ta wancan lokacin ta ci gaba da zaben.

An  yi jana’izarsa a Babban Masallacin Azare bayan sallar La’asar.