Da Dumi Dumi

Allah Jikanka Babana

MALAM BASHIR_YAHUZA_MALUMFASHI ya rubuta wannan wake a ranar Lahadi: 28-Ramadan-1440 (BH), daidai da 02-06-2019 (Miladiyya), domin tunawa da mahaifinsa, Malam Yahuza Maiturare; wanda ya rasu shekaru 14 da suka gabata, ranar 28 ga Ramadan, 1426(BH).

Wannan shi ne mahaifina,

Ya rayu can wata rana.

 

Shi ne tsoka a ruhina,

ADVERTISEMENT

Jininsa ke tafiya a raina.

 

Shi ne ZAKARA a gidana,

Bai yo gadarar neman suna.

 

Shi ya rike kaunar mamana,

Sun shayar da ni kauna.

Ya ganar da ni kaina,

ILIMI shi ne mutuncina.

 

Ya yo kimtsi ga kargona,

Don in rikon ’yan uwana.

 

Ya yo zumunci duk rana,

Ba ya wulakanci ko raina.

 

Burinsa kowa ya yi rana,

Ba ya bakin rai mai kuna.

Yau kam babu shi BABANA,

Ya koma wurin MAHALICCINA.

 

ALLAH muke roko Ya tuna

Shi Ya ba shi ALJANNA!

 

Amin Allah karo mana,

Fatahin tallafar mahaifana!

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya