Da Dumi Dumi

Allah ne kurum Ya fitar da mu – Dokta Umar Chonoko

Dokta Umar Chonoko
Dokta Umar Chonoko

Kwana nawa ka yi kana tsare a hannun masu garkuwa da ku?

Mako daya na yi a hannunsu, domin na kai musu kudin fansa ne da nufin karbo yayana a ranar Lahadi amma sai suka rike ni.

Ta yaya kuka kubuto daga hannunsu?

Gaskiya zan ce Allah ne kawai Ya taimake mu domin akwai masu gadinmu a cikin dajin mataki-mataki amma duk da haka addu’o’in ’yan uwa da dangi da abokai da sauran jama’a sai Allah Ya kubutar da mu.

Ko za ka yi bayanin irin rayuwar da kuka yi a hannunsu a cikin daji?

ADVERTISEMENT

Rayuwa ce mara dadi ko kadan, domin ta kai ga suna yi mana wasu irin tambayoyi marasa dadi da rainin wayo kamar wai wa muka sani yana da kudi a unguwarmu da kuma neman jin kwakwaf na dukiya ko kaddarori da wanda suke tsare da shi ya mallaka a kauyensu, ba ma wanda suka gani a zahiri ba. Da kuma sauran tambayoyi marasa ma’ana. Sannan a yanzu haka dole sai na je asibiti domin a duba lafiyata saboda gaskiya sauro sun cije mu da yawa. Tunda a waje muke kwana sannan wajen kamar yana kan tsauni ne ga sanyi. Duk irin rigar da ka sa dole sai ka ji sanyi sai kuma na yi rashin sa’a, rigar da nake sanye da ita ’yar shara-shara ce.

Ba ni da wani mayafi, haka zan kwanta a kasa, wani lokaci sai mu shimfida ganye a kasa mu kwanta a kai. Idan suka ga dama kuma su hana mu kwantawa a kan ganyen, saboda wasu lokuta suna cikin maye. Don haka sai su ce babu dalilin su bar mu mu shimfida ganye mu kwanta. Idan kuma ka ki suna iya wulakanta ka.

Me ya faru a ranar da ka je kai musu kudin?

Da na je can a ranar Lahadi sai muka wuce inda yayana yake, domin in biya kudin fansa in karbe shi. Da na isa wurin da yake na tarar da shi ne da wani mutum da suke garkuwa da shi a daure. Su biyu kurum ni kuma daga zuwa ni ma sai suka rike ni. Sai muka koma mu uku a sansanin. Bayan kwana biyu sai suka kwashe mu zuwa wani sansanin, inda muka sake tarar da wadansu mutum biyu a daure, fuskarsu duk a rufe da kyalle. An kuma daure su a jikin bishiya har da kafafunsu.

Yaya aka yi kuka kubuta?

Ikon Allah ne kurum saboda mun yi addu’a matuka a kan samun nasara kafin mu dauki wannan mataki mai wahala. Domin da sun fahinci wannan shiri namu, Allah kadai Ya san abin da za su yi mana amma da yake mun karanci yadda masu gadin suke sai Allah Ya taimake mu.

Ko jami’an tsaro sun taka rawa wajen kubutar da ku?

Abin da kurum na sani shi ne, lokacin da aka sace yayana na kai rahoto ofishin ’yan sanda na Afaka, domin su san halin da ake ciki. Tun daga nan ban san ko wace rawa suka taka ba, domin ka san kowa ta kansa kurum yake yi.

Yanzu ga shi Allah Ya dawo da kai, yaya kake ji?

Muna godiya ga Allah. Ikon Allah ne kurum Ya fitar da mu. Mun tarar da iyali da ’yan uwa, a yanzu muna cike da murna da mika godiya ga Allah da kuma sauran jama’a.

Share