✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa Shugaban Asibitin Jinya na Kaduna rasuwa

Allah Ya amshi ran Dokta Tukur Abdullahi da maraicen shekaranjiya Laraba, bayan ya yi jinya ta kwana goma. Likitan, wanda kafin rasuwarsa shi ne Shugaban…

Allah Ya amshi ran Dokta Tukur Abdullahi da maraicen shekaranjiya Laraba, bayan ya yi jinya ta kwana goma.

Likitan, wanda kafin rasuwarsa shi ne Shugaban wani asibiti mai zaman kansa mai suna Jinya Specialist Hospital da ke Kaduna. Ya rasu ne yana da shekara 83 a duniya. Ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya 16 da jikoki da dama, cikinsu har da babbar ’yarsa, Hajiya Hannatu Tukur Abdullahi, ma’aikaciya a Gwamnatin Jihar Katsina.

Marigayin, yaya ne ga Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi, Mai shari’a Saddik Abdullahi Mahuta. Lokacin rayuwarsa ya yi aikace-aikace a hukumomin lafiya daban-daban na Gwamnatin Tarayya da tsohuwar Jihar Kaduna, inda ya rike mukamin Kwamishina (Minista) a ma’aikatu daban-daban a Gwamnatin Tarayya, zamanin mulki Janar Murtala Mohammed da kwamishina a tsohuwar Gwamnatin Jihar Kaduna. Ya shugabanci kwamitoci daban-daban da suka danganci al’amuran lafiya a matakin Tarayya, cikinsu har da na tsarin Inshorar Lafiya na Gwamnatin Tarayya. Kuma shi ne shugaban kwamitin da ya assasa gina manyan Asibitocin Gwamnatin Tarayya (Federal Medical Centres).

Marigayi Dokta Tukur, wanda aka fi sani da ‘Malam’ mutum ne mai hakuri da kishin addinin Musulunci. Marubucin wakokin fasaha na Hausa, inda kafin rasuwarsa ya wallafa kundin wasu daga cikin wakokinsa mai taken “Wakokin Najeriya” wanda Kamfanin Dab’i na ABU Press Zariya ya wallafa a shekarar 2012.

An yi jana’izarsa a jiya Alhamis a Malumfashi, Jihar Katsina da misalin karfe 4;00 na maraice bisa tsarin Musulunci. Allah Ya jikansa da rahama, amin.