✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Almajirai 16 da aka mayar Kaduna daga Kano suna da Coronavirus

Almajirai 16 da suka taho daga Kano, an same suna dauke da cutar coronavirus bayan sun shiga Kaduna, wanda hakan ya sa adadin almajirai 21…

Almajirai 16 da suka taho daga Kano, an same suna dauke da cutar coronavirus bayan sun shiga Kaduna, wanda hakan ya sa adadin almajirai 21 ke dauke da cutar a Jihar Kaduna.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya NCDC, a ranar Laraba ta sanar da samun karin mutum 17 masu dauke da cutar, sai dai Kwamishinar Lafiya ta jihar, Dokta Amina Mohammed-Baloni, ta ce ainihin sabbin wadanda suka kamun mutum 16 ne.

An yiwa mutum 17 gwaji tun da farko, kuma gwamnatin jihar ta ankarar da hukumar NCDC game da hakan. Kwamishinar ta tabbatar da gwajin da aka yi wa almajiran 16 da suka shiga jihar daga Kano ya nuna suna dauke da cutar – wanda hakan ya kawo adadin masu fama da cutar a jihar Kaduna ya haura daga tara zuwa 25.

“Yawaitar samun masu dauke da cutar da suka taho daga bulaguro daga wasu jihohin — ya tabbatar da fargabar da gwamnatin jihar ke yi cewa akwai yiwuwar yada cutar daga makwabtan jihohi da kuma yadda zirga-zirga tsakanin jihohin ke taimaka wa wajen bazuwar cutar,’´ inji ta.

Kwamishinar, ta kara da cewa a yunkurin dabbaka matakan kare yaduwar cutar, jami’an lafiya na sanya ido sosai kan wadanda suka sulalo suka shiga jihar kuma ake zargin suna dauke da cutar – duk da dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohin.

Aminiya ta ruwaito cewa, gwamnatin jihar a ranar Litinin ta sanar cewa mutum biyar din da aka samu suna dauke da cutar a jihar almajirai ne – da aka dawowa dasu daga Kano.

Jihar Kaduna dai ta sallami masu fama da cutar har mutum shida – wadanda suka warke daga cutar coronavirus – ciki har da gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai.