Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Almajirai na iya samun ilimi ba tare da bara ba – Malam Bashir

Malam Bashir Lawal

Malam Bashir Lawal shi ne Shugaban Makarantar Ma’ahad, kuma Na’ibin Limmin Masallacin Juma’a na Sheikh Dalhatu As’salafi Tudun Jukun Zariya. A tattaunawarsa da Aminiya ya ce almajirai na iya samun ilimi ba tare da sun yi bara ba da sauran batutuwa:

Me ya sa ka yi huduba kan matsalar bara da al’majiranci da wadansu ke dauka kamar ibada?

ADVERTISEMENT

Almajiranci da bara matsaloli ne da a yau ’yan jarida da malaman addini da sauran mutane suke ta tattaunawa a kansu. Bara da almajiranci abubuwa ne da suke haduwa a wani lokaci, wani lokacin kuma su rabu, domin ba dole ba ne idan akwai almajiranci, ya zama akwai bara to amma yanzu sun hade har ya zama ba a iya raba tsakanin bara da almajiranci. Amma ya kamata al’umma su san bambancin bara da almajiranci. Bara shi ne rokon mutane abin da mutum yake ganin idan aka ba shi zai iya toshe masa matsalolin rayuwarsa ko magance masa wata matsala ta rayuwarsa.

A tarihin Najeriya bara ana iya cewa tsohuwar matsala ce sabuwa, domin masu bincike sun cewa kafin jihadin  Shehu Usman Dan Fodiyo babu bara a kasar Hausa. Wadansu masu binciken kuma sun ce bara ta fara ne bayan zuwan Turawan mulkin mallaka, wadanda suka dauki ilimin addini a matsayin makaskanci abu, malaman addini suka zama ba su da galihu, kuma ba su da wani abu da suke samu daga gwamnati.

ADVERTISEMENT

A da tsarin da ake bi shi ne idan alaramma ya kafa tsangaya to zai zama dukkan mahaifin da zai kawo dansa, yaron zai fara ne daga matsayin tittibiri ko kolo har lokacin da zai kai matsayin da ake kira gangaran ko alaramma, to mahaifin zai rika kawo masa kayan abinci. Sannan lokaci bayan lokaci zai rika kawo wa dansa ziyara ya ga halin da yake ciki, kuma ya yi wani abin hasafi ga malamin. Wannan tsari idan mun kalle shi za mu ga ya yi kama da tsari irin na makarantun kwana na boko.

Sai iyaye suka manta da wajibin da Allah Ya dora musu na ba ’ya’yan da suka haifa tarbiyya, sai su rika daukan ’ya’yansu suna kai su almajiranci.

Malamai kuma suka ga cewa ba za su iya daina wannan hanyar ta karantarwa ba sai suka fito da sabuwar hanya ta duk wani yaron da mahaifinsa ya kawo shi makaranta domin karatu, ba zai kawo shi da komai ba. Daga nan wani ma ba zai kara ganin dansa ba sai dai ranar da za a kawo masa gawar dan ko wata annoba ta zo sai a kawo wa mahaifinsa shi, ko ya ji labarin cewa dansa ya rasu.

Ka ji halin da muka tsinci kanmu da sunan almajiranci a yau ke nan, sai dai kadan ne daga cikinsu suke kwatanta irin wancan tsohon tsari na da

Akwai kasar da ake bin wannan tsari na almajiranci da bara kamar yadda ake yi a Arewacin Najeriya?

Ko rantsuwa ka yi a kan babu inda ake bara a duniya sai Najeriya musamman Arewa ba kaffara, baya ga Nijar da Chadi. Idan kuma an fadada a ce Arewacin kasar Kamaru, wato kasashen da suka fi makwabtaka da mu.

Idan ana son canja tsarin wace hanya kake ganin za a bi?

Akwai wani tsari da wasu kasashen Larabawa suke da shi wadanda kuma ba su da wadata kamar kasar Yemen inda sai an hau saman dutse za ka tarar da tsangayar almajirai da yawansu ya kai dubu biyu ko uku, amma dukkansu babu wanda yake bara ko roko. Kuma za ka same su a ckin kyakkyawar yanayi, haka kuma yake a Sudan, ana kiran wajen da sunan Halwat ana tara yara masu yawa a ba su karatun Alkur’ani. Kuma a nan kasar akwai iyaye da yawa da suka dauki ’ya’yansu suka kai su Sudan suka yi hadda, kuma hadda gangariya ba tare da sun taba yin bara ba. Akwai irin wannan tsarin a kasar Pakistan da Malesiya.

A kasar Muritaniya su ba ma karatun Alkur’ani ba, har karatun litattafai rubutawa ake yi a allo. Kuma yaro zai gama ya zama babban malami ba tare da ya taba yin bara ko rokon kowa wani abu ba.

Sai kuma nau’in bara na biyu da nakasassu suka fi yi. Akwai kuma wadanda suke fakewa da ciwo su yi bara. Akwai kuma wadanda suke bara da sunan talauci, sai ka ga mutum lafiyarsa kalau wanda ba abin da ba zai iya yi ba, amma sai ka gan shi yana neman taimako.

Sai nau’in bara da sunan tumasanci, ko fadanci, ko bambadanci, wadanda suke tarewa a gidan masu dukiya suna kuranta su da fadin wani abu a kansu domin su dauki wani abu su ba su, shi ma bara ne.

Malam mene ne matsayin bara a Musulunci?

Bara a Musulunci haram ne da nassosin hadisai kuma ta kowace siga daga cikin sigogin da muka ayyana a baya. Amma kuma akwai ka’ida ta addinin Musulunci da take halatta saboda lalura, amma ita kanta lalurar tana da ka’ida, domin kamar yadda shari’a ta ce za a iya cin mushe, to ba cewa aka yi  ka yi ta yawo da shi ba. Malamai cewa suka yi bayan ka ci babu laifi ka dauka har ka sa a jaka amma da ka fita daga wannan hali na matsi ko na lalura sai ka haka rami ka binne don kada wani ya dauka ya ci.

Don haka bara tana da hali da shari’ar Musulunci take halatta a yi, inda Allah a cikin Alkur’ani Mai girama Yake siffanta masu imani da cewa wadanda a cikin dukiyar da Allah Ya ba su suka san cewa akwai wani sanannen yanki da shari’a ta ware ta ce a ba wanda ya zo ya yi bara cewa yana cikin lallura ko matsi da kuma wanda ya haramta wa kansa yin bara alhali kuma yana cikin matsi. Wani idan ka dubi ’ya’yansa za a iya gane cewa ya shiga cikin matsi, ko mutumin da jarrabawa ta fada masa shi ma ya halatta su yi bara har su fita daga wannan jarrabawa.

Miskini ko talaka ko matalauci na sosai wanda ba ya da abin da zai iya biya wa kansa bukata sannan ba ya bara, kuma bai fada wa kowa ba, kuma bai matsa wa mutane, amma mutane da sun gan shi za su iya gane cewa da alama yana bukatar taimako to ya halatta a taimaka masa. Mutumin da yake fita a kullum matukar za ka iya nemo abin da za ka ci kamar ci uku to ba ya halatta ka yi bara, idan kuma kai mawadaci ne wato mai juya kudi ne kamar dan kasuwa ko ka mallaki akalla Dirhami 50, to idan kana da wannan jarin ba ya halatta ka je ka yi bara.

Manzon Allah (SAW) ya ce duk wanda yake bara to yana tambayar mutane  ne garwashin wuta, idan ya gadama to ya ci gaba da rokon mutane don ya yawaita garwashinsa na Jahannama.

Sannan akwai zubar da kimar addinin Musulunci musamman wajen abokan zamanmu domin abin da suke fassarawa shi ne ai wadannan Musulumi ne, kuma Musulunci ne ya ce su yi bara, alhali Musulunci ba ruwansa da bara da almajiranci. Kuma a cikin almajirancin nan wadansu na koyo munanan dabi’u da ba a sansu ba tare da koyar da rashin tausayi.

A karshe ina mafita?

Masu dukiya su ji tsoron Allah akan dukiyar da Allah Ya ba su wajen fitar da zakka, don yana daga cikin tsari na Musulunci a samar da hukumar tattara zakka da raba ta ga wadanda suka cancanta. Zakka tana da matsayi na musamman wajen rage matsalolin matsi da al’umma suka samu kansu a ciki.

Gwamnati ita ma ta ji tsoron Allah domin ba a hana mutane yin almajranci ko hana su yin bara har sai an samar musu da abubuwa biyu. Na farko gwamnati ta ba kowa aikin yi domin hakkinta ne a mahanga ta Musulunci. Na biyu idan babu aikin yi da gwamnati za ta samar wa al’umma to akwai ofishi na musamman da gwamnatin Musulunci take da shi na kula da daukar nauyin wadanda suka gaza. Sai gwamnati ta samar da irin wannan waje kafin daukar  matakin hana almajiraci ko bara.