Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Al’ummar Abbare a Taraba suna neman dauki

Al’ummar garin Abbare da ke Karamar Hukumar Lau a Jihar Taraba sun koka kan yadda wasu mutane ke sanya kayan soja suna barazanar hallakasu.

Al’ummar sun bayyana hakan ne a wata takardar da suka rubuta dauke da sa hannun mai maganda yawun mutanen garin, Alhaji Muhammed Sale, inda ya bayyana cewa wasu gungun mutane da ba a san su waye ba, suke zuwa sanye da kayan sojoji su kashe musu shanu, inda yanzu haka sun kashe shanu sama da 100 sannan kuma sama da 500 suka bata.

ADVERTISEMENT

Ita dai wannan takarda, sun mika ta ne ga Hedkwatar Sojojin Najeria da ‘Yan sanda da jami’an tsaroon farin kaya, inda suka nemi a gudanar da binckie a kan lamarin.

ADVERTISEMENT