Da Dumi Dumi

Al’ummar Afirka ta kudu sun dukufa wajen yi wa Mandela addu’a

Al’ummar Afirka ta Kudu sun dukufa wajen yi wa tsohon Shugaban kasa, Nelson Mandela addu’ar neman samun sauki, a lokacin da ya shafe kwanaki yana kwance a asibiti. Wasu kuwa kira suke yi ga iyalansa da gwamnatin kasar kan lallai su kyale shi “ya tafi (makoma).”
Jami’an gwamnati ba su da cikakken bayani game da halin da lafiyarsa take ciki, tun bayan da aka kwantar da wannan dattijo dan shekara 95 a asibiti, ranar Asabar din da ta gabata, bayan ya yi fama da ciwon huhu.
“Na ga mahaifina, ya samu lafiya. Kuma shi mai fafutika ne,” a cewar  ’yarsa Zindzi, a hirar da ta yi da jaridar The Guardian ta Landan a ranar Lahadin da ta gabata.
Sai dai mafi yawan al’ummar Afirka ta Kudu sun fara sakankancewa kan lallai shugaban kasarsu bakar fata na farko yak us akai ghargara, musamman ganin yadda ya yi fama da rashin lafiya.
Kafafen Yada labarai da kamfanonin dillancin labarai na duniya, wadanda suka hada da BBC da AFP da Reuters duk hankalinsu ya karkata kusan kashi 90 cikin 100 zuwa asibitin da aka kwantar da Nelson Mandela. Don haka gwamantin kasar ta tsaurara matakan tsaro a asibitin. Su kuwa likitoci suna ta fafutikar ganin sun shawo kan cutar huhu da addabe. Wannan cuta dai ya kamu da ita ne, tun lokacin da aka daure shi a tsibitin Rhodes, a daidai sa’adda yake ganiyar fafutikar kwato hakkin bakaken fata, a karkashin tutar jam’iyyarsu ta ANC.

Share