✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Bassa sun bukaci INEC ta takatar da zabe a Karamar Hukumar Toto

Kabilar Bassa da ke Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa ta bukaci Hukumar INEC ta dakatar da gudanar zabubbukan da ke tafe sai gwamnatin jihar…

Kabilar Bassa da ke Karamar Hukumar Toto a Jihar Nasarawa ta bukaci Hukumar INEC ta dakatar da gudanar zabubbukan da ke tafe sai gwamnatin jihar ta tabbatar da zaman lafiya a yankinsu.

Babban Sakataren Kungiyar Ci gabar Al’ummar Bassa ta Kasa, Mista Gwatana Dogwo ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Lafiya, inda ya ce kiran ya zama wajibi inda ya ce a yanzu kusan dukan al’ummarsu ta Bassa da ke yankin sun bar gidajensu suna gudun hijira a wasu garuruwa a ciki da wajen jihar sakamakon hare-hare da  ake kai musu tun bara

Ya ce “A madadin al’ummar kabilarmu ta Bassa da ke Karamar Hukumar Toto ina bayyana wa duniya cewa ya kamata gwamnati ta kawo karshen kisar kiyashi da ake yi mana tun bara. Kawo yanzu mun yi asarar rayuka da dukiyoyi da dama. A yanzu kusan dukan kauyukanmu babu kowa, duk muna gudun hijira a wasu wurare daban. A kan haka ne ma muke kira ga Hukumar INEC ta dakatar da zabubbuka a yankin Karamar Hukumarmu ta Toto baki daya. Don idan aka yi haka ba a yi wa al’ummarmu da yankinmu adalci ba. Maimakon haka ya kamata gwamnatoci a dukan matakai su gaggauta yin duk mai yiwuwa wajen dawo da zaman lafiya da tabbatar da cewa al’ummarmu sun dawo gidajensu daga inda suke gudun hijira kafin a gudanar da zabubbukan.”