✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Kudancin Kaduna sun bayyana musabbabin rikicin yankin

Shugabannin al’umma a yankin Kudancin Kaduna sun ce musabbabin rikicin da ya haifar da hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 15 da jikkata 24…

Shugabannin al’umma a yankin Kudancin Kaduna sun ce musabbabin rikicin da ya haifar da hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutum 15 da jikkata 24 a Unguwar Pah II da ke kauyen Gwandara a Karamar Hukumar Jama’a, sun faru ne dalilin kashe wadansu Fulani biyar da aka yi a watan Nuwamban da ya gabata.

Binciken da Aminiya ta gudanar a yankin, ya gano cewa kusan shekaru biyu da suka wuce ake zaman dardar sanadiyyar wani rikici da ake yi a tsakanin wadansu makiyaya da wani manomi da ake kira Balat, wanda ake zargi da haddasa rikicin, wanda zuwa lokacin hada wannan rahoton ya arce daga garin.

Yayin da yake yi wa Aminiya karin haske, Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Karamar Hukumar Jama’a, Alhaji Abdullahi Bayero ya ce asalin rikicin ya shafi wadansu mutane ne kawai a tsakaninsu wanda ya yi sanadiyyar kisan wani dattijo mai kimanin shekara 60 mai suna Yakubu Musa a kauyen Dogon Awo da ke Kogum a masarautar Godogodo da ke karamar hukumar a ranar 26 ga Nuwamban bana.

“Daga baya sai wadansu matasan yankin suka auka wa wata Rugar Idris a ranar inda suka kashe wadansu kananan yara biyu; Shu’aibu Idris dan sheakara 9 da Balki Idris, ’yar shekara 7,” inji shi.

Ya ce nan take macen ta rasu yayin da namijin ya karasa a asibiti. “Matasan ba su daddara ba sai suka sake tare wadansu matan Fulani tsofaffi da suka yiwo hayar babur su biyu, bayan sun taso daga Rugar Alhaji sun iso daidai kauyen Gindin Dutse sai matasan wurin suka rufar musu, suka kashe matan Fulanin masu suna Doka Alhaji Ahmadu da Asiya Alhaji Ahmadu da dan acabar da ya dauko su mai suna Abubakar Abbas, dan asalin Jihar Jigawa da ke zaune a Kogum, kuma bayan sun kashe su suka jefa gawarwakinsu a wata tsohuwar rijiya suka toshe bakinta,” inji shi.

Ya ce sai da sojoji suka kama wadansu masu unguwanni a yayin binciken, kafin a gano rijiyar da aka jefa su, aka haka aka fito da su. Masu unguwannin da aka kama su ne, Habila Dogara da Duniya Biya da Ibrahim Ali da kuma Gora Bako Nkom.

Alhaji Ilyasu Musa, shi ne Sakataren Kungiyar Jama’atu Nasril Islam na Karamar Hukumar Jama’a da Kudancin Kaduna, kuma mamba a Hukumar Zaman Lafiya ta Jihar Kaduna (Kaduna Peace Commission), ya ce ya halarci tonowa da ciro gawarwakin a cikin rijiyar.

“Kuma da ni aka yi jana’izarsu a garin Jagindi Tasha bayan sojoji sun mika wa ’yan sanda gawarwakinsu kuma sun mika ga Kungiyar Miyetti Allah,” inji shi.

Da Aminiya ta tuntubi Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), reshen Karamar Hukumar Jama’a, Rabaran Ben Ayuba ya tabbatar da faruwar hakan, inda ya kara da cewa sanadiyyar haka suka shirya tarurruka da fastoci da limamai da shugabannin Fulani da Kungiyar CAN da kuma Jama’atu Nasril Islam a garin Godogodo kuma suka sake shirya wani shiri a gidan Rediyon Salama da ke Kafanchan don yin kira kan zaman lafiya.

“Al’ummar Fulani sun yi mana alkawarin cewa babu wani abu da zai faru kuma suka bukace mu da mu sanar da su idan wani abu zai faru, wanda hakan ya sa muka ji dadi sai daga baya muka ji wannan harin,” inji shi.

Rabaran Ben, ya yi kira ga gwamnati ta yi kokari ta kama wanda ake zargi wanda a sanadiyyarsa ne wannan rikicin ya sake kunno kai mai suna Balat, don fuskantar hukunci.

Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Peter Danjuma Aberick da Shugaban Kungiyar Miyetti Allah reshen Kudancin Kaduna, Alhaji Abdulhamid Musa da shugabannin CAN da Jama’atu duka sun yi kira ga kowa da a zauna lafiya domin jami’an tsaro sun bazama wajen neman duk wadansu masu hannu a tayar da dukan rikicin da ke faruwa.