Search
Subscribe
Al’ummar Kundulum sun gudanar da addu’o’in gode wa Gwamna Inuwa kan gina musu hanya

Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe

Al’ummar Kundulum sun gudanar da addu’o’in gode wa Gwamna Inuwa kan gina musu hanya

Al’ummar Kundulum a Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe sun jinjina wa Gwamnan Jihar, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, bisa ba da aikin hanyar da ta tashi daga Unguwar Arawa ta wuce Malam Inna ta isa Wuro-Kesa zuwa Kundulum har garin Kurba mai tsawon kilomita 11.5.

Aikin hanyar shi ne na farko da Gwamnan ya bayar a hawansa mulki kuma hanyar za ta lashe Naira biliyan 1 da miliyan 700. Gwamnatin Ibrahim Hassan Dankwambo ta ba da aikin hanyar a baya  ba tare da biyan ’Yan kwangila ba; kana ta yi watsi da ita tun a shekarar 2017.

Al’ummar Kundulum sun yi wannan jinjina ne a lokacin da suka gudanar da addu’a  don godiya ga Gwamna Inuwa Yahaya bisa aikin wannan hanya da suke neman a yi musu tun iyaye da kakanni.

A jawabin Hakimin Kundulum, Malam Shu’aibu Muhammad, ya yaba wa  Gwamna Inuwa Yahaya kan yadda ya zabi al’ummar yankin Kundulum a matsayin na farko da za su fara shaida aikin hanya a mulkinsa; inda ya roki a samar musu da ababuwan more rayuwa, kamar ruwan sha da wutar lantarki da sauransu har zuwa yankunan da ke makwabtaka da su.

A nasa tsokaci, Babban Limamin Kundulum Malam Haruna Sale, cewa ya yi sun shirya wannan addu’a ta musamman ce don nuna farin cikinsu ga Allah da kuma Gwamna Inuwa Yahaya bisa wannan aikin hanya da suka shaida; wanda suka jima suna neman a yi musu.

Walin Kundulum Malam Ibrahim Shu’aibu kuma kira ya yi ga Gwamnan ya ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka na raya kasa; sa’annan ya nemi ya hada kai da Hukumar Ayyukan Raya Kasa (CSDP), domin samar da wasu ayyukan inganta rayuwar jama’a a tsakanin al’ummar jihar.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin