✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Nijeriya cin buri a kan Janar Buhari ba namu ba ne (2)

Ci gaba daga makon jiya Babu shakka mulkin Jam’iyyar PDP na shekara 16 ya kusan kai kasar nan ga halaka, kuma jiki magayi koda wani…

Ci gaba daga makon jiya

Babu shakka mulkin Jam’iyyar PDP na shekara 16 ya kusan kai kasar nan ga halaka, kuma jiki magayi koda wani bai fada mana ba, jikinmu yana gaya mana cewa al’amura sun kai magaryar tukewa wajen tabarbarewa da lalacewa.
Babu tsaro ga talaucin tsiya sun dabaibaye mu a kasar nan, ta yadda muna rayuwa ne kamar a gandun dabbobi. Galibin mutane ba su san inda suka fito ba, ba su san ina za su je ba. Kowa ka gani hankalinsa ba a jikinsa yake ba. Mutane na neman wani maceci da zai kwato su daga wannan bakar jarraba wato PDP wadda Allah ya ara mata dama na tsawon shekara 16 amma ta kasa yin amfani da damar don inganta makomar kasar nan. Yadda al’amura suka kazance a lokacin mulkin PDP, musamman a zamanin Shugaba mai barin gado, Jonathan abin akwai ban tsoro, domin mun kai wani mataki da kowanenmu yake fita daga gida ba tare da tunanin zai iya komawa gida da rai ba.
To, amma fa abin da ya kamata a sani ba zaben Buhari ne kawai zai canja halin da muke ciki ba, matukar galibin jama’a ba su gyara halinsu sun tsarkake zukatansu tsakani da Allah ba, tilas ne kowanenmu ya daura aniyar fara gyara daga kansa. Akwai abubuwan da ba gwamnati ko Shugaba ne zai zo ya gyara mana ba. Yadda kowanenmu yake gudanar da mu’amalarsa a tsakaninsa da iyalinsa da yadda yake yi da makwabtansa da mutanen unguwarsu da wuraren harkokinsa, ba Shugaba ne zai tsaya a kansa ya ce ya yi abin da ya dace ba. Imaninsa da Allah da hukunce-hukuncensa zai yi amfani da su wajen yin abin da ya dace ko akasin haka. Abin da Shugaba ko Gwamna ko gwamnati za ta shigo ciki shi ne idan mutum ya ketare iyaka a huldarsa da abokan zamansa ya kai ga shiga hakkinsu da doka ba za ta iya lamunta ba. Ya ya Buhari zai yi da kai idan a boye kana tauye mata da ’ya’yanka saboda kai ne mijinsu ko mahaifinsu? Ina ma zai samu labarin abin da kake yi? Alhamadulillahi yanzu jama’a sun fara nuna wa barayin gwamnati da suke zuwa da kudi suna rabawa ga Shugabannin jam’iyyu da jami’an tsaro da Sarakuna da malaman addini domin su murde zabe. Zai yi kyau nan gaba jama’a su rika nuna musu kyama. Ban yarda da masu cewa idan barayin siyasa suka kawo muku kudi ku karba ku ki zabensu ba. A’a duk wanda ya kawo muku kudi don yana son kau zabe shi, ku gaya masa a idonsa cewa ba za ku karba ba. Ku gaya masa cewa kun gaji da bakin mulkinsa da sata. Ku shaida masa a kan idonsa cewa za ku gwammace ku mutu da talauci domin ’ya’yanku da jikokinku su samu ’yanci daga bakin mulkin da ke cike da sakaci da tsaron rayuka da dukiyar jama’a. Ku shaida masa gwanda talauci ya kashe ku domin ’ya’yanku su samu damar da za su yi karatu su samu aikin yi da ku karbi kudinsu da zai tabbatar da ku a cikin talauci.
Akwai wajibcin mu fara fitowa muna nuna wa ’yan siyasa da masu mulki zababbu da nadaddu cewa, dukiyarsu ta haram da suka tara ta handama da cuta da karya, ba ita muke bukata ba.Muna bukatar a kare mana rai da dukiya da addini da mutunci fiye da naira ko dalar da suke dofara mana.
Siyasa lamari ne da ke bukatar mutane na kwarai, saboda da ita ake yin mulki, amma sai yanzu ta zama wulakantacciyar sana’a, duk wani mugu sai ya ce shi dan siyasa ne, ya yi ta raba kudi a zabe shi, sai abin da hali ya yi. Mulki shi ne karshen karfi na yin gyara ko barna saboda haka bai kamata a danka mulki a hannun mabarnaci ba, Basidi ko hauhabu ko murakkabu duk wata amanarmu, ya kamata mu nema mata ahlin da ya dace da ita, musamman amanar rayukanmu da lafiyarmu da dukiyarmu da mutuncinmu da addininmu. Duk wanda ba ya jin tsoron Allah, ba ya jin kunyar mutane bai kamata a ji tsoronsa ba, balle ma a ji kunyarsa.Duk abin da yake tinkaho da shi Allah ya fi shi, ko wane ne shi, ko dan wane ne. Allah ne kadai abin tsoro.

Anas Saminu Ja’en
Mataimakin jami’in hulda da jama’a na kungiyar Muryar Talaka
Reshen jihar Kano
07033882307