Search
Subscribe
Amarya ta kashe mijinta don ya hana ta kallon fim

Amarya ta kashe mijinta don ya hana ta kallon fim

A ranar Larabar makon jiya ne wata amarya mai suna A’isha Idris da ke zaune a Unguwar Jahun a Bauchi ta kashe mijinta saboda ya hana ta kallon fim din Hausa ya ce ta tashi ta yi sallah, lamarin da ya sanya ta watsa masa tafasasshen ruwa daga bisani Allah Ya yi masa rasuwa.

Wakilinmu ya yi tattaki zuwa gidan marigayin inda ya zanta da kanin wanda aka kashe mai suna Sani Muhammad Ladan, inda ya bayyana masa cewa, ‘’ Ni kanin marigayi Muhammed Auwal Ladan ne wanda matarsa A’isha ta halaka shi a ranar Larabar makon jiya, muna fata Allah Ya gafarta masa. Abin da ya faru shi ne, a ranar Laraba da misalin karfe 7 na dare, bayan da ya shiga cikin dakinta sai ya same ta tana kallon fim din Hausa, sai ya ce mata ta tashi ta yi sallah, sai ta ki, sai ya sanya hannu ya kashe (DbD) din, ya cire sidin ya karkarya, sai ya dauki DbD din ya sanya a cikin dakinsa.’’
‘’Daga nan sai ta fara zaginsa, da ya juya zai fita daga cikin dakin, sai ta dauko wani bokiti cike da ruwan zafi ta watsa masa, nan take ya fadi. Da mutane suka taru sai ta fita daga cikin gidan ta gudu zuwa gidan wani dan uwanta, daga bisani mutane suka je gidan inda suka fito da ita aka mika ta ga rundunar ‘yan sanda ta Jihar Bauchi.’’
Sani Ladan ya ci gaba da cewa, ‘’Yau kimanin watanni tara ke nan da aurensu, kuma ita ce matarsa ta farko a duniya, lokacin da aka yi auren suna zaune lafiya babu wata matsala a tsakaninsu, domin auren soyayya suka yi. Amma abin da ya faru ya daga hankalin duk wani mutum da ke zaune a cikin garin Bauchi. A nan cikin garin Bauchi ya aure ta. Kuma bayan da abun ya faru babu wani daga gidansu da ya zo domin yi mana jaje, kodayake lokacin da za a yi masa sallah akwai wani daga gidansu da ya zo amma aka ce masa ya bar wajen saboda dalilai na tsaro.’’
‘’Marigayin yana da mota da yake tukawa zuwa jihohi daban-daban, yana daukar mutane daga Bauchi zuwa Abuja zuwa Kano da Gombe da makamantansu, kuma kowa ya san cewa yana zaune lafiya da matarsa.’’
‘’Saboda haka a matsayina na kaninsa, ina kira da babban murya ga mazajen da suke barin matansu suna kallon fina-finai su shafa wa kansu ruwa, domin mun ga irin illar da hakan ya jawo a gidan nan, inda aka kashe mana babban yayanmu saboda fina-finan hausa.’’
Sani Ladan ya ce, ‘’ shekarun marigayi Muhammad Auwal 30 ne da wani abu, ita kuma matarsa shekarunta 18 ne, kuma lafiyarta kalau ba ta da wata matsala ta tabin hankali. Kafin ta watsa masa ruwan zafi shi ne ya kira sallah a kofar gidanmu, bayan da ya koma cikin gida ne ya hadu da wannan jafa’in, inda daga bisani aka garzaya da shi zuwa asibiti a nan ne ya cika.’’
‘’Muna zaune a Jahun ne a bayan gidan limamin Bauchi. Mahaifinmu ya ce babu wani mataki da za a dauka a kan A’isha, domin duk wani matakin da za a dauka ba za a taba dawo da Auwal duniya ba. Amma akwai wadansu daga cikin mutanen gidanmu da suka bayyana cewa ba za su taba yafe mata ba, dole sai sun dauki fansa, amma za mu cigaba da kwantar musu da hankali domin a bar komai ga Allah.’’
‘’Mahaifin Aisha ba ya da koshin lafiya, lokacin da ya samu labarin abin da ‘yarsa ta aikata ya shiga cikin mawuyacin hali. Kuma har zuwa wannan lokacin nan da muke zantawa da kai Aisha tana hannun ‘yan sanda, inda suke cigaba da gudanar da bincike. Mahaifiyarta ta fito ne daga Fadan Karshi da ke kan iyakar jihohin Kaduna da Nasarawa.’’
A karshe ya shawarci magidanta da cewa, ‘’lokaci ya yi da ya kamata su maida hankalinsu wajen neman ilimi maimakon kallon fina-finan da yake lalata tarbiyyar al’umma. Mun samu tabbacin cewa A’isha tana matukar son fim din Ali Nuhu.’’
Usman Adamu wani mazaunin Unguwar Kuka ne a cikin garin Bauchi da ya san mahaifin A’isha, ya bayyana wa wakilinmu cewa mahaifin A’isha Idris yana zauna ne a garin Jagur da ke yankin karamar hukumar Bauchi, kuma a can ne aka daura musu aure. Daga bisani Usman ya ba wakilinmu lambar wayan mahaifin A’isha Idris, amma an buga wayar a lokuta daban-daban ba a same shi ba.
Lokacin da A’isha ta kashe mijinta ta gudu zuwa gidan wani mai suna Yaya Bala da wasu suka ce Kawaunta ne, amma wakilinmu ya gano cewa ba kawaunta ba ne yana auren kanwarta ce mai suna Hadiza Yaya Bala da suke zaune a Unguwar Dutsen Tanshi da ke garin Bauchi, kuma lokacin da wakilinmu ya je gidan wani mazaunin gidan da ya bayyana sunasa da Umar, ya ce tuni ’yan sanda suka kama Yaya Bala, yayin da kanwarta Hadiza matar Yaya Balan ta gudu daga gidan.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin matan da suke zaune gida daya da A’isha game da wannan batu, amma sun ce babu abin da za su sake fada wa manema labarai, domin a cewarsu, Sani Muhammad Ladan ne kawai aka ba shi damar ya yi magana da manema labarai game da wannan batu.
Da Wakilinmu ya tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Bauchi (DSP) Haruna Muhammad domin jin ta bakinsa game da wannan batu ya ce labarin bai isa ofishinsa ba, amma da zarar ya samu labarin zai yi cikakken bayani.
Wakilinmu ya gano cewa a halin yanzu A’isha tana ofishin ‘yan sanda da ke Unguwar Dutsen Tanshi ne a Bauchi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin