✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amaryar wata 4 ta sha guba a Legas

Al’ummar garin Idi Araba da ke Karamar Hukumar Mushin a Jihar Legas, sun wayi gari da abin alhini inda aka ce wata matar aure mai…

Al’ummar garin Idi Araba da ke Karamar Hukumar Mushin a Jihar Legas, sun wayi gari da abin alhini inda aka ce wata matar aure mai suna Maryam Rabi’u ta sha gubar sinifa lamarin da ya yi sanadiyar rasuwarta a ranar Juma’ar makon jiya.

Bayanai sun ce, Maryam wacce aka yi wa aure wata hudu da suka gabata ta kasance cikin damuwa lamarin da ya sanya ta komawa gida wajen mahaifiyarta wacce ta lallabe ta ta mayar da ita dakin mijinta inda daga nan ta sha gubar da ta yi sanadiyyar rasuwarta.

Duk da cewa, ana tunanin tsananin damuwa ce ta kai Maryam ga shan gubar da ta yi ajalinta, amma duk binciken da Aminiya ta gudanar domin jin damuwar da ta sanya marigayiyar daukar wannan mataki ya ci tura. Wadansu daga cikin makusantanta da wakilin Aminiya ya zanta da su sun bayyana ta da mutuniyar kirki mai girmama na gaba, kuma mai yawan karanta Alkur’ani Mai girma.

An yi jana’izar Maryam Rabi’u a ranar Asabar din makon jiya kamar yadda Musulunci ya tanada.