✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta ba da kayan agaji ga al’ummar Ngalda

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta ba da agajin kayayyakin abinci da sauran kayan tallafi ga jama’ar da ambaliyar ruwa ta lalata…

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) ta ba da agajin kayayyakin abinci da sauran kayan tallafi ga jama’ar da ambaliyar ruwa ta lalata wa gidaje a garin Ngalda da ke Karamar Hukumar Fika a Jihar Yobe.

Kimanin kwana daya bayan aukuwar lamarin ne Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Idi Barde Gubana ya kai ziyarar jajanta wa mutanen, sannan ya bai wa Hukumar SEMA umarnin ta kai kayayyakin tallafin ga wadanda ambaliyar ta shafa.

Hukumar SEMA ta kai agajin ne bisa jagorancin Babban Sakataren Hukumar Dokta Mohammad Goje.

Da yake karbar kayayyakin, Shugaban Karamar Hukumar Fika, Alhaji Baba Abare ya gode wa gwamnatin jihar bisa wannan tallafi, sai ya hori wadanda bala’in ya shafa su dauki kaddara cewa Allah ne Ya aiko musu su kuma yi addu’ar Allah Ya kare sake aukuwar haka nan gaba.

A nasa tsokaci, Dagacin Ngalda, ya bayyana jin dadinsa da godiya ga Gwamnatin Jihar Yobe kan daukar matakin gaggawa da nuna damuwa kan lamarin mutanen Ngalda.

Da yake jawabi, Babban Sakataren Hukumar Dokta Muhammad Goje, ya hori wadanda suka samu tallafin su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata.

Ya jinjina wa kokarin karamar hukumar kan yadda cikin gaggawa ta kwashe mutanen da ambaliyar ta shafa bayan sanar da su halin da ake ciki lokacin da ambaliyar ta auku don kai su wasu yankunan don tseratar da su.

Kayayyakin da aka raba sun hada buhunan shinkafa 141 da jarkunan man girki 30 da katifu 141 da kayayyakin sawa na yara da zannuwa 141.

Sauran sun hada da bargunan rufa da gidajen sauro 141 da dila 5 na kayan sawa da bokitan roba da takalma da sauran abubuwan aikin gida.