✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya ta hallaka mutum 200 a Indiya

A dadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar Indiya ya haura mutum 200, yayin da ake ci gaba zabga ruwan sama kamar da bakin…

A dadin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a kasar Indiya ya haura mutum 200, yayin da ake ci gaba zabga ruwan sama kamar da bakin kwarya a Yammaci da Kudancin kasar.

Jami’an agaji sun kwashe sama da mutum miliyan daya da dubu 200 zuwa wasu sansanoni domin sama musu mafaka.

Daga cikin yankunan da ambaliyar ta fi kamari, har da garin Kerala mai cike da wuraren yawon bude-ido, yayin da a  bara, garin ya gamu da mummunar ambaliyar da bai taba fuskanta ba, a kusan shekara 100, inda mutum 450 suka mutu a lokacin.

A makwabciyarta Jihar Karnataka kuwa, mutane akalla 48 ne suka mutu, inda wani jami’i ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa (AFP) cewa, mutum 16 sun bace, kuma har yanzu ana nemansu.

An aike da masu aikin ceto da suka hada da sojojin kasa da na ruwa da na sama don gudanar da aikin ceto da samar wa wadanda lamarin ya rutsa da su sauki.