✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta lalata gonakin shinkafa a Taraba

Ambaliyar ruwa tayi sanadiyyar lalacewar shinkafar da aka noma a gonakin gefen kogin Taraba da Benuwe, a karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba. Majiyarmu ta…

Ambaliyar ruwa tayi sanadiyyar lalacewar shinkafar da aka noma a gonakin gefen kogin Taraba da Benuwe, a karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba.

Majiyarmu ta gano cewa ambaliyar ta faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da ake yi, inda mafi yawan shinkafar da ruwa ya cinye ta gama nuna yayin da kadan ya rage a girbeta.

Wani manomi da abin ya rutsa da shi, Alhaji Nuhu Muhammed, ya ce a shekarar data gabata ya girbe shinkafa buhu 500, amma a yanzu ambaliyar ruwan ya shafe gonar ta yadda ba zai samu komai ba.

Sarkin yankin na Gossol, Alhaji Idi Ciroma, ya bayyanawa AMINIYA cewar ambaliyar ta shafe daruruwan gonakin shinkafa, wanda hakan ya haifar da asara ga dubban manoman yankin.