✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfani da lemun tsami wajen gyaran fata

Ko kun kasance daga cikin wadanda kuraje ke bata musu fuska? Shin kun kasance cikin wadanda wajen shafe-shafen nau’o’in man kara hasken fata kuraje masu…

Ko kun kasance daga cikin wadanda kuraje ke bata musu fuska? Shin kun kasance cikin wadanda wajen shafe-shafen nau’o’in man kara hasken fata kuraje masu yawa ke feso mawa tare da barin tabbai bakake? Ko kun san me zai warkar da wadannan tabbai da kurajen bugu da kari har da sanya fata haske? Lallai ba wani abu ba ne illa amfani da lemun tsami na tsawon wata uku ko fiye. Lemun tsami na dauke da sinadaran da ke magance kowace irin cutar fata idan aka yi hakuri. Ganin yadda wadannan hade-haden lemon tsami ke taka rawar gani a wajen yaki da cututtukan fata ya sanya a yau na kawo muku yadda ake amfani da su a fata domin samun saukin wadannan cututtuka.

• Haskaka gwiwa da gwiwar hannu da kuma yatsar da ta yi baki sakamakon man kara haske: Idan gwiwa da yatsun kafa da hannu suka yi baki sosai sakamakon yawan shafa man haske, sai a samu lemun tsami daya a yanka shi gida biyu sannan a rika shafawa a inda ya yi baki a jiki na tsawon minti ashirin safe da yamma kullum, za a sha mamaki.

• Kurajen fata: A samu lemun tsami a yanka shi gida biyu sannan a rika matse ruwansa ana goga shi a kan kuraje ko tabon fata. Sannu a hankali tabon zai fara haske har ya bace. Amma sai an yi hakuri. Idan aka fara amfani da wannan hadin kada a matse kurajen da suka feso.

• Farin hakori: A samu ‘baking soda’ sannan a kwaba da ruwan lemun tsami. A dauko magogin goge hakora  a rika lakuta ana gogawa a hakora. Yin hakan na sanya hasken hakora sosai musamman ga masu hakoran da suka riga suka dafe suka canja launi.

• Hasken fata: Lemun tsami na dauke da sinadarin bitamin C don haka yawan amfani da shi a fata na dada hasken fata. Amma ana son amfani da man SPF idan ana yawan amfani da lemun tsami a jiki ko fuska. Yawan amfani da shi na sanya rana ta rika dakar fuska amma idan an samu man SPF ana shafawa kafin a fita, hakan na hana rana yi wa fatar illa.

• Amfani da shi a matsayin man shafawa: A samu  man kwakwa sai a zuba shi a cikin murta sai a samu lemun tsami guda daya ko biyu sannan a matse ruwan a cikin wannan man sai a kwaba su a rika shafawa a jiki a matsayin man shafawa. Yin wannan hadin na kare  fatar jiki da ga haifar da cututtuka da dama.

• Domin cire kwalliyar fuska: Idan ba a manta ba, a baya na taba fada muku cewa rashin goge kwalliya a fuska kafin a kwanta barci na haifar da fesowar kuraje, don haka, a samu lemun tsami sai a hada da man dogon yaro a samu auduga ana goge fuskar da shi har sai kwalliyar ta fita tsaf kafin a kwanta barci.