✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfani da sinadarin Bitamin E, wajen gyaran jiki

Sinadarin Bitamin E yana nan kamar magani. Kuma za a iya samunsa a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya ko na koli. Sinadarin na…

Sinadarin Bitamin E yana nan kamar magani. Kuma za a iya samunsa a shagunan da ake sayar da kayan kwalliya ko na koli. Sinadarin na gyara jiki sosai. Da yawa mata za su ga wannan sinadarin a shago amma ba su san amfaninsa ga jiki ba. A yau na kawo muku yadda za a yi amfani da wannan sinadari wajen gyara jiki. Wannan sinadari na nan iri daban-daban amma zan lissafo muku yadda za a yi amfani da su. Kada a yi amfani da na sha wajen gyara fuska. A tabbatar da cewa, wanda za ku yi amfani da shi na magani ne kuma za a iya tantance su idan an tambaya a wajen masu sayar da magunguna.

 

  • Bitamin E na ruwa:

A matso sinadarin a hannaye, sannan sai a shafa a fuska da daddare kafin a kwanta. Kada a sanya da yawa a fuska don kada maikon ya yi yawa a fuska. Wannan sinadari na gyara fuska da kuma rage kurajen fuska.

 

  • Ruwan Bitamin E na gashi:

A bude sinadarin Bitamin E 2 ko 3 daidai tsayin gashinki. Sai a shafa man a gashi da kuma fatar kai. Sai a wanke gashin bayan minti 30 ko sa’a 1.

 

  • Kwayar Bitamin E:

Wannan sinadarin ya fi amfani a jiki. A hadiye kwaya daya kullum na tsawon kwana 15. Yana taimakawa wajen sanya fata sheki da laushi, kuma yana sanya tsirar gashi da wuri.

 

  • Man Bitamin E:

A matse ruwan man a cikin man shafawa, sannan sai a kwaba su. Man na gyara fatar jiki.

  • Za a iya hada wannan sinadarin da man baki don samun lebe mai laushi.