✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin azumi ga lafiya

Azumi na wajaba ne a kan mutum mai hankali da lafiyar jiki, ba mai rauni ko maras hankali ba. Wannan shi ya sa a addinance…

Azumi na wajaba ne a kan mutum mai hankali da lafiyar jiki, ba mai rauni ko maras hankali ba. Wannan shi ya sa a addinance da kuma a likitance ba kowa ne aka yarda ya yi azumi ba. Duk da haka kuma akwai marasa lafiyar da azumi kan yi wa amfani sosai wadanda su ma za a yi dan bayanin amfanin azumi a gare su.
Da farko dai azumi na daya daga cikin hanyoyin gyara lafiyar jiki da ta tunani ga mai lafiya, domin a wasu lokuta ciki kan bukaci hutu daga kowane irin abinci na wani dan lokaci. Hakan kan sa kitsen jiki ya narke, domin akan fara amfani da shi a matsayin abinci wanda kan sa mutum ya dan rage teba. A yayin da mutum ke azumi kuma, hanta kan fito da abincin da ta tara (sinadarin glycogen wanda yake ba da kuzari na dan wani lokaci) don amfani da shi, domin ita hantar ta fara shirin ajiye sabo. Wannan ma kadai kan kara lafiyar hanta. Bayan hanta shi ma hanji yakan samu ya dan huta na wani lokaci, ya daina kumburi ko cushewa da yake yawan yi a wasu mutanen.
Masu yin azumi suna cike da tunani na annashuwa da na zumudin lada na aikin ibada, wanda wannan annashuwa kadai wani karin lafiya ne ga aikin kwakwalwa.
Ga marasa lafiya kuma, akwai cututtukan da azumi kan sa a samu sauki sosai. Na farko shi ne hawan jini. Hawan jini kan kara sassaita a wasu mutanen yayin azumi kamar yadda binciken masana da dama yakan nuna. Misali, wani likita dan kasar Amurka mai suna Dr. Goldhamer da ya kware a bincike kan azumi, ya yi nazarin amfanin azumi ga masu hawan jini. A cikin mutane masu hawan jini da ya gwada yayin da suke yin azumi, kashi 98 cikin 100 ba su bukaci magungunansu ba yayin azumin, wato azumi kawai ya sassaita hawan jinin nasu.
Sai kuma masu ciwon suga, su ma azumi kan sassaita yawan sugar jikinsu, sai dai akan shawarce su da su rika yin amfani da na’urar auna suga a kullum saboda sugan zai iya yin kasa sosai, su galabaita.
Ga masu shan miyagun kwayoyi (musamman a wannan zamani da ake shan kwayoyi iri-iri da ake ganin kamar magunguna ne, wato irinsu tramal da maganin tari), azumi na daya daga cikin hanyar horar da kwakwalwa barin sabo da miyagun kwayoyi. Ga mai so ya daina wannan mummunar dabi’a, azumi zai iya taimakonsa kwarai da gaske.
Amma kuma akwai wadansu larurori wadanda a addinance ba a dora wa masu su azumi ba, a likitance ma haka. Wadannan sun hada da masu tabin hankali da marasa lafiyar da sai an kwantar an tayar da masu tarin fuka ko ciwon sida ko wata larura wadda take bukatar magani (domin magungunan wadansu cututtukan kan bukaci abinci kodayaushe) masu gyambon ciki da dai sauransu. Wadansu masu juna biyun ko masu shayarwa su ma sukan galabaita, abin da suke dauke da shi idan suka yi azumi. Duk dai masu irin wadannan larurori ban da ’yar fatawar likita suna bukatar fatawa ta malamai don a tabbatar za su iya azumi ko a’a. Wanda ciwonsa ba mai warkewa ba ne sai dai ciyarwa da mai azumi ke nan a kansu.
Me ya kamata mai azumi ya bude baki da shi?
A yanayi na zafi, wanda kan sa ruwan jikin mutum kan saurin karewa ta hanyar zufa, dole wanda ya kai azumi ya fara kokarin mai da ruwan jikinsa tukun bayan an tauna dabino. Wannan abin sha zai fi kyau ya zama mai dan dumi, domin hanji su ware, kafin daga bisani a sha na sanyi. Mutane da dama za su lura cewa idan abin da suka sha ba mai zafi ba ne yana saurin cika musu ciki. Wannan abin sha zai iya zama kunu ko koko ko shayi da dai sauransu. Idan aka dan sha kadan, hanji ya ware, sai a kara da duk abin da ya samu. Ba dai a so a cika cikin tashi guda. Ba kuma a so a ci abinci dab da lokacin kwanciya.
Yana da kyau a kara yawan cin abinci mai gina jiki, irinsu naman kifi ko na kaza ko na dabbar da aka samu da kwai da madara da awara da kosai da ire-irensu a kan sauran masu kara kuzari irinsu shinkafa da tuwo da burabusko.
Amsoshin tambayoyi:
Gwajin sukarina maki shida (6.0) ne. Likita ya ce ya yi sama sosai, ina mafita?
Daga Maryam Legas
Amsa: A’a, kafin a ce makin suga na cikin jini ya yi sama sosai sai ya haura maki bakwai (7.8) idan ba a ci abinci ba a lokacin da aka dau jinin. Idan kuma an ci abinci, kada ya haura maki sha daya (11.1). Haka kuma sai alamun ciwon suga irinsu yawan fitsari, sun fito fili. Don haka kada ki ta da hankalinki.
Ni dai ina da kiba kuma ina son na dinga motsa jikina. Ina yin gudu amma duk jikina sai ya rika ciwo har cikin namana da tafin kafata kamar ba zan iya tafiya ba.
Daga Maikudi Sardauna, Kawo
Amsa: To ai dama haka ake so. Idan ka yi kwana biyu zuwa biyar ka ci gaba a haka za ka nemi ciwon ka rasa. Sai dai kawai ka nemi dan parasitamol ka sha idan ka fara jin ciwon. Sa’annan kuma idan har ila yau ka ga ciwon jiki ya ki karewa sai ka tsagaita, ka dawo sassarfa maimakon gudun.
Ga kuma azumi na gabatowa don haka duk abin da ka rasa na kiba a wannan wata kada ka ce sai ka mayar da shi bayan an gama azumin.
Wai idan jinin mutum ya nuna maki 150/100 to yana da hawan jini ke nan? Kuma mece ce shawara?
Daga Usman Mu’azu, Funtua
Amsa: kwarai kuwa, wannan maki na nufin bugun jini ya hau. Shwararwarin su ne: 1-Rage cin gishiri da maggi ko ko kanwa ko mangul (wato sa wa daidai gwargwado a miya) yakan saukar da hawan jini. 2-Yawan motsa jiki kamar tafiyar kasa ta minti 30 zuwa 45 a kullum kan saukar da hawan jini. 3-Idan kana aiki ba hutawa kuma, kamar Asabar da Lahadi) kan sa hawan jini ya sauko. 4-Barin shan taba sigari da barasa yana sa hawan jini ya sauko daidai gwargwado. 5-Zullumi da rashin kwantar da hankali kan jawo hauhawan ciwon saboda haka idan aka kwantar da hankali, za a samu sauki sosai. 6-Shan maganin hawan jini a kan ka’ida ga mai wannan ciwo kamar yadda likitansa ya zayyana, yana hana kamuwa da cututtukan da hawan jini kan kawo kuma mutum ya yi rayuwarsa kamar kowa. Amma da zarar an bar shan magani, to komai na iya faruwa. Su wadannan magunguna sai an daure, domin haka nan za a yi ta shan su ba fashi har tsawon rayuwa ko kuma idan an ga hawan jini ya sauka da kyau a dan dakatar.

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin tambayoyi

Shin kwayoyin hutun haihuwa din nan da ake kira ‘microgynon’ suna da wata illa ne? Wanne ya fi dacewa na yi tsakanin kwayoyi da allura da kuma sauran hanyoyin samun hutun?
Daga Uwargida H. Umar, Gombe
Amsa: Ana tsara iyali ne don lafiyar uwa da ta jariri ta bunkasa kafin a samu wani juna biyun. Mutum zai ga amfanin haka idan ya lura da yadda mace mai ciki da goyo take karewa, ita ba ta huta ba, na goye bai huta ba, balle abin da ke ciki. Akwai hanyoyin ba da tazarar iyali kala-kala. Duk kusan sun fi shafarki a matsayinki na mace fiye da maigida.
Hanya ta farko ta kin daukar ciki da ta shafi mace ita ce ta shayarwa. Mafi yawan mata (ba duka ba) ba sa al’ada tsawon shayarwa – ko da kuwa tsawon shekara biyu suka shayar. To a irin wannan yanayi ba su ba daukar ciki sai sun yaye. Wannan dabara ba ta da wata matsala, domin haka Ubangiji ya tsara mata da yawa, don a samu tazara tsakanin jarirai.
Ma’aurata kuma za su iya yin kirgen wata wanda ya fi shafar mai gidan. A kirgen wata, mai gida zai kauce wa ranakun daukar ciki. Wadannan ranaku su ne kwanakin tsakiyar watan matar – wato watanta na al’ada.  Wannan kirge yana da dan rikitarwa domin sai mace ta tabbatar cewa watanta ba ya rikici, sa’annan kuma gami da cewa yawancin magidanta ma ba su san mene ne kwanakin al’ada ba. A irin wannan yanayi dole maigida ya tambayi matarsa ta fahimtar da shi.
Ga dan misalin kirgen wata; a mace mai kwanan wata 28, daga rana ta 9 zuwa goma sha 19 su ne ranakun tsakiyar wata, wato ranakun da za a iya daukar ciki. A mai kwana 32, ranakun 11 zuwa 21 su ne ranakun daukar ciki. Shi ma dai wannan bayani maigida da uwargida su je su ga likitansu domin karin haske.
Sauran hanyoyin dabaru da suka shafi uwar gida yawanci na asibiti ne kamar allurai da kwayoyi (irin wanda kike tambaya a kai) da saka sinadarai daban-daban a mahaifa. Kuma dukkansu suna da ’yan matsaloli wadanda suka hada da rikicewar al’ada ko ciwon mara ko sa kiba ko hana samun juna biyu na tsawon watanni bayan an daina amfani da su, da dai sauransu. Wadannan ’yan matsaloli sun bambanta daga wata mace zuwa wata, wato wata ciwon mara kawai za ta yi, wata kuma kiba kawai za ta yi. Abin da kawai akan ba mata shawara shi ne sai sun gwada kusan kowane kafin su san wanda ya fi karbarsu. Akan samu mata da dama su gwada dabara daya, walau allura ko kwayoyi a kuma dace a karon farko, a mafi yawan lokuta kuma, sai an jarraba kusan kowane.