Search
Subscribe
Amfanin koren ganyen shayi

Amfanin koren ganyen shayi

Koren ganyen shayi na da amfani a jikinmu domin shansa na kara lafiya da kuma kara kyan fata. Za a iya shafa ganyen shayin a fuska. Koren ganyen shayi na kare fata daga saurin tsufa. Bayan haka, yana kare jikinmu daga cututtuka da dama. Yawan shan koren ganyen shayi na sanya a ga mutum kamar saurayi koda ya hada shekaru. Hanyoyin da za a iya amfani da koren ganyen shayi.

• Za a iya amfani da koren ganyen shayi a fuska;

A kan sanya wannan ganyen a cikin man shafawa da dama. Domin ganyen na kunshe da sinadarin bitamin C da A da kuma E. Amfani da ganyen na rage maikon fuska kuma fuskar ta yi santsi yadda ko alamar kuraje ba za a gani ba. Za a samo mayonnaise sai a dibi cokali uku daga ciki. Sannan dakakken ganyen shayi. Za a rika shafawa a fuska ban da gefen idanu. Sai a bar shi na tsawon minti 20 sai a wanke da ruwan dumi.

• Amfani da koren ganyen shayi na rage warin numfashi.

A tafasa ganyen shayi. Bayan haka, sai a jira na tsawon minti 30. Sai a rika amfani da shi wajen wanke baki. Yin hakan na hana datti zama a kan hakora. Kuma zai kare bakin daga wari.

Shan shayin na rage kiba; ana iya shan shayi safe da yamma domin rage maikon jiki.

• Koren shayi na rage tumbi ga macen da ta taba haihuwa da wadda ba ta taba haihuwa ba.

Shan ganyen shayi marar sukari akalla sau biyar a rana na matukar rage tumbi ga mata musamman matar da ta taba haihuwa. Gara a gyara tunda ba a kwalliya da tumbi. Yana da kyau a jure na tsawon wata biyar za a yi matukar mamakin yadda tumbi zai shanye.

• Ganyen shayi na magance ciwon ido.

A sanya ganyen shayi a gidan sanyi na tsawon minti biyar sannan a rika dorawa a kan idon har sai ya narke. Yana rage ciwon ido mai zafi.

• Yana gyara fuska.

A samu koren ganyen shayi sannan a zuba burbudin a cikin zuma sai a rika shafawa a fuska na tsawon minti ashirin akalla sau biyu a rana; safe da yamma. Yin haka na magance fesowar kurajen fuska.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin