✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin man lemun tsami a jiki da fata

Man lemun tsami na da muhimmanci sosai musamman ma a fata. Domin yana dauke da sinadarin bitamin C. wannan sinadarin kuma na kara lafiya ne…

Man lemun tsami na da muhimmanci sosai musamman ma a fata. Domin yana dauke da sinadarin bitamin C. wannan sinadarin kuma na kara lafiya ne a jiki da fata. Man na warkar da kurajen fuska da kwarkwata. Yana taimakawa wajen kara wa fatar fuska haske ba tare da yin bilicin ba. Uwa uba kuma yana taimakawa wajen magance mura. Ana amfani da man ‘sunscreen’ idan za a shiga rana. Kada a shiga rana da man lemun tsami a fuska domin zai iya illatar da fata. Don haka an fi son shafa shi da safe ko yamma domin samun sakamako mafi inganci.

Yadda za a hada man lemun tsami

A samu lemun tsami sai a bare bawon kada a yi amfani da ruwan lemun tsami wajen hada man lemun tsamin. Sannan sai a samu man kwakwa (idan ba a manta ba na rubuto muku yadda ake hada man kwakwa kwanakin baya).

Bayan an bare bawon, sai a shanya su a karkashin fanka kamar na tsawon awa daya. Bayan sun dan bushe, sai a saka a gora sannan a zuba man kwakwa a gauraya bawon da man a gorar sannan a rufe.

Sai a samu wurin da ba rana ko daki ko kicin na tsawon mako biyu. Amma a kullum ana zuwa ana girgizawa. Shi ke nan! Man lemun tsami ya yi.

Za a iya amfani da man zaitun ma idan ba a da man kwakwa.

Idan ba za a iya bin wannan hanyar ba akwai wata hanya da za a bi don hada man lemun tsamin.

A sa bawon a tukunya sannan sai a zuba man kwakwa a dora a wuta amma kada wuta ta yi yawa. Ana gaurayawa na tsawon mintuna biyar. Bayan haka, sai a sauke ya huce sannan sai a zuba a kwalba.