Categories: Kwalliya

Amfanin ruwan lalle a fata

Barkanmu da sake saduwa da ku a wannan filin namu na kwalliya. Jama’a da dama sun san cewa lalle abin ado ne ga mace. Bayan haka ruwan lallen ma na da matukar amfani ga fata. Ana shuka lalle ne a wuraren da ke  da zafi. Yanayin zafin wuri ke nuna kyan launin lalle. Don haka a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da lalle a fata.

  • Domin samun sulbin fuska, a jika lalle na tsawon awa biyu sannan a kwaba shi da ruwansa sai a diga man zaitun da kwanduwar kwai sannan a shafa a fuska na tsawon minti talatin sannan a wanke da ruwa. Ana son shafa irin wannan hadi kamar sau daya a mako.
  • A jika lalle da ruwa sannan a zuba man zaitun da man kwakwa a rika wanke gashin kai da shi domin hana gashi tsinkewa da kuma sanya gashi laushi,
  • Domin magance amosanin kai; a kwaba lalle da ruwan lemun tsami kadan sannan a shafa a fatar kai a bar shi na tsawon minti goma zuwa sha biyar kafin a wanke da sabulun wanke gashi.
  • Ruwan lalle shi ne babban abin da ke taya lalle kamawa a fatar hannu. Ana gane lalle mai kyau ne ta ganin irin launin ruwan da ke jikin lalle.
  • Shi kansa lalle abin ado ne ga mata idan aka sanya shi a tafin kafa ko a hannu.
  • Ana wanka da ruwan lalle bayan ya tsumu domin kara launi ga amaryar gobe. Za a iya jika ruwan da lalle mai dan dama ya tsumu bayan amaryar gobe ta gama wanka za ta iya watsa wannan ruwan a wankan karshe domin sanya fata laushi da launi mai kyau.

ADVERTISEMENT
. .

Recent Posts

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

6 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

6 hours ago

Matashin da ke sace kudin coci ya shiga hannu

Wani matashi da ake zargi da sace kudin da ake tarawa na sadaka a cocin "Divine church of God" a…

7 hours ago

‘Yan Sanda sun bada belin Malam Niga a Kaduna

Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kaduna ta bayar da belin Malam Lawal Yusuf Muduru da aka fisani da Malam Niga wanda…

19 hours ago

An yi garkuwa da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da yin garkuwa Kwamandan shiyyar Karamar Hukumar Suleja kuma Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda ACP Musa…

1 day ago

An gano zakin da ya tsere daga gidan zoo na Kano

Bayan shafe daren jiya ana neman wani rikakken zaki da ya kufce daga gidansa a gidan namun daji na Kano,…

1 day ago