✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amfanin tafarnuwa ga lafiyar dan Adam

Tafarnuwa na da amfani masu yawa wajen kare lafiya da kuma maganin wasu matsaloli

Tafarnuwa na cikin kayan yaji da jama’a da dama ke sha’awar amfani da ita ta hanyoyi daban-daban, ko da yake wasu na gudun warinta.

Aminiya ta zanta da wani likita, Dakta Abdullahi Ridwan wanda ya tabbatar da amfaninta ga dan Adam.

Ya ce tafarnuwa na da tasiri wajen rigakafin cutar asma inda ake bukatar mai cutar a duk dare kafin ya kwanta barci, ya dafa ta ya sha da madara.

Ana kuma amfani da ita wajen rigakafin sanyi da tari ta hanyar cin ta ita kadai ko hadawa da citta a sha idan ana bukata.

Bincike ya tabbatar da cewa cin tafarnuwa na kashe kwayoyin cuta masu sa dan Adam atini ko gudawa.

Tana kuma da tasiri wajen bayar da kariya daga cutar hawan jini, shi ya sa ake bukatar a rika amfani da ita akai-akai.

Yawan cin tafarnuwa da abinci yana taimakawa wajen saurin narkar da abincin da aka ciki ta yadda sinadaran gina jiki za su shiga cikin jini a kan lokaci.

A gargajiyance kuma akan yi amfani da tafarnuwa wajen maganin cin ruwa.

A same ta a goge ta a zuba a cikin ruwan dumi saanna a sa kafa cikin ruwan na kamar minti talatin.

Kadan ke nan daga cikin amfanin tafarnuwa.