✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amitabh Bachchan ya zama sarkin ’yan fim na Indiya

Shahararren dan fim din nan na Indiya, Amitabh Bachchan, ya zama Sarkin ’yan fim na Indiya, a sakamakon tuntubar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar…

Sarkin Fim na Indiya, Amitabh BachchanShahararren dan fim din nan na Indiya, Amitabh Bachchan, ya zama Sarkin ’yan fim na Indiya, a sakamakon tuntubar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a Turai, domin gano dan wasan da ya fi kowa shahara a duniyar fina-finan Indiya.
An gudanar da wannan zabe ne, a daya daga cikin bukukuwan murnar cika shekara 100 da fara shirya fina-finan Indiya.
dan wasan, wanda ya yi fice wajen fitowa a manyan fina-finai, ya samu magoya baya da yawa daga cikin ’yan kallo da masu sharhi kan fina-finai, inda ya zama ya doke kowane dan wasa samun kuri’u masu yawa, wanda dalili ke nan aka nada shi wannan sarauta.
Amitabh ya kwashe shekaru sama da 40 yana fitowa a fina-finai, kamar “Sholay” da “Deewar.” Ya yi fice wajen hada kan masu fim da masu wasan talabijin, inda ya rika shirya wasannin talabijin na ‘Kaun Banega Crorepati’ da sauransu.
Kamar yadda ake masa lakani da ‘Big B,’ Bachchan kuma ya kasance dan fim na Indiya na farko da aka karrama a bikin zayyana na ‘Madame Tussaud’ kamar kuma yadda a baya-bayan nan ya zama jakada daga Indiya, wajen kunna fitilar gasar Olympic da aka gudanar a Landan, a 2012.
A zaben na jin ra’ayi da aka gudanar, an yi amfani ne da dandalin intanet da fagagen masu sharhi kan fina-finai da sauransu, inda aka zabi Amitabh a matsayin na daya, shi kuwa Dilip Kumar ya zo na biyu. Mai biye masu a baya, shi ne Shah Rukh Khan, wanda ya zo a matsayi na uku. Inda ita kuma Madhuri Didit ta yi fice a cikin mata, ta zo a matsayi na hudu.
“Ina alfahari da wannan sana’a tamu, musamman ma yanzu da take kara bunkasa. Muna ta yin kokarin ganin cewa mun yi wani abu sabo kuma na daban.” Inji Madhuri.
“Akwai kayatarwa ga al’amarin a ce an daukaka ni haka, sai dai kuma an dora mani babban nauyi, wanda ya sa dole in kara azama ga ayyukana. Ina kaunar haka, ina kaunar aikin da nake yi.” Inji ta.
Sauran ’yan was an da aka zaba a matsayi daban-daban sun hada da na 5 Raj Kapoor, na 6 Nargis, na 7 Deb Anand, na 8 Waheeda Rehman, na 9 Rajesh Khanna da kuma ta 10 Sridebi.
Wasu kuma da suka tabuka abin kirki, sun hada da Salman Khan na 11, Aamir Khan na 14, Dharmendra na 15, Hema Malini  ta 18, Madhubala 24, Kajol 30, Hrithik Roshan 32, Rani Mukerji 38, Kareena Kapoor 43, Mumtaz 50, Saif Ali Khan 59, Priyanka Chopra 86 da kuma Katrina Kaif 93.