✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amotekun ba za ta raba kan  kasa ba – Abiodun Fadeyi

A tattaunawa da Aminiya Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo Mohammed Abiodun Fadeyi a ofishinsa  a Ibadan ya ce an kafa Rundunar Amotekun ne domin…

A tattaunawa da Aminiya Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Oyo Mohammed Abiodun Fadeyi a ofishinsa  a Ibadan ya ce an kafa Rundunar Amotekun ne domin tsaro, ba domin raba kasa ba. Kuma ya yi bayani kan abin da ya hana sanya Fulani a cikin Amotekun da yadda za a gyara lamarin:

Me za ka ce a kan hangen da wadansu ke yi cewa an kafa Rundunar Amotekun ce domin raba Najeriya da kafa kasar Oduduwa?

Babu gaskiya kan wannan zargi domin dukkanmu muna sane da tabarbarewar tsaro a ko’ina a Najeriya inda wadansu suke kashe mutane a kullum da garkuwa da mutane da satar shanu da  fashi da makami. ’Yan sanda da sojoji suna kokari sosai amma akwai alamar aikin ya fi karfinsu.  Shi ne ya sa gwamnonin jihohi 6 na wannan sashi suka yanke shawarar kafa Rundunar Amotekun don su taimaka wajen sintiri a dazukan da wadannan miyagu suke boyewa yta adda za a iya kama su a mika su ga jami’an tsaro domin hukunta su.  Gwamnonin sun mika bukatu da shawarwari ga majalisun dokokin jihohinsu domin kafa dokar da za ta karfafa  wa dakarun Amotekun gwiwa wajen gudanar da ayyukansu. Kafin mu sanya hannu a kan dokar a nan Jihar Oyo sai da muka kira taron masu ruwa-da-tsaki daga ko’ina kuma suka amince da samar da dokar. Don haka ba a kafa wannan doka domin raba Najeriya da kafa sabuwar kasar Yarbawa kamar yadda wadansu ke hange ba.

Kungiyar Miyetti Allah ta zargi majalisarku cewa ta ki amincewa da sanya samarin Fulani cikin Amotekun ne don ana so a kore su dagaJihar Oyo. Ko kana sane da wannan zargi?

Na ji irin wannan surutu marar kan gado amma kamar yadda na gaya maka tun farko, Allah ne Ya samar da Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa kuma babu abin da zai raba ta. Misali akwai Fulani masu yawa da suka shafe shekara fiye da 100 suna zaune a sashen Oke-Ogun na Jihar Oyo, mafi yawansu ba su san garuruwansu na asali a Arewa ba kuma sun yi auratayya da Yarbawa a wannan sashe. To yaya za a ce an kori wadannan mutane daga wannan sashi a dalilin kafa Amotekun?

Ai su ma ’yan Najeriya ne da suke da ’yanci zama a ko’ina kuma mun riga mun zama daya. Saboda haka babu gaskiya a cikin zargin da ake yi. Su ma Fulanin sun amince da samar da Amotekun ne domin ba sa jin dadin barnar da ake yi ta kisan jama’a, shi ya sa suke so a sanya su cikin Amotekun domin su yi aiki tare.

Abin da ke faruwa shi ne akwai wadansu miyagun Fulani da suka haifar da wannan matsala wajen shiga tsakaninsu da kulla munafuncin raba kawunansu. Amma majalisa ta riga ta amince da daukar samarin Fulani cikin Amotekun kuma idan Allah Ya yarda za a sanya su cikin dakarun da za a horar nan gaba kadan. Muna so Najeriya ta koyi da  Amurka ne ta fannin samar da kabilu daban-daban da suka hadu suka samar da dunkulalliyar kasa ba tare da bambancin addini ko kabila ba. Irin hake muke fatar samu a Najeriya wata rana mu ji an ce gwamnatocin Arewa sun nada Yarbawa a kan mukaman kwamishinoni saboda dadewarsu da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban al’umma. Su kuma gwamnatocin Yamma su nada Hausawa da sauran kabilun Arewa da ke zaune a jihohinsu bisa irin wadannan mukamai. Yin haka ne zai kawo hadin kan kasa da ci gaba tare da zaman lafiya a tsakanin jama’ar Najeriya.

Dokar kiwo da majalisarku ta kafa a baya Kungiyar Miyetti Allah ba ta ji dadin kafa ta ba domin akwai takurawa gare su. Me za ka ce kan haka?

Ai na gaya maka akwai wadansu daga cikinsu (Fulani) da suke kulla makirci a tsakaninsu. Mun samu labarin cewa wadannan Fulani ba ’yan Najeriya ba ne kuma tuntuni aka fara bincike. Amma kamar yadda Kungiyar Miyetti Allah ta bayar da shawara akwai bukatar sayen manyan filaye a cikin dazuka domin kiwon dabbobinsu majalisa tana nan tana duba yiwuwar amincewa. Sai dai muna duba yadda za a iya kebe musu filayen kiwo ta yadda ba zai shafi gonakin manoma ba domin guje wa aukuwar matsala a tsakaninsu. Shawarata gare su ita ce idan suka hango abin da ba su amince da shi ba, to su rubuto bukatunsu da murya daya su kawo mana domin hanzarta daukar mataki.

Yaya kake ganinn makomar Najeriya a nann gaba kan rayuwar miliyoyin jama’arta?

A gaskiya matsalar jama’ar Najeriya ta yi yawa domin tunda aka haifemu ba mu taba ganin irin barnar da wadansu kebabbun mutane suke yi wajen satar dukiyar talakawa ba, irin na kasar nan. Cin hanci da rashawa ya yi yawa domin miliyoyin Dalar Amurka da aka kebe domin yi wa jama’a ayyukan gina hanyoyi da asibitoci da makarantu da samar da ruwan sha ne wadansu mutane suke sacewa babu tausayi. Amma abun da nasani shi ne duk da irin wannan barna Najeriya ba za ta taba rabuwa kamar yadda wadansu ke hange ba. Kuma Allah zai yi mana jagoranci wajen gano hanyar gyara wannan matsala.