✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (2)

Assalamu alaikum Baban Sadik. Da fatan kana lafiya kai da iyalanka. Ni dalibi ne a fannin “Software Engineering,” ina son ka yi mini gamsasshen bayani…

Assalamu alaikum Baban Sadik. Da fatan kana lafiya kai da iyalanka. Ni dalibi ne a fannin “Software Engineering,” ina son ka yi mini gamsasshen bayani game da “Cloud Computing.”  Ka huta lafiya.

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Bayani kan tsarin “Cloud Computing,” in dai gamsasshe ne, yana bukatar bincike mai zurfi don samar da gamsarwa. Sai aka yi sa’a shi ne fannin da za mu kutsa da zarar mun gama amsa wadannan tambayoyi da a halin yanzu muke amsawa. Amma duk da haka, abin da kalmar “Cloud Computing” ke nufi a dunkule shi ne: “Tsarin sadarwa na tafi-da-gidanka.”  A warware kuma, “Cloud Computing” wani tsari ne da ke bai wa mutane damar mu’amala da bayanai ko manhajoji kai-tsaye, wadanda ke aijye a wasu kwamfutoci a wasu wurare daban, ta hanyar wayoyinsu na salula ko kwamfuta. Abin da ya fi shahara a zamanin baya shi ne ka saukar da manhaja sannan ka loda wa kwamfutarka ko wayar salula, don amfani da ita a duk sa’ar da ka samu dama. Ko ka saukar da wasu bayanai a kan wayarka ko kwamfutarka, don amfani da su a duk sa’ar da ka tashi bukata.  A tsarin “Cloud Computing,” ba haka lamarin yake ba.

Karkashin wannan tsari na “Tsarin sadarwar tafi-da-gidanka,” asalin bayanan ko manhajojin suna ajiye ne a wasu kwamfutoci ko ma’adanai na zamani, wadanda jama’a ke iya kaiwa gare su a duk sa’ar da suka tashi bukata.  Karkashin wannan tsari, ba ka bukatar saukar da manhaja a kan wayarka da dukan bayananta, ko saukar da wasu tarin bayanai ya zama suna dauke kan wayarka a koyaushe.  Sai dai ka shigar da bayananka kawai a asalin shafin da ke dauke da su, sai a isar da kai kai- tsaye, ta hanyar Intanet.

Kyakkyawan misali da zan ba ka shi ne na manhajar Gmail. Manhajar da ke kan wayarka ta Gmail ba ita ce ke dauke da sakonninka na Imel da ake aiko maka ko kake aika wa jama’a ba. Kawai kofar isa ga bayanan ne ke kan wayarka. Da zarar ka shigar da suna (username) da kalmar sirri (password) sai a riskar da kai asalin bayanan. Shi ya sa ma idan ka rasa wayarka, sanadiyyar sata ko lalacewa da zarar ka samu wata sabuwar wayar, kana saukar da manhajar Gmail a sabuwar wayar, za a loda maka sakonninka kai-tsaye. Ka ga da a ce a kan wayarka hakikanin bayanan suke, da ka rasa su ke nan daga wancan tsohuwar wayar da aka sace ko ta lalace.

Haka nan manhajar rubutu na Microsoft Office – irin su Word da Edcel, da Powerpoint.  A farkon lamari ana sayensu ne a dauke cikin faifan CD, ko ka je shafin Microsoft da ke Intanet ka saya, sai a saukar maka su kan kwamfuta ko wayarka. Amma a halin yanzu wasu lambobi kawai za ka saya masu suna: “License Code.”  Da zarar ka saya za a ba ka dama a shafin Microsoft da ke Intanet, ka samu isa zuwa ga manhajar ita kanta kai-tsaye. Haka ma Kamfanin Google suna da irin wadannan manhajoji, irin su: “Google Docs” da “Google Sheets” da kuma “Google Slides.”  Dukan wadannan ba ka bukatar saukar da su a kan kwamfutarka. Shafin google kawai za ka je a Intanet, ka budo su, ka rubuta abin da za ka rubuta, ka dabba’awa (printing), ko ka taskance su (sabing) a shafinka; duk sa’ar da ka tashi bukata sai dai ka shiga shafinka na Google da ke dauke da wannan manhaja, ka yi tu’ammali da su kai-tsaye.

Kafin in karkare. Tsarin “Cloud Computing” na dauke ne da rukunai guda uku. Na farko shi ne asalin muhallin da ke dauke da bayanai ko manhajar. Wannan shi ake kira “Cloud Storage System.”  Kwamfutoci ne da ke jone da dibga-dibgan ma’adanai na zamani masu mizani bila-adadin. Dukan manyan kamfanonin sadarwa na duniya suna da su a wasu wurare ko kasashe da suka tanada. Google na da irin wannan muhalli da ake kira: “Data Centers” a wurare sama da goma sha biyu a fadin kasar Amurka kadai.  Kamfanin Microsoft ma na da su.  Sannan cikin watan jiya (Janairu, 2019) ya bude wata sabuwar cibiyar adana bayanai a kasar Jamus da Suwizaland da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates).

Rukuni na biyu shi ne fasahar Intanet. Wannan shi ne titin da wadancan bayanai da ke ma’adanar da bayaninsu ya gabata, suke bi a yayin da ka bukace su daga inda kake, a ko’ina ne kuwa a fadin duniyar nan.  Kada ka mance, a tsarin “Cloud Computing,” bayanan da kake mu’amala da su ba a kan waya ko kwamfutarka suke ba. Dole sai da Intanet za ka iya riskarsu.

Sai rukuni na karshe, wato na’urar sadarwar da kake amfani da ita wajen isa ga wadancan bayanai ko manhaja. Wannan kuwa ya hada da wayar salula da kwamfuta da iPad ko duk wata na’ura da ke iya aiwatar da sadarwa a tsakaninta da wata na’ura ’yar uwarta. Wannan ya hada da talabijin da na’urar dafa abinci (oben) da na’urar wanki (washing machine) da na’urar wanke farantai ko kwanukan abinci (dish washer), wadanda suke dauke da tsarin da ke taimaka musu wajen aiwatar da sadarwa a tsakaninsu da duk wata na’ura ko muhallin da ke iya hakan.

Wannan, a takaice shi ne dan abin da zan iya cewa a halin yanzu. Kamar yadda na yi alkawari, da zarar mun gama amsa tambayoyi, za mu kutsa cikin wannan fanni in Allah Ya so. A ci gaba da bibiyarmu.  Na gode.

(Za mu ci gaba mako mai zuwa)