✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (4)

Assalamu alaikum Baban Sadik da fatan kana lafiya. Don Allah wasu hanyoyi zan bi domin zama kwararre a fannin “Networking?”  Da fatan zan samu kyakyawar…

Assalamu alaikum Baban Sadik da fatan kana lafiya. Don Allah wasu hanyoyi zan bi domin zama kwararre a fannin “Networking?”  Da fatan zan samu kyakyawar amsa.  Na gode.

Adda’u Yahaya Tsangaya.

 

Wa alaikumus salam, Malam Adda’u barka dai. Hanyoyin zama kwararre a fannin “Networking” bai wuce zuwa makaranta ta kwarewa a fannin ba.  Fannin “Networking” dai yana da matakai da dama da kuma nau’o’in fannoni da dama. Amma a takaice, akwai matakai biyu shahararru wanda kamfanin Cisco da ke kasar Amurka ke bayar da takardun shaida a kansu idan aka koye su daga makarantu ko cibiyoyin da ke da rajista da su.

Matakin farko shi ne: “Certified Cisco Networking Associate,” wato: “CCNA” ke nan.  Wannan a matakin Difloma ake mallakarsa, hatta cibiyar karantar da ilimin kwamfuta ta Jami’ar Bayero da ke Kano, tana karantar da wannan fanni a wannan mataki. Mataki na biyu kuma shi ne: “Certified Cisco Networking Professional,” wato: “CCNP.”  Wannan shi ne mataki na sama, a kan na farko da bayaninsa ya gabata. Kuma da zarar ka gama samun horarwa, sai a yi maka rajista da asalin cibiyar Cisco da ke kasar Amurka da ba ka damar rubuta jarrabawar kwarewa, wato: “Certification” ke nan.  Da wannan takardar shaida duk ma’aikata ko hukumar da ke neman kwararre a wannan fanni za ta kalle ka, kuma ta dauke ka, in Allah Ya so.

Bayan Jami’ar Bayero da ke karantar da wannan fanni, akwai cibiyoyin karantar da ilimin kwamfuta irin su APTECH da NIIT, da su ma suna karantarwa, tare da shirya maka jarrabawar kwarewa ta karshe. Na kuma tabbata duk akwai su a birnin Kano da Abuja da Legas da Fatakwal da Kaduna.  Allah Ya sa a dace, Ya kuma ba da ilimi mai amfani, amin.

Assalamu alaikum, sunana Jamilu BBT Kiru, Kano.

Tambayoyina su ne: Idan zan yi anfani da manhajar “Play Store” yaya zan yi?  Kuma kamar idan zan rubuta sakon Imail nawa na kaina, yaya zan yi?  A taimaka a ba ni amsoshin tambayoyina.  Na gode.  Ina yi muku fatan alheri.

 

Wa alaikumus salam, Malam Jamilu barka da warhaka. Manhaja ko Cibiyar Play Store manhaja ce da ke dauke da dukan manhajojin da aka gina su, ta hanyoyi da ka’idojin gina manhaja da Kamfanin Google ya gindaya, don amfani da su a kan wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Android. Wannan cibiya tana nan a kan duk wata wayar salula da ke dauke da babbar manhajar Android.  Kuma akwai manhajoji nau’o’i uku. Na farko su ne wadanda dole sai ka saya, kafin ka iya saukarwa don amfani da su a kan wayarka. Na biyu su ne wadanda za ka iya saya don samun cikakken fa’idarsu, amma akwai na kyauta masu dauke da nakasa; har da tallace-tallace. Sai na uku wadanda kyauta ne su gaba daya. Wadannan sun kasu kashi biyu; akwai masu dauke da tallace-tallace a cikinsu, wadanda masu su suke amfana da su musamman idan an latsa su. Kashi na biyu kuma wadanda ba sa dauke da tallace-tallace; garau suke. Daga cikinsu akwai nau’in manhaja ta Kur’ani Mai girma mai suna: “Android Kur’an.”

Amfani da wannan cibiya mai dauke da manhajoji dai babu wahala.  Ka’ida ko sharadin kwaya daya ne; ya zama kana da adireshin Imel na Kamfanin Google, wato: “Gmail” ke nan. Tuwona maina ke nan.  Masu abu da abinsu; dan kura da kallabin kitse.  Idan ba ka da adireshin Imel na Gmail, ba za ka iya saukar da manhaja ko daya ba, balle ka yi amfani da ita a kan wayarka. Idan ka budo manhajar a karon farko, za a bukaci ka shigar da adireshinka na Imel ne, ko “lambar waya.”  Kada ka rudu.  Lambar wayar da suke nufi a nan ita ce wacce kake amfani da ita wajen shiga Gmail dinka, idan da lambar waya ka bude a matsayin suna (username). Ko kadan kada ka dauka ana nufin kowace lambar waya ce.  Idan ba ka da adireshin Imel na Gmail, za a ba ka damar bude sabo nan take. Da zarar ka bude, kai-tsaye za a zarce da kai wannan cibiya, ka kwashi garabasa a sama. Allah Ya sa a dace, amin.

 

Assalamu alaikum Baban Sadik. Da fatan lafiya, Allah Ya kara basira.  Tambayoyina su ne: Ta yaya ake gina manhaja (application)?  Sannan kai tsaye yake hawa cibiyar “Play Store?”  Kuma ana biyan wani kudi na musamma ne kafin budewa da dorawa?  Ka huta lafiya.

Daga Salmanu Mukhtar Kano.

 

Wa alaikumus salam, Malam Salmanu barka ka dai. Tambayarka ta farko kan yadda ake gina manhaja, ba ta da amsa tilo. In dai manhajar wayar salula kake nufi, kana bukatar kwarewa a fannin ilimin gina manhajar wayar salula, kamar yaren “Jaba” misali, ko “Phython.”  Sannan kana bukatar kayan aiki, wato manhajojin da ake amfani da su wajen gina manhajar, irin su: “Android Studio” da asalin manhajar “Jaba” da dai sauran kayayyaki. Don samun cikakken bayani, na zayyana wadannan abubuwa a cikin kasidar da na gabatar mai take: “Tsarin Babbar Manhajar Android,” kashi na 7. Kuma kana iya samun kasidar a shafina da ke: <http://www.babansadik.com/category/wayar-salula>.

Tambayarka ta biyu na son sanin ko kai-tsaye manhajar da ka gina za ta samu hawa wannan cibiya. Amsar ita ce: a’a. A matsayinka na kwararre mai gina manhaja, dole ka yi rajista a Kamfanin Google, wanda wannan shi ne zai ba ka damar yin gwaji a karon farko, wajen ganin ko manhajar ta cika ka’idar da Google ya tanada. Daga nan sai ka dora da kanka, a lokacin da kake so. Idan an karba za ka ga sako kan haka. Amsar tambayarka ta karshe da ke cewa ko ana biyan wasu kudade ne kafin a dora, ita ce a’a. Muddin dai ka yi rajista da Kamfanin Google, wanda rajistar kyauta ne, sannan manhajar da ka gina ta cika ka’idar muhallin, ba ka bukatar biyan wani kudi.  Da fatan ka gamsu.

 

Za mu ci gaba mako mai zuwa