✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (5)

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah shawara nake nema da karin haske a kan karatu a fannin “Cyber Security” da kuma damarmakin aiki da yake…

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah shawara nake nema da karin haske a kan karatu a fannin “Cyber Security” da kuma damarmakin aiki da yake da su.  Saboda na samu gurbin karatu ne a mataki na biyu a Jami’ar Bayero, Kano.  Na gode. 

[email protected]

Wa alaikumus salam, Malam Shamsu barka ka dai, kuma ina maka fatan alheri.  Yadda ka fara lafiya, Allah sa ka gama lafiya, ka samu fitowa da sakamako mai kyau wanda zai amfane ka da al’umma baki daya, amin.  Hakika nakan yi farin ciki a duk sa’ar da na ga matasa na samun gurabe don karantar fannoni irin wadannan, wadanda a duk duniya yanzu da su ake tinkaho.  Ina son sanar da kai cewa, shekaru sama da goma da bayyanar wannan shafi, ya zaburar da matasa da dama wadanda suka nuna kansu na son su karantar ilimi da kwarewa a fagage masu alaka da kimiyyar fasahar sadarwa na zamani.  Kai ma ina maka barka da zuwa wannan fage.

Dangane da tambayarka cewa wadanne damarmaki ne wannan fanni na “Cyber Security” yake dauke da su kan batun aiki ke nan, bayan an kware, to, da farko dai wannan fanni na “Cyber Security,” kamar yadda ka sani, fannin da ke karantar da dalibai hanyoyin kare bayanai ta hanyar kayayyaki da na’urorin sadarwa ne a Intanet.  Ma’ana, yadda sojojin kasa da na ruwa da na sama ke kare kasa a zahirin rayuwa, inda ido ke ganin ido, wannan fannin a bayar da kariya ne a giza-gizan sadarwa na duniya.  Shi ya sa kalmar “Cyber” ta zo cikin sunan fannin. Sabanin zamanin baya da galibin hanyoyin tsaro na zahiri ne kadai ake la’akari da kuma tanadi gare su don kare dukiya da rayuwar al’umma, a yanzu yaki ya koma giza-gizan sadarwa na duniya.  Yadda ake kai hari ta teku, ko sararin samaniya, ko iyakar wata kasa, haka ake kai wa kasashe hari a yanzu ta hanyar Intanet.  To, wannan fanni na karantar da masu koyonsa ne yadda ake kare kwamfutoci da wayoyin salula da bayanai na mutane ko na hukuma da kwamfutocin da ke dauke da manhajojin da ke sarrafawa su kayayyakin sadarwar da kasar ke amfani da su.

Shekaru kusan shida da suka gabata na gabatar da kasida da aka buga a wannan shafi mai albarka, mai taken: “Dandatsanci: Wani Sabon Salon Yaki Tsakanin Kasashe a Duniya,” inda na zayyana ire-iren hare-haren da kasashe ke kai wa wasu kasashe da suke zaman doya da manja da su, ta hanyar Intanet.  Na kuma nuna cewa babu wata kasa da ta kubuta daga irin wannan aiki, domin ya zama ruwan dare, gama duniya.  Wadanda ake jin na suka wai su ne kasashen Amurka da Sin da Koriya ta Arewa da Isra’ila da Iran; kowace na zargin ’yar uwarta cewa ta kai mata hari na dandantsanci ga wasu kwamfutocin da ke dauke da bayanan kasarta.  Wasu kan yi haka ne ta amfani da kwararrun da suka tanada, wasu kasashen kuma suna yin hakan ne ta hanyar sojan gona.  Akwai ’yan Dandatsa na haya da dama da ke zaune, suna jiran wanda zai yi hayarsu ne kawai su yi masa aiki ya biya su.  Don haka, a wanann fanni na “Cyber Security,” za a koya maka yadda za ka kalubalanci ire-iren wadannan nau’o’im ayyukan ta’addanci ne da ke yaduwa a Intanet.  Sai dai sabanin yadda misalaina suka rinjayar, wannan fanni bai takaitu ga hukumomin kasashe kadai ba, hatta manyan kamfanonin kasuwanci da na sadarwa – irin su tarho da kwamfuta da saye da sayarwa – duk suna da bukatuwa zuwa ga masu kwarewa a wannan fanni.

Don haka, idan har ka kware a wannan fanni, hukumomin tsaron Najeriya na iya daukarka aiki, domin a halin yanzu ma hukumar sojin Najeriya ta kaddamar da cibiyar tsaron kasa ta hanyar giza-gizan sadarwa a bara, don bibiyar hanyoyin da kasarmu ke samun barazana a wannan bangare. Bayan haka, Hukumar Yaki da Tu’ammali da Kudaden Haram ta Kasa wacce aka fi sani da EFCC a gajarce, tana iya daukarka aiki.  Domin hukumar na da cibiya ko sashe na musamman da ke lura da kafafofin sadarwa na zamani wajen aiwatar da laifuffukan da suka shafi sace kudade da wadansu ke yi.  Har wa yau, hukumar ’yan sanda ma na da bukatuwa ga wannan ilimi, da sauran hukumomin tsaro irin su Kwastam da Magireshan da ICPC da Babban Bankin Najeriya, (CBN), duk suna daukar kwararru a wannan fanni.

A daya bangaren kuma, zamani ya canja sosai, ba wai sai hukumomin gwamnati ba kadai, akwai kamfanoni masu zaman kansu, wadanda ke tu’ammali da bayanai masu dimbin yawa, kamar kamfanonin sadarwar wayar salula, irin su: MTN da 9Mobile da Airtel da Glo, duk suna daukar masu kwarewa a wannan fanni sosai.  Idan muka koma bangaren kamfanonin kasuwanci ma haka abin yake.  Ba nan kadai ba, idan Allah Ya sa ka dace, har kasashen waje kana iya samun aiki, musamman a manyan kamfanonin sadarwa na duniya masu rassa a Najeriya, irin su Google da Microsoft da IBM da sauransu, duk suna iya daukarka aiki.

Shawarar da zan ba ka a nan ita ce, idan Allah Ya sa ka gama lafiya ko kuma kafin ka kammala karatun, ka yi kokari ka kware a daya daga cikin fannonin gina manhajar kwamfuta, irin su Jaba, ko Python, ko JabaScript da CSS da HTML, ko kuma wani ilimi da ke da alaka da wadannan.  Wannan zai taimaka maka matuka wajen sanin aiki cikin sauki.

A karshe ina maka fatan alheri da gamawa lafiya.  Allah maka jagora, amin.