✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (6)

Assalamu alaikum, barka da wannan lokaci. Ina daga cikin tsofaffin dalibanka a shafin Kimiyya da Kere-kere. Na karu matuka da rubuce-rubucenka. Kana daya daga cikin…

Assalamu alaikum, barka da wannan lokaci. Ina daga cikin tsofaffin dalibanka a shafin Kimiyya da Kere-kere. Na karu matuka da rubuce-rubucenka. Kana daya daga cikin dalilan da yanzu haka suka sa nake koyon dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming Languages). Ina maka addu’ar Allah Ya kara maka lafiya da imani da ilimi da nisan kwana. Daga karshe, shin, zan iya tuntubarka wajen neman shawarwari ta wannan lambar a koyaushe, ko akwai wani adireshin naka daban? Asha ruwa lafiya. 08149273937

Wa alaikumus salam, ina godiya matuka da addu’o’inku. Allah Ya ba mu dacewa baki daya da amfanuwa da abin da muke karantawa a wannan shafi mai albarka. Na yi farin ciki matuka da jin haka.  Dama manufar samar da wannan shafi shi ne don karuwar al’umma, musamman da nau’o’in ilimi na zamani da kowace al’umma ke tinkaho da shi a yau.

Daga lokacin da na fara rubutu a wannan shafi, cikin watan Oktoban shekarar 2006, wato shekarar da aka fara buga jaridar AMINIYA ke nan, da yawa cikin masu karatu sun aiko sakonni makamantan wannan. Kuma wannan ke nuna cewa ana fa’idantuwa da bayanan da muke kwararowa. Hatta masu karatun digiri na uku (PhD) suna amfana da wannan rubutu sosai. Akwai wadanda suka bukaci in aiko musu wani bangare na rubuce-rubucen da na yi a baya a wasu fannoni na sadarwa, suna karatun PhD a wasu kasashe na Afirka. Wannan abin alfahari ne ba gare ni ba kadai, ga Hukumar Kamfanin Media Trust, wacce ke samar da wannan jarida a duk ranakun Juma’a.  Allah Ya saka mata da alheri da sauran ma’aikata da editocin da ke kashe lokuta don ganin kowane shafi ya kintsu a kan lokaci.

A karshe, kana iya tuntubata ta wannan lambar, ta hanyar sakon tes, kamar yadda ka rubuto yanzu.  Idan bukata ce mai tsayi, kana iya aiko bukatar mu yi magana kai- tsaye, duk da yake sakonnin tes kadai nake karba a wannan layin, amma zan iya kiranka don bayar da tawa gudunmawa iya karfina. Haka kuma, kana iya aiko sako ta adireshin Imel din TASKAR BABAN SADIK, wato: [email protected].  Na gode matuka.

 

Salamun alaikum Baban Sadik yaya aiki, ina fata ka sha ruwa lafiya.  Allah Ya sa mu dace amin.  Don Allah Baban Sadik shafin Facebook dina aka yi hacking.  Yaya za a yi in dawo da shi? Na gode Allah Ya saka da alheri.

Daga Kamaliddeen, Kano 07046357914

 

Wa alaikumus salam, Malam Kamalu barka ka dai. Abin da zan iya fahimta dai a takaice, shi ne, wani ya kwace shafinka.  Hanya mafi sauki ita ce ka kai koke ga hukumar Facebook don su taimaka maka cikin sauki. Wannan wani abu ne da suka saba yi. Domin ko na ce zan yi maka bayani filla-filla kan yadda za ka dawo da shafin ba lallai ba ne ka fahimta cikin sauki, sannan bayanin zai tsawaita matuka. Ka shiga wannan adireshin: https://m.facebook.com/hacked.

Shafi ne na musamman da hukumar Facebook suka tanada musamman don saurara da karbar koken masu matsala irin wannan. Sun san ana sace shafukan mutane. Sun san irin badakalar da ke faruwa a wajen. Domin a duniyar Intanet gaba daya babu inda ake aikata manyan laifuffuka cikin sauki irin dandalin Facebook. Kawai ya danganci saninka ne ko idan abin ya shafe ka. Don haka, ka hau shafin sai ka ba su bayanan da za su bukata. Kafin nan, ka tanadi hoton ID Card dinka na makaranta ko wajen aiki ko wanda Gwamnatin Najeriya ta ba ka, irin katin zabe, ko katin shaidar zama dan kasa “National ID Card,” domin za su tambaye ka ko ma su ce ka loda musu hotonka mai dauke da wadannan bayanai.  Manufar ita ce don su tantance kai ne hakikanin mai shafin tukun, kafin a je batun taimaka maka wajen karbo shafin. Kada a yi kitso da kwarkwata. Ina yi maka fatar alheri kuma Allah Ya sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, fatar alheri. Ina da tambaya kan bude shafin facebook ne; idan na fara bude facebook sai in sa sunana da sunan mahaifina, to sai a bukaci lambar waya ko email address.  Wannan lambobi su ne?  Ban gane ba; lambar wayar da nake amfani da ita ce ko wata ce daban?

Daga Idris Musa, Ilorin, Kwara:  08034988388.

Wa alaikumus salam Malam Idris barka ka dai. Lallai lambar da ake bukata taka ce, ko adireshin Imel. Domin su ne za su wakilce ka a tashar Facebook din, kuma da su za a yi amfani wajen nemanka ko hada ka da mutanen da kuke da kamanceceniya na alaka ko wurin zama ko harkar rayuwa iri daya. Idan ka shigar za a aiko maka lambobi don tantance kai ne, daga nan shafi ya samu.

Da fata ka gamsu.  Allah Ya sa a dace, amin.