Da Dumi Dumi

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (7)

Dikoda da faifan DVD a jiki
Dikoda da faifan DVD a jiki

Assalamu alaikum, gaisuwa da fatar alhaeri. Yarona ne ke son zama kwararren injiniya a kan gyaran waya da kwamfuta.  Shi ne nake son sanin matakan da suka kamata mu bi tun daga matakin sakandare zuwa jami’a da irin kwasa-kwasan da suka kamata a dora shi don cimma burinsa na rayuwa. Yanzu haka yana karatu a daya daga cikin Technical School a Katsina. Na gode. Abu Mus’ab, Kaduna. 08033602969

Wa alaikumus salam, barka ka dai Baban Mus’ab, godiya nake da fatar alherin da ake mini. Dangane da manufar dora danka a fannin ilimin da ya danganci injiniya na gyaran wayar salula, ina iya cewa wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci.  Na farko dai zai samu aikin yi kai-tsaye.  Na biyu zai zama mai daukar wadansu aiki.  Na uku, wanda ya fi muhimmanci, shi ne zai rika koya wa wadansu, har su kware kamar yadda ya  kware shi ma.  Samun irin wannan tsari da tafarki a aikace, musamman a wannan lokaci da muke fama da rashin aikin yi a kasarmu, abu ne da zai taimaka matuka wajen fitar da matasanmu daga kangin rashin aikin yi da zaman banza da kuma shaye-shaye.

Duk da cewa ban san kwasa-kwasan da wannan makarantar koyon sana’a da ke Katsina take karantarwa ba, amma a jami’o’inmu ban ce akwai wani fanni na musamman don karantar da  fannin gyaran wayar salula ba. Amma zai iya daukar fannin Computer Engineering. Fanni ne da ya shafi yadda kwamfuta ke aiki da yadda ake kwance ta da gyara ta da kuma kirkirar abubuwan fasaha daga gare ta.  Sai dai hakan ya danganci tsarin makarantar. Akwai jami’o’in da suke karantar da wannan fanni a aikace, wato a koya maka yadda komai ke gudanuwa da yadda kai ma za ka aiwatar da karatun, ba wai a nazarce kadai ba. Amma galibin makarantunmu suna karantar da ire-iren wadannan fannoni ne a nazarce, sai in dalibai sun yi sa’ar malamin da zai fuskantar da su ta hanyar ba su ayyukan gida a aikace da sauran dabarun kwarewa.

A tare da haka, shawara ita ce, ko ma wane fanni ya karanta, zai iya kwarewa a fannin gyaran waya sosai.  Sirrin na cikin abubuwa guda uku ne. Abu na farko shi ne, ya zama yana da sha’awa kan fannin sosai. Wannan zai sa ya yawaita karance-karance da mayar da hankali kan abin. Abu na biyu shi ne, ko dai ya samu kwarewa a makaranta ta musamman inda ake karantar da wannan fanni a aikace, ko kuma a nema masa wani kwararren mai gyaran waya inda zai koya a aikace. Abu na uku shi ne, duk wata na’ura ko kayan aiki da zai bukata, a saya masa.  Wannan zai taimaka masa wajen kwatanta abin da yake koya ba tare da fargaba ba.  Domin shi wannan fanni fa fanni ne da ke bukatar aikatawa. Ba wai tsantsar karatu ke sa a kware a kai ba. Ba kamar fannin tarihi ba ne.

Wannan shi ne dan abin da zan iya bayarwa na shawarwari da fuskantarwa.  Allah Ya sa a dace, amin.

ADVERTISEMENT

 

Assalamu alaikum, barka dai. Don Allah Abban Sadik, ina son ka fada mini shafin da zan rika saukar da manhajar kwamfuta kamar yadda ake yi a wayoyin salula na zamani ta hanyar cibiyar Playstore. Kuma don Allah ina son ka rubuto mini sunan makarantar da zan yi karatu ta kafar Intanet. Na gode:  abdulmalikhassandanmoyi@gmail.com  08173472741

Wa alaikumus salam, Malam Abdulmalik. Da farko dai ina ba ka hakuri sanadiyyar kin daukar kiranka a lokuta daban-daban. Hakan ya biyon wasu dalilai ne guda biyu. Na farko shi ne, na ce tes kawai za a rika aikowa a wannan layi. Idan kana da bukatar zantawa da ni ka sanar da ni ta tes, zan iya ba ka lokaci na musamman da za ka kira ni ko ni in kira ka sai mu tattauna in saurari bukatarka. Dalili na biyu kuma shi ne yanayin shagulgula da ke gabana. Wannan yana cikin dalilan da suka sa kawai sakon tes nake karba a layin ba kira. Idan na ce zan saurari kowa ya kira, to, ba zan iya gabatar da komai nawa ba. In ka lura, tun cikin watan Yuli muke ta amsa tambayoyin masu karatu, har yanzu kuma ba mu gama ba. Ka kaddara kirana kowanne daga cikin masu sakonnin nan ya yi; yaushe zan iya biya wa kowa bukatarsa?  A gafarce ni.

Dangane da bukatarka kuma, ina son ka san cewa, tsari da kintsin wayoyin salula na zamani da irin babbar manhajar da suke amfani da ita ya sa aka samar musu da tsari na musamman wajen saukar da manhajoji masu tsabta kuma cikin sauki, galibinsu ma kyauta. Amma kwamfuta ba ta samu wannan gata ba. Tabbas akwai wuraren da za ka iya saukar da manhajojin kwamfuta kyauta, amma ba su da tsabta. Kuma suna iya cutar da kwamfutarka ko da kuwa kana da manhajar kariya daga kwayar cutar kwamfuta, wato, “Anti-birus.”

Akwai daidaikun shafukan Intanet da ke dauke da manhajoji na kyauta zalla. Wadannan su ake kira: “Shareware” ko “Free Applications.”  Galibin wadannan za ka samu suna dauke da tallace-tallace a soke a cikinsu.  Idan ka zo loda wa kwamfutarka, kuma aka yi rashin sa’a ba ka san kan abin ba, za ka yi kitso da kwarkwata. Sai bayan kwana biyu sai ka fara ganin wasu dabi’u marasa kan-gado da kwamfutarka ke nunawa. Ba komai ba ne illa kwaya ta sha, wanda aka dura mata ta hanyar wadancan manhajoji na kyauta. Hausawa kan ce: “Araha ba ta ado.” Daga cikin shafukan da za ka iya samun wadannan nau’ukan manhajoji akwai shafin CNET (<http://download.cnet.com>), sai kuma shafin Softonic (<http://en.softonic.com>). Sannan akwai shafi na musamman inda za ka samu manhajojin da ba ka bukatar loda wa kwamfuta, wato: “Installing.” Su kawai manhajoji ne na tafi-da-gidanka.  Amfaninsu galibi idan ka yi aron kwamfuta ne, ba ka son loda manhajojin da kai kadai ne za ka yi amfani da su, ko kuma ba ka da damar da za ka iya loda manhaja, sanadiyyar karancin ’yanci da aka ba ka. Hakan kan faru ga kwamfutocin da ofis ke bai wa ma’aikata.  Akwai manhajoji na al’ada, gama-gari (irin su Google Chrome, Mozilla Firefod da sauran makamantansu). Wadannan su ake kira “Portable Apps.” Idan ka saukar sai dai ka matsa, nan take za su budo sai ka yi amfani da su.  Idan ba ka bukata, sai kawai ka goge su (Delete) daga kan kwamfutar shi ke nan. Ka je shafin PortableApps da ke: <https://www.portableapps.com>

Akwai wadanda ke dauke da manhajoji na kyauta amma masu nakasasshiyar siffa da aiki. Asalinsu na sayarwa ne, amma idan kana son gwadawa don ganin yadda suke aiki, sai a ba ka kyauta ka dandana. Idan ka gamsu, sai ka saya. Wadannan su ake kira: “Trial Bersion Applications”. Kana iya samunsu a shafukan manya-manyan kamfanonin kwamfuta irin su Microsoft da Adobe da IBM da sauransu. Za a ba ka kyauta na wasu ’yan kwanaki ko watanni. Galibi bai wuce kwana 90; wata uku ke nan. Da zarar kwanakin sun kare, sai ka kasa amfana da manhajar, saboda irin kariyar da suka sanya a ciki.

 

Share