Da Dumi Dumi

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (7)

Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (7)

Assalamu alaikum, Baban Sadik Allah Ya kara basira. Don Allah tambaya nake a kan “Nokia Lumia 1350”; ana iya Upgrading dinta ta koma Android? Muna godiya. Yakub Z.

Wa alaikumus salam Malam Yakubu, barka dai.  Ina godiya da addu’a. Ita wayar salula nau’in Nokia Lumia tana dauke ne da babbar manhajar “Windows Phone,”wadda Kamfanin Microsoft ya gina kuma yake dora wa kwamfutocinsa. Duk tsare-tsarenta na babbar manhajar “Windows Phone” ce, don haka a al’adance babbar manhajar “Android” ba zai yi mata ba. Amma duk da haka an samu wadanda suka yi yunkurin mayar da wayar salula nau’in Lumia zuwa Android, kuma sun dace, amma tare da wasu matsaloli masu yawa, wadanda gwamma ma rashin yin hakan.  A tare da dacewar ma, ba dukan nau’o’in Lumia ba ne ake iya dora musu babbar manhajar Android.  Nau’o’in Lumia da aka gwada kuma aka dace suka dauki babbar manhajar Android dai su ne tsofaffin nau’o’in Lumia, irin su: Lumia 520 da Lumia  521 da Lumia  525 da Lumia  526, sai kuma Lumia 720.

Bayan gwajin da aka gudanar kuma aka dace suka dauki babbar manhajar Android, wayoyin sun tashi, dauke da manhajar Android din, amma kuma fasahar Bluetooth ba ta yi. Haka ma na’urar sauraron sauti (Earpiece) ba ta yi. Haka ma manhajar daukar hoto (Camera) ita ma ba ta yi.  Mafi girman matsalar ma ita ce, bayan an dora musu babbar manhajar Android, an lura wayoyin duk ba su iya kamo siginar rediyo, wanda da shi ne kowace wayar salula ke amfani wajen karba da amsa kira, tare da shiga Intanet. Wannan ya faru ne saboda ka’idojin da aka gina asalin wayar sun sha bamban da tsarin da aka kintsa cikin babbar manhajar Android. Ke nan, akwai-ya-babu-ne.

Idan kana bukatar mayar da wannan wayar zuwa nau’in Android, zai dace ka kai wa masu gyara, wadanda suka kware wajen iya gyaran wayar salula.

Su za su duba su gani, idan har zai yiwu a farke ta don dora mata babbar manhajar Android din, za su sanar da kai. Amma kamar yadda ka gani, wannan wayar da kake tambaya a kanta ba ta cikin wayoyin da aka yi ittifakin za su iya karbar babbar manhajar Android.  In kuwa ba zai yi dole ba sai ka yi, shawarata ta karshe ita ce, ka sayar da ita ka sayi sabuwar wayar salula mai dauke da babbar manhajar Android. Akwai su da yawa kuma masu inganci, wadanda za su iya gudanar maka da duk abin da kake son wayar salula ta yi maka.

ADVERTISEMENT

A takaice dai, su wayoyin salula kamar motocin hawa ne; muddin ba asalin injinsu ba ne ka dora musu, to, sai an samu matsala.  Da fatan ka gamsu da dan takaitaccen bayanina.  Allah Ya sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik. Da fatan kana lafiya. Ina bukatar bayani a kan na’urar cire kudi ta ATM, a sawwake.  Daga Abdullahi Jalingo.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdullahi. A baya mun gabatar da bayani mai tsayi kan wannan na’ura tun farkon bayyanarta a Najeriya. Amma a takaice, na’ura ce da ake amfani da ita wajen cire kudin da ka adana a taskar bankinka.  Bayan cire kudi ma, kana iya amfani da na’urar ATM wajen aike wa wani kudi kai-tsaye, wato “Instant Transfer” ke nan. Abin da haruffan “ATM” ke nufi shi ne, “Automated Teller Machine,” wato na’urar bayar da kudi mai sarrafa kanta. Wannan na’ura dai tana dauke ne da manyan bangarori guda uku. Na farko shi ne asalin na’urar, wato kwarangwal dinta ke nan. Wannan shi ake kira “Hardware.”  Sai bangare na biyu wanda ya kunshi manhajar da ke sarrafa na’urar, wannan shi ake kira: “Software.”  Sai bangare na uku da ya kunshi yanayin sadarwar da na’urar ke amfani da shi wajen aiwatar da harkokinta. Wannan kuwa ya hada da tsarin sadarwa a tsakaninta da kwamfutocin da ke sarrafata daga cikin bankin da take makale a farfajiyarsa. Sai kuma yanayin sadarwar da ke hada alaka tsakanin ita na’urar da kuma kamfanin da ke aiwatar da tsarin musayar kudade a tsakanin bankuna a Najeriya. Wannan kamfani shi ake kira “Interswitch.” Shi kadai ne ke da alhakin wannan aiki a Najeriya a halin yanzu.

Yadda wannan na’ura ke aiki kuwa shi ne, a duk sa’ar da ka zo ka zira katinka a cikinta, za ta bukaci ka ba ta kalmar sirrin da bankinka ya ba ka sa’ar da kake karbar katin. Da zarar ka rubuta, za ta tambaye ka me kake son yi? Kana iya zabar cire kudi, ko duba balas, ko sauya kalmar sirri ko wani abu daban. Da zarar ka zaba, sai a kai ka inda kake so.  Idan cire kudi ne, za a tambayi nau’in taskarka; “Current” ne ko “Sabings?” Idan ka zaba, nan take sai na’urar ta kai ka inda za ka zabi adadin kudin da za ka cire. Kana gaya mata, sai ta aiwatar da sadarwa da bankinka don tabbatar da samuwar adadin kudin da kake son cirewa.  Idan ka cika ka’ida, sai kawai ta aiko maka. Idan kuma na’urar da kake amfani da ita ba na bankinka ba ne, bayan an ba ka kudin kuwa, sai Kamfanin Interswitch ya zaftare adadin kudin da na’urar ta ba ka daga taskarka dake bankinka, ya zuba a taskar bankin da ka ciri kudin daga na’urar ATM dinsu.

Wannan a takaice shi ne bayani kan na’urar ATM. Don karin bayani, kana iya ziyartar shafin TASKAR BABAN SADIK don karanta asalin kasidar da na gabatar kan wannan na’urar, shekara 8 da suka shude. Kana iya isa ga wannan kasida a wannan adireshi: https://www.babansadik.com/yadda-naurar-atm-ke-aiki-1. Da zarar ka je karshen wannan kasidar, za ka ci karo da kashi na biyu.  Allah Ya sa a dace, amin.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya