Amsoshin sakonni da tsokacin masu karatu (8)

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina yi maka fatan alheri tare da godiya kan abubuwan da muke amfanuwa da su. Allah Ya kara basira. Ina neman shawararka game da wani wanda ya sace min account dina na Facebok ya canja sunana kuma yake amfani da sunansa.  Amma kuma da abokaina yake mu’amala.  Ta yaya zan dawo da sunan nawa? 

 

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Idris. Ina godiya da addu’o’i. Dangane da bukatarka kan wanda ya sace maka shafinka na Facebook, ya canja sunan sannan yake mu’amala da abokanka da shafin, zai dace in san shin, zuwa yanzu da aka kwace maka shafin, kana iya hawa shafin ne?  In eh, to, sai ka canja kalmar sirrinka kawai kai-tsaye ba tare da wani bata lokaci ba.  Bayan ka canja kalmar sirri, sai ka je bangaren “Settings” ka canja sunan zuwa sunan shafin na asali. Wannan zai kare shafin nan gaba daga kutse.

Amma idan ya kwace shafin ne gaba daya ba ka iya komai a kai, shin, ya cire lambar waya ko adireshin Imel din da ka sanya a shafin ne? Za ka iya gane hakan idan ka yi kokarin hawa shafin da “Password” dinka na baya, za a ce ba daidai ba ne, “Kana son canja password dinka ne?” Sai ka matsa eh. Daga nan za a zarce da kai wani shafi mai dauke da bayanan da kake amfani da su wajen hawa shafin. A nan ne za ka gane idan ya cire su ko bai cire ba. Idan bai cire su ba, to, abin da sauki, wai cire wando ta ka. Sai kawai ka bukaci a aiko maka lambobin tantancewa (Berification Code) zuwa lambar waya ko adireshin Imel din. Ana aiko maka sai ka yi maza ka shigar a inda aka tanada, za a zarce da kai shafin da za ka sanya sabuwar kalmar sirri (Password). Da zarar ka canja sai kawai ka je bangaren “Settings” ka canja sunan zuwa sunan da kake sha’awa. Sai dai kuma wani abin lura, idan har bai kai watanni shida da canja sunan ba, ba za a bari ka iya sake canja sunan ba sai bayan wata shida.

To, amma idan ka samu ya cire dukkan bayanan da Facebook za su iya tuntubarka da su ya sanya nasa, a nan kam sai hakuri, a galibin lokuta. Don haka, idan ka tarar da hakan, kana iya tuntubata ta hanyar aiko mini sakon tes (kada ka kira layin), don duba lamarin, in ga ko za a iya kwato shafin.

ADVERTISEMENT

Wannan shi ne takaitaccen bayanin da zan iya yi. Allah Ya sa a dace, Ya kuma yi jagora, amin.  Na gode.

 

Assalamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce: Ina da waya kirar Lumia wajen shekara 3 ke nan amma ta ki yin setting, kuma ba ta shiga yanar gizo.  Har ofishin MTN na kai ta amma abin ya gagara.

Daga A’isha Tudun Maliki.

 

Wa alaikumus salam, barka dai Malama A’isha. Duk da cewa baki yi cikakken bayani kan kirar da nau’in Lumia din ba, ga alama tsohuwar yayi ce. Abin da ke faruwa shi ne, Kamfanin Microsoft, wanda shi ne mamallakin wadannan nau’o’in wayoyin salula na zamani, ya daina bai wa tsofaffin nau’o’in wayoyin Lumia sakonnin tagomashi da zai kara musu inganci ta hanyar sabunta su.  Abin da wannan zance ke nufi dai a fayyace shi ne, ire-iren wadannan wayoyin salula an daina yayinsu.  Na farko ke nan.

Na biyu, ban san me ke damun wayarki ba wanda ya hana ta iya tagaza komai, amma ga alama matsalarta ba karama ba ce; tunda har kin kai ta ofishin MTN amma su ma sun kasa yin wani abu, kamar yadda kika fada.  Shawarata ita ce, in da hali a samu sabuwa a saya. Akwai wayoyi nau’o’i daban-daban masu inganci, kuma masu arha, wadanda za su iya yin komai babbar waya za ta iya yi ta hanyar yin kira da amsa kira da hawa Intanet. Wadannan sun fi samar da natsuwa da kwanciyar hankali.  Amma gyara tsohuwar waya wacce kamfanin da ya samar da ita ma ya daina sabunta bayananta, kashe kudi ne kuma ba lallai a samar da cikakkiyar biyan bukata ba.

Wannan ita ce shawarata, kuma ina miki fatan alheri.  Na gode.

 

Assalamu alaikum Baban Sadik, Allah Ya taimaki gwanina a duniyar Intanet. Ban ga mutum mai son taimakon al’umma ko son ci gaban al’ummar Hausawa a wannan fanni irinka ba. Wallahi ban ganshi ba har yanzu. Allah Ya taimake ka a kan wannan manufa naka.

Daga sabon mai bibiyarka Muhammad bin Muhammad, Numan, Jihar Adamawa.

 

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Muhammad, mai babban suna. Ina godiya matuka da addu’o’inka da kuma kyautata mini fata da ka yi. Duk abin da kake ganin yana burge ka daga gare ni, kyautar Allah ce da dacewa cikin ganin damarSa. Wallahi ba hikima da kokarina ba ne. Fatata ita ce, duk abin da nake rubutawa, wanda sakamakon bincike ne da nake gudanarwa da kuma fahimtata kan abubuwan da nake karantawa, ya zama mai amfani da ga al’umma, ya samar da fa’ida ta hanyar inganta fahimta da tunanin wadanda suke karantawa.  Abin da yake kuskure ne kuma, Allah nusar da su su gane hakan, kada su hakkake kuskure a cikin kwakwalwa da zukatansu.

Ina yi maka fatan alheri a ko’ina ka samu kanka.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya