Da Dumi Dumi

Amsoshin sakonni masu karatu ta tes da imel

Assalamu alaikum Baban Sadik, tambayata a kan Google ne; shin, ta yaya aka samar da shi, kuma yaya yake ajiye bayanai a cikin kwamfutocinsa, kuma shin, ko akwai hukuma mai kula da wannan shafi?

Daga Nasiru Dauran, Talata Mafara, Zamfara

Wa alaikumus salam, Malam Nasir barka ka dai.  Shafin Google, ko Manhajar Google, ko Kamfanin Google, duk abubuwa ne da suka dunkule zuwa abu daya. Idan ka ce “Google”, to, hakan na ishara ne zuwa ga dukkan ukun nan, ko biyunsu, ko daya daga cikinsu.  Asali manhaja ce ta zakulo bayanai da wasu samari su biyu suka gina, tun cikin shekarar 2005.  A lokacin, suna karatunsu na digiri na uku a Jami’ar Stanford da ke kasar Amurka. Wadannan samari su ne: Larry Page da Sergey Brin.  Sannan shekarunsu duk ba su shige 25 ba a duniya.

Samar da wannan manhaja ta neman bayanai ne ya haddasa kafa kamfani da gidan yanar sadarwa mai dauke da manhajar, don taimaka wa masu neman bayanai don bincike ko gamsarwa ta ilimi, samun bayanai ba tare da wata matsala ba. Wannan gidan yanar sadarwa na Google (www.google.com) yana dauke da wata manhaja mai suna “Google Crowler,” wacce ke yawo a giza-gizan sadarwa ta duniya (World Wide Web) don debo bayanai, ta amfani da rariyar likau (Web Links), tana zuba wadannan bayanai a kwamfutocin kamfanin, a tsarin ABCD…DYZ.  Wannan tsarin adana bayanai shi ake kira “Indeding” a harshen kimiyyar sadarwar zamani. Da zarar ka shiga gidan yanar sadarwar ka shigar da kalma, nan take sai wannan manhaja ta zakulo maka dukkan bayanai masu alaka da wannan kalma da ka shigar, ta zuba maka su a gabanka; zabi wanda kake so. Idan ka latsa nau’in bayanin da kake son isa gare shi, sai a cilla ka asalin gidan yanar sadarwar da ke dauke da bayanan kai-tsaye, ka duba da kanka.

A hakikanin gaskiya babu wata hukuma da ke lura da wannan gidan yanar sadarwa domin na kamfani ne ba na wata hukumar gwamnati ba. Wannan kamfani na Google na kasar Amurka ne, duk da cewa yana da rassa a kusan dukkan nahiyoyin duniya. Da fatan ka gamsu.

ADVERTISEMENT

 

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah wace hanya zan bi wajen bude akwatin Imel?

Daga Baban-Yaya Dan Employer, Kwanar-Dangora.

Wa alaikumus salam, barka dai.  Bude akwatin Imel abu ne mai sauki.  Sai dai in ba wayar salula mai dauke da babbar manhajar Android kake amfani da ita ba, sai dai ka yi amfani da kwamfuta wajen yin hakan. Ka shiga wannan gidan yanar sadarwa idan na Gmail kake so: http://mail.google.com sai ka gangara kasa inda aka rubuta “Create an Account,” ka matsa, za a kai ka inda za ka cike fom ta hanyar shigar da dukkan bayanan da ake bukata daga gare ka kafin ka bude. A ciki za a bukaci ka zabi suna (username) da kalmar iznin shiga (password) da sauran bayanai.  Idan kuma Yahoo kake so, shiga nan: http://mail.yahoo.com, duk tsarin iri daya ne.  Idan wayarka ba Android ba ce, kana iya shigar da wancan adireshi na Google, amma za su bukaci ka shigar da lambar wayarka ce, sai su turo maka shafin da ke dauke da fom da za ka cike.  Da fatan ka gamsu.

 

Assalaamu alaikum, don Allah ina son a mini bayanin yadda zan adana sakon wayata cikin katin ma’adanar waya (Memory Card).  Saboda na ji ka yi bayani a jaridar AMINIYA, kuma ni lokacin da aka yi bayanin ba ni da ita.

Daga Almajirinka: Kabiru Ridwan Sakkwato.

Wa alaikumus salam, wannan ba wani abu ba ne mai wahala. Na farko ka sanya katin ma’adanar wayar a cikin waya, sannan ka je manhajar sakonni (Messages), ka shiga “Options” wato bangaren zabi ke nan. Za ka gan shi a bangaren hagu ko dama; ya danganci nau’in wayarka. A jerin bayanan da ke bangaren “Options” za ka ga inda aka rubuta “Mark All,” sai ka matsa.  Hakan zai sanya wa dukkan sakonnin da ke ciki alamar “maki” (wato check mark). Da zarar an sa musu alamar maki, sai ka sake zuwa “Options” har wa yau, ka latsa. Daga cikin jerin zabin da ke wurin za ka ga “Mobe to Memory Card” ko wani abu makamancin haka. Sai kawai ka zaba, za a kwafe su duka a kai maka su cikin katin ma’adanar wayar ba bata lokaci. Sannan kana iya kwafe su ma zuwa katin SIM dinka, duk ta wannan hanya, muddin lambobinka ba su cike ma’adanar SIM din ba.

A takaice dai, kowace irin waya kake amfani da ita, ba a rasa manhaja ta musamman da za ka iya saukarwa don aiwatar da hakan ta amfani da kwamfutarka. Sai ka jona wayar da kwamfutarka, ka bi tsare-tsaren da ke ciki, za a ba ka damar kwashe duk abin da ke cikin wayarka zuwa kwamfutarka.  Wannan ma shi ya fi sauki.

Da fatan ka gamsu.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya