Da Dumi Dumi

Amsoshin sakonni masu karatu ta tes da imel

A smartphone user shows the Facebook application on his phone in the central Bosnian town of Zenica, in this photo illustration, May 2, 2013. Facebook Inc's mobile advertising revenue growth gained momentum in the first three months of the year as the social network sold more ads to users on smartphones and tablets, partially offsetting higher spending which weighed on profits. REUTERS/Dado Ruvic (BOSNIA AND HERZEGOVINA - Tags: SOCIETY SCIENCE TECHNOLOGY BUSINESS) - RTXZ81J

Kamar yadda aka saba lokaci zuwa lokaci, ga wasu daga cikin sakonninku nan.  Don Allah a rika turo sakonni masu ma’ana, kuma a rika rubuto wuri da sunan mai aikowa.  Allah sa mu dace, amin.

 Malam mene ne ingancin kwamfuta nau’in HP da DELL wajen rike caji?

 Daga: 08073188022

A gaskiya ya danganci abubuwan da kwamfuta ke dauke da su na masarrafai da tsarin babbar manhajar da ke dauke a cikinta.  Amma la’akari da kamfanin da ya kera kwamfuta, don gano ingancin batir ba abu ba ne da zai bayar da kyakkyawan sakamako. Abin nufi, idan ana son gano karkon batir din kowace kwamfuta, ba a la’akari da kamfanin da ya kera kwamfutar, sai dai a yi la’akari da nau’in babbar manhajar da ke  cikin kwamfuta da yawan masarrafai ko manhajojin da take dauke da su.  Wani abin lura bayan wadannan kuma shi ne tsawon rayuwar batir din tun sa’ar da aka kera shi. Idan babbar manhajar da ke dauke cikin kwamfutar tana da nauyi, sanadiyyar daruruwan manhajoji da masarrafan da ke taimaka mata wajen aiwatar da ayyukanta, wannan na nufin kwamfutar za ta rika zukar makamashi sosai.  Haka idan akwai wasu abubuwa da aka makala mata don sadar da bayanai, kamar ma’adanar filash da faifayin CD/DBD da makalutun sadarwa na Intanet (Internet Modem); duk wadannan na jan makamashi musamman idan kwamfutar ba a jone take da wutar lantarki ba.  Amma la’akari da kamfanin da ya kera kwamfuta kadai ba ya nuna ga batir din da ya ya fi karko.

Idan kana son batirinka ya yi karko, ka rage yawan mu’amala da wasannin kwamfuta (computer games). Ka cire duk wata na’ura ko ma’adana da ka makala wa kwamfutar da zarar ka gama amfani da ita.  Ka rage mizanin sautinta (system bolume).  Idan akwai faifan CD ko DBD a cikin ma’adanar CD ROM dinka, ka rika cire shi, da zarar ka gama amfani da shi.  In son samu ne da zarar ka sanya faifan CD ko DBD mai dauke da sauti ko bidiyo, ka kwafe shi zuwa babbar ma’adanar kwamfutar kawai, don rage mata mizanin makamashi da za ta rika zuka. Sannan ka rage kaifin hasken shafin kwamfutar (Screen brightness).  Sannan ka bi duk inda wata masarrafa mai gudanuwa ta karkashin kasa (Background tasks) take aiki, wacce ba ka bukatarta, ka dankwafe ta. Wadannan, kadan ne daga cikin abubuwan da mai kwamfuta zai yi don rage yawan makamashin da kwamfutar take zuka idan ya zare ta daga kan wutar lantarkai kai-tsaye. Da fata ka gamsu.

ADVERTISEMENT

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah wai yaya Facebook suke hada mutum da dan uwansa ko wani wanda ya sani (People you may know)?  Abin yana ba ni mamaki, sai in ga hoton wanda na sani an kawo, ko ma dan uwana na jini; duk da ba ni na nema ba. Yaya abin yake ne? 

Daga: Usman Mu’azu Funtuwa, Katsina

Wa’alaikumus salam, Malam Usman. Barka dai,  wannan abin da kake gani kuma yake ba ka mamaki ba maita ba ce, ba kuma sihiri ba ne; kintsi ne irin na manhajar kwamfuta ta musamman da hukumar Facebook ke amfani da ita wajen hada alaka tsakaninka da wadanda ka sani ko ka san wadanda suka sansu, ta la’akari da nau’o’in bayanan da ka shigar a shafinka sa’ar da kake bude shafin ko bayan ka bude. Kada ka mance, a sa’ar da kake bude shafin ka bayar da sunanka da gari ko wurin da aka haife ka da jiharka da kasarka da addininka da ra’ayoyinka na siyasa ko addini watakila. Sannan ka fadi sunan makarantun da ka yi a baya ko kake kan yi da wuraren da ka yi aiki a baya ko kake kan yi; wadannan bayanan ne suke amfani da su wajen nemo wadanda bayanansu suka dace da naka, don haka akwai alaka a tsakaninku. Domin in har bayanan da kuka bayar (kai da su) a sa’ar da kuke bude shafinku sun zo daidai, to babu yadda za a yi a kasa samun alakar sanayya a tsakaninku.

Yadda suke amfani da wadannan bayanai wajen gano irin wannan alaka kuwa yana dauke ne cikin wani tsari da suka dunkule cikin wata manhaja mai suna: “Facebook Algorithm.”  Wannan manhaja ita ce ke da alhakin aiwatar da kashi 70 cikin 100 na abubuwan da kake gani a shafin dandalin Facebook.  Ita ce ke gano wane ne kai, kuma wane ne abokinka, kuma yaya karfin alakar dake tsakanin bayanan da ka bayar da wadanda wadansu suka bayar? Karfin wannan alaka ne ke tabbatar da abin da kake gani.  Akwai mizani na musamman da aka tsara a cikin manhajar, wanda ke gejin karfin alakokin da ke tsakanin bayanan mutane. Idan karfin alakar ta kai wani adadi na yawa, sai manhajar ta hade ku wuri daya.

Wannan shi ne abin da suke yi. Amma cikakken bayani kan yadda hakan ke faruwa ba abu ba ne mai sauki. Akwai sarkakiya sosai cikin lamarin. A takaice ma dai, a duniyar Intanet ta zamanin yau, samun shafi mai dauke da cinkoson manhajoji da sarkakiya ta kwarewa (professional sophistication), irin shafin Facebook, kamar da wuya.  Abin sai wanda ya kware a fannin kimiyyar sadarwa na zamani zai iya fahimtarsa cikin sauki. A takaice wannan shi ne abin da hukumar Facebook ke yi wajen bijiro maka da wadannan mutane da kake ganin ka san su, amma ba ka bukaci a bijiro maka da su ba, watakila ma ba ka tunanin ganinsu a shafin. Da fatan ka gane.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya