✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu (1)

Ahuwa…! Saboda wasu dalilai da suka sha karfina ba zan samu ci gaba da kasidar da muka faro makonni uku da suka gabata ba a…

Ahuwa…! Saboda wasu dalilai da suka sha karfina ba zan samu ci gaba da kasidar da muka faro makonni uku da suka gabata ba a yau, sai dai mako  mai zuwa in Allah Ya so.  A bi ni bashi don Allah. A yau ga wasu daga cikin sakonnin da kuka aiko a baya.  Da fatan za a gafarce ni. A sha karatu lafiya.

Salamun Alaikum Baban Sadeek, yaya jama’a?  Allah yasa mu dace, amin.  Don Allah yaya ake yi a fim a mayar da mutum tagwaye (‘yan biyu)?  Daga Alhassan
Wa alaikumus salam, Malam Alhassan da fatan kana lafiya.  Hakan kan kasance ne ta hanyar amfani da na’urar daukan hoto na zamani, wacce ke da ire-iren wadannan hanyoyin dabaru masu ban mamaki.  Bayan na’urar daukar hoto, akwai masarrafa ko manhajar kwamfuta mai iya aiwatar da wannan aiki cikin sauki.  Idan ka kalli fina-finai irin su Matrid misali, za ka ci karo da abubuwa masu ban al’ajabi wadanda wasu ma kana iya rantsewa ba za su iya faruwa ba, amma a fim suna faruwa.  Shi yasa ake kiran fim a hausance da suna “Shiri.”  Ma’ana wani abu ne aka shirya, ba wai hakika ba ne; kawalwalwaniya ce kawai.  Da fatan ka gamsu.
Salamun Alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya da dukkan ma’abota wannan shafi mai albarka. Ina son saka kalmomin izinin shiga (Password) na Facebook, amma ban san yadda ake yi ba.  Daga Abubakar Aminu mai Cingam, Legas: 07031105049
Wa alaikumus salam Malam Abubakar, akwai sarkakiya kadan cikin tambayarka.  Shin, daman can kana da shafi ne a Facebook?  In eh, ke nan ka mance kalmominka ke nan.  Idan kuma a a, to, ai daman babu yadda za a yi ka iya shigar da kalmomin shiga tunda baka bude shafi ba.  Idan ka mance ne, akwai shafi da za su kaika inda za a yi maka tambayoyi, da zarar ka amsa tambayoyin sai a aiko maka da fam din da za ka cika don canza wata sabuwar kalmar shiga.  Da fatan ka gamsu.
Assalaamu alaikum, Allah ya saka maka da alheri.  Ina son ka aiko mini da kasidar “Tsibirin Bamuda” da wacce ake tsara “Facebook” ta wannan adireshin Imel: [email protected].  Daga Aliyu Sadis, Minna, Neja: 08064022965
Wa alaikumus salam, Malam Aliyu ka gafarce ni saboda jinkirin amsa maka bukatunka.  Ka duba jakar Imel dinka, tuni na tura maka. Allah amfanar da mu baki daya, amin.
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, don Allah a taimaka a mana cikakken bayani kan yadda ake canza kalmomin izinin shiga a shafin Facebook.  Daga Nura Sahabi, Pangamu, Gangare, Suleja: 08034145643
Wa alaikumus salaam, Malam Nura, bayani kan yadda ake canza kalmomin shiga shi ne: ka je “Settings” a shafinka, ka gangara inda ake canza kalmomin shiga, wato Password, sai ka canza.  Wannan ba wani abu ba ne mai wahala.  A waya kake ko a kwamfuta.  Allah sa a dace.
Salaamun alaikum Baban Sadik, Allah ya taimake ka.  Wai me ake nufi da shafin musayar hoto na Pinterest, da kuma shafin Microsoft?  Kuma ya ya ake amfani dasu ne?  Daga Aminu Sadauki, Unguwar Dosa, Kaduna: 07032958029
Wa alaikumus salam, Malam Aminu barka ka dai. Shafin Pinterest dai shafi ne da ake musayar hotuna, kamar yadda ka fada.  Amma kafin ka fara amfana da hotunan wasu, sai ka yi rajista, sannan ka nemi abokai wadanda za ka iya musayar hotuna da su.  Kana da damar loda hotunanka, ka kuma killace wadanda kake son musayar wadannan hotuna da su daga cikin mambobin wannan Dandali.  Shafin Pinterest na daga cikin shafuka ko Dandalin Abota da suke tashe a wannan zamani, bayan dandalin Facebook.  A daya bangaren kuma, shafin Microsoft dai gidan yanar sadarwar kamfanin Microsoft Inc. ne da ke kasar Amurka, wanda Bill Gates da abokinsa Paul Allen suka kafa tun shekarar 1975.  A halin yanzuwannan shafi na dauke ne da bayanai kan dukkan hajojin wannan kamfani da ke gina manhajar kwamfuta, babba da karami.  Da fatan ka gamsu.
Assalaamu Alaikium Baban Sadik, ya ya aiki?  Da fatan kana lafiya.  Wai me ya sa idan mutum ya kira wani, sai a nuna masa cewa: Call is being Diberted?  Na gode.  Daga Usman Muazu Funtua, Katsina: 08106067660
Wa alaikumus salam, Malam Usman, a duk sadda ka ga haka, to alama ce da ke nuna cewa lallai mai layin ya toshe layin ne, don juya dukkan masu kiransa zuwa wani layin daban; ko don saboda matsalar rashin ingancin yanayin sadarwa, ko don rashin kudi a layin, ko wasu dalilai dai da shi kadai ya sani.  Kana iya hakan me ta hanyar hadin gwiwa da kamfanin waya, wanda hakan ke samuwa a cikin kowace wayar salula na zamani.  Da fatan ka gamsu.
Gaisuwa ta musamman ga Baban Sadik.  Ina maka fatan alheri, Allah ya kara maka basira, amin.  Tambayata ita ce: wane dalili ne yake haifar da rufewar Imel (Emel Blocking or Inbalidating of Email), sannan ta wace hanya za a iya budewa (Unlock), bayan kamfanin manhajar Imel (irin su Yahoo, ko Gmail, ko Hotmail) ya rufe?  Daga Kabir Ibn Usman, Abuja.
Malam Kabir Usman, barka ka dai. Ban da masaniya dangane wadannan kalmomi da kayi amfani da su wajen bayanin tambayarka, a ilimance.  Amma na fahimci inda tambayar ta dosa.  Akwai hanyoyi biyu da kamfanin manhajar Imel ke rufe wa mai jakar Imel akwatin Imel dinsa.  Hanyar farko ita ce dadaddiyar hanya.  Hakan na faruwa ne idan mai jakar Imel ya yi watanni 6 bai shiga akwatin Imel dinsa ba, sai a rufe. Wannan rufewa shi suke kira: Deactibation.  A duk sadda ka tashi shiga za a sanar da kai halin da akwatin Imel din ke ciki.  Amma za a nuna maka hanyar budewa, wato: Reactibation ke nan.  Amma a yanzu ma kamfanonin manhajar Imel sun daina amfani da wannan tsari.  
Sai hanya ta biyu, wacce ke samuwa sanadiyyar canza tsarin shiga Imel dinka, ko na’urar da kake amfani da ita wajen shiga.  Misali, idan ka saba shiga akwatin Imel dinta ta hanyar kwamfuta ce, sai kwatsam watarana ka bukaci shiga ta hanyar wayar salularka a karo na farko, kamfanin manhajar Imel zai dauka ba kai ba ne, wani ne ke kokarin shiga ba izini, don haka sai a toshe akwatin, ace sai ya fadi ranar haihuwar da ya bayar a sadda yake cike fam din bude akwatin, ko a ce ya fadi amsar tambayar sirri da aka masa sadda yake bude akwatin.  Masu Dandalin Facebook ma kan yi amfani da wannan tsari wajen tantance hakikanin mai shafi idan ya shiga ta hanyar da bai saba ba.  Abin da wannen ke nufi shi ne, a duk sadda kake shiga akwatin Imel dinka, ko shafinka da ke Dandalin Facebook, akwai masarrafa ta musamman da ke haddace hanyoyin da kake shiga shafin ko akwatin dasu.  Duk sadda aka samu sauyi, to za a tuhumi wannan sauyi ta hanyar neman tantancewa.  Idan shafinka ne, sai ka bayar da bayanan da aka tambayeka, muddin ka kasa kuma, to ba za a taba bari ka shiga shafin ba.  Don haka, zaman lafiyarka daya ne; ka fadi amsar tambayar da aka maka.  Da fatan ka gamsu.
Baban Sadik barka da bincike. Ni dai idan na yi kira a waya ko aka kira  ni, bayan na gama sai inji hajijiya tana dauka ta, wani lokacin kuma sai inji kunne na ya toshe yana kara kamar kukan gyare.  Don Allah Baban Sadik ka yi mini bincike; me ke kawo min hakan?  Daga Ali Fancy, Garko, Kano: 08027921665
Malam Aliyu wannan al’amari ne da ke da alaka ta kai tsaye da kwarewa a fannin likitanci, wanda kamar yadda na sha bayyanawa, ni ba likita ba ne.  Duk wani illa da na’urorin kimiyyar sadarwar da kere-kere ke haddasawa, ko da an ga na fadi wani daga cikinsu, na hakaito ne daga kwararru, amma ban da kwarewa ta musamman wajen tabbatar da daidai ko kuskuren ire-iren wadannan abubuwa.  Don haka ina bayar da shawara da ka mika wannan kuka naka ga Dakta Auwal Bala a shafin “Kiwon Lafiya.”  Da fatan za a gafarce ni sanadiyyar rashin samun gamsuwa kan wannan mas’ala. Allah baka lafiya, ya kuma sa a dace wajen gano matsalar da ke haddasa wannan lalura gareka, amin.  Na gode.
Assalaamu Alaikum, Baban Sadik ga jinjina ta gareka, Allah ya kara maka kwazo, amin.  Na gode: 08162424124
Wa alaikumus salam, ina godiya matuka gare ka/ki da wannan addu’a da jinjina.  Allah saka maka/miki da alheri, amin summa amin.  Na gode.
Baban Sadik, ina fatar Allah ya kara maka lafiya, tare da mu, amin summa amin. Daga Nasiru Sani Gusau: 07064340375
Na gode matuka Malam Nasiru, kaima Allah saka maka da alheri mai dimbin yawa. Allah kara mana fahimta da juriya wajen daukar ilimi da aiki da shi, amin.
Assalaamu alaikum, me ya sa idan sakon tes bai tafi ba, amma kuma sai a cire wa mutum kudi?  Musa Bamalli, Zariya: 08035951530
Wa alaikumus salam, da fatan ana lafiya.  Hakan ya danganci tsarin kamfanin waya ne. Galibinsu sun saita na’urarsu ne ta rika debe kudin hidimar aika maka sakonka da zarar ka masa maballin aika sakon da ke wayarka.  Idan aka samu tangardar girgidin yanayin sadarwa (Network Fluctuation), sakon bai je ba, shi ke nan, kudinka sun sha ruwa. A ka’ida ba haka ya kamata abin ya zama ba.  To amma tunda hakar na’urar take, ba yadda suka iya.  Kamfanin waya daya ne na sani a kasar nan wanda ke iya dawo maka da kudinka nan take idan tes bai je ba, ko da bayan kwana daya ne.  Wannan kamfani shi ne na bisafone, wanda kuma bai yadu ba sosai a kasar nan.  Don haka sai dai hakuri.  Wannan wata masala ce wacce idan mutum na da lokacin da zai iya batawa, yana iya gyatta ta, ta hanyar zuwa da sanar da su halin da kake ciki.  To amma nawa za ka kashe zuwa ofishinsu? Nawa za ka kashe wajen dawowa?  Idan suka ki, kace dole sai an biya ka, sai dai kotu.  Nawa za ka kashe wajen tsayar da mai kwato maka hakkinka, wato Lauya?  Don haka sai dai hakuri.  Allah sa mu dace, amin.