✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu (6)

A yau dai in Allah yaso mun zo karshen sakonnin masu karatu. A mako mai zuwa za mu shiga wani maudu’in kuma. Shafin Kimiyya da…

 Hoton Manhajar kwamfutaA yau dai in Allah yaso mun zo karshen sakonnin masu karatu. A mako mai zuwa za mu shiga wani maudu’in kuma. Shafin Kimiyya da kere-kere na farin cikin taya dukkan daukacin masu karatu bikin babbar sallah da ke tafe ranar Talata in Allah yaso. Allah Ya karbi ayyukanmu, ya gafarta mana zunubanmu, ya kuma albarkaci lokutanmu baki daya, amin.

Assalaamu alaikum, barka da warhaka. Allah ya taimaka ya kuma kara fahimta.  Don Allah ina so ka turo mini rubutun da ka yi mai take: “Tsakanin kwakwalwa da Zuciya wa ke Samar da Tunani,” ta adireshin Imel dina da ke kasa.  Sannan kuma ina neman izninka akan zan dora wannan kasida a shafina da ke Intanet, domin sake yada ta.  – Ahmad Abdulnasir Shu’aib, dorayi, Kano: 08182788350 – [email protected]
Wa alakumus salaam Malam Ahmad. Da farko dai na tura maka wannan kasida da ka bukata ta adireshinka na Imel da ka turo. Bayan haka na amince har abada, cewa ka sanya wannan kasida a shafinka da ke Intanet. Illa dai kamar yadda ka’idar nakalto bayanai na ilmi ta nuna, ka bayar da hakkin mallaka. Ma’ana ka tabbatar da sunan wanda ya rubuta. Allah sa a dace, amin.
Assalamu Alaikum Baban Sadik, barka da warhaka.  Me ake nufi da “Serber” da kuma “Client”?  Shin, akwai bambanci a tsakanin wadannan kalmomi ne ko dai duk abu daya ne ake nufi?  Domin a wani lokaci sai inji an ambacesu a lokaci daya.  Ka huta lafiya.  –  Uncle Bash, Jimeta-Yola: 0703713338
Wa alaikumus salaam Uncle Bash.  Wadannan kalmomi dai suna da alaka mai girman gaske a tsakaninsu, duk da cewa sun sha bamban wajen ma’ana.  Da farko dai, Kalmar “Serber” a ilimin sadarwa ta kwamfuta na nufin wata masarrafa ce ko na’urar kwamfuta ko sadarwa mai dauke da tsarin mika bayanai tsakaninta da wata na’ura ‘yar uwarta.  A daya bangaren kuma, Kalmar “Client” na ishara ne ga wata masarrafar kwamfuta ko na’urar sadarwa mai iya nemowa ko karbo bayanai daga wata masarrafar kwamfuta ko na’urar sadarwa mai dauke da masarrafar mika bayanai mai suna “Serber” da ma’anarta ta gabata.  Kalmar farko ita ce muke kira da suna “Uwar-garke” a Hausar zamani na bangaren sadarwa.  Mun kira ta “Uwar-garke” ne saboda yanayin aikinta. Kamar yadda ka san saniya uwar-garke ke baiwa ‘ya’yanta mama, a duk sadda suka bukata.  Haka wannan masarrafa ta “Serber” ke bai wa duk kwamfuta ko masarrafar da ta bukaci wani bayani daga gare ta.  Asali, “Uwar-garke” kwamfuta ce da ke dauke da shafukan Intanet (Web Pages) ko bayanai a gajere ko dogon zangon sadarwa, wadda ke iya fahimtar sakon bukatar bayanai (Rekuests) daga wata masarrafa ko kwamfuta ‘yar uwarta.  Ita wannan kwamfuta ba ta bukata sai dai kawai a bukata daga gare ta.  
Duk sadda sakon bukata ya iso gare ta, takan yi amfani da wasu ka’idojin sadarwa (Communication Protocols) wajen tantance ingancin sakon, da kuma tambayar wadda ta turo sakon harshe irin na sadarwa.  Da zarar ta gamsu da jawaban da ta samu, nan take sai ta bayar da bayanan da aka bukata daga gare ta.  Ita kuma mai nema, ita ce “Client.” Tana iya zama kwamfuta ce ko wayar salula, ko na’urar sarrafa bayanai (irin iPaid, ko Samsung Galady Note, ko Galady Tab, ko Google Nedus).  Har wa yau, ana iya samun kwamfutoci masu bukatar bayanai (Clients) sama da goma su diro kan Uwar-garke guda a lokaci daya, kuma duk tana iya amsa musu nan take.  Dukkan wannan al’amari kan faru ne cikin kankanin lokacin da bai wuce dakiku (seconds) 10 ko 20 ba, iya gwargwadon ingancin yanayin sadarwar da ke tsakanin mai nema da wanda ake nema daga gare ta.   Wannan yanayi ko tsari shi ake kira “Client-Serber Model” a ilimin kimiyyar sadarwar zamani.
Assalaamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka, ina fatan kana lafiya tare da daukacin masu karatu.  Tambayata ita ce: shin, me ya sa idan mutane suka ga mutum da babbar wayar, sai ka ji suna tambayar cewa, “Shin Android ce?” Abin da nake son sani a nan shi ne: Mene ne Android?  Kuma wani abu ne yasa wannan wayar da ke dauke da Android ta fi tasiri a tsakanin wayoyin salula na zamanin yau da yasa har mutane ke rubibin sayenta?  Sannan kuma ko akwai kwamfutar Android?  In akwai, shin, mene ne ya bambanta wayoyin Android da kwamfutar?  –  Uncle Bash, Jimeta-Yola: 0703713338
Wa alaikumus salam Uncle Bash, da fatan kana lafiya kai ma. Da farko dai kamar yadda ka tambaya, kalmar “Android” na ishara ne zuwa ga babbar manhajar wayar salula da galibin wayoyin salular kamfanin Samsung, da LG, da Motorola, da SonyEricsson, da kuma HTC.
 A baya-bayan nan kamfanin wayoyin salula na kasar Sin mai suna TECNO ya shigo cikin harkar shi ma, inda ya fito da wayoyin salula masu kima, masu zafi, masu inganci, dauke da wannan babbar manhaja ta Android.  Babbar manhajar Android na kamfanin Google Incorporated ne da ke kasar Amurka, ta hadin gwiwa da wasu kamfanonin waya da harkar sadarwa kusan 10.  Tana daga cikin shahararrun manyan manhajojin wayar salula da ake ji da su a duniya a yau.  Sadda kamfanin Nokia ya saye kamfanin Symbian da ke bai wa sauran kamfanonin waya irin su Samsung da LG da Motorola lasisi, sai suka koma kan wannan babbar manhaja ta Android. Ga dukkan alamu, wannan na daga cikin abin da ya daga su, har a karshe suka shallake kamfanin Nokia a kasuwar wayar duniya baki daya. Nau’in wannan babbar manhajar waya dai ita ce Android Jelly Bean 4.3.
Daga cikin dalilan da suka haddasa mata shahara da karbuwa a tsakanin jama’a a duniya akwai saukin mu’amala, da hanyoyin samar da masarrafar wayar salula masu saukake mu’amala da bayanai ko ita kanta wayar, a saukake kuma na kyauta.  Bayan haka, wannan babbar manhaja ta Android tana da ingantacciyar hanyar sadarwa ta Intanet ba tare da matsala ba, da hanyoyin ta’ammali da bayanai daga waje ko cikin wayar masu inganci; ta hanyar masarrafar na’urorin daukar hoto, da na’urar daukar bidiyo, da fasahar Bluetooth da dai sauransu.  Sannan akwai kwamfuta mai dauke da wannan babbar manhaja ta Android. Kamfanin kera kwamfutoci da wayar salula mai suna Dell ne ya fara kera kwamfutocin tafi-da-gidanka (Laptops) masu wannan babbar manhaja.  Cikin makonni uku da suka gabata ya fitar da wasu nau’ukan kwamfutocin tafi-da-gidanka jerin nau’in Dell dPS, guda uku: wato Dell dPS 11, da 12, da kuma 13.
Wadannan siffofi ne suka bambanta babbar manhajar wayar salula ta Android (wanda kamfanonin Samsung, da LG, da Motorola, da HTC, da SonyEricsson ke kerawa) da wayoyin salula masu dauke da babbar manhajar Windows Mobile (wadanda kamfanin Nokia, misali, yake kerawa).  Babbar manhajar Windows Mobile wacce ke dauke cikin nau’ukan wayar Nokia Lumia da dukkan rabe-rabenta, ta sha bamban.  
Na farko dai ta fi wahalar sarrafawa ga mai dan karamin sani, wanda bai saba mu’amala da kayayyakin sadarwa na zamani ba, sannan ba ka iya sarrafa bayanan da ka taskance cikin karamar ma’adanar MMC dinka, sabanin Android.  Abin da kamfanin Microsoft ya fi damuwa da shi a wannan babbar manhaja shi ne tsaron bayanai, da tsaron ita kanta babbar manhajar, wato: “User and Applications Data Security.”  A daya bangaren kuma, ban taba amfani da kwamfuta mai dauke da babbar manhajar Android ba, domin ba su yadu sosai ba. Kamfani daya ne na sani yake kera su, kuma ba su yadu ba.  Amma dole za a samu bambanci wajen masarrafai, da yawan abubuwa masu taimaka wa kwamfuta aiwatar da ayyukanta, wadanda wayar salula ba ta da irinsu. Amma idan ka kebe wannan, duk dabi’ar sauri, da saukin mu’amala duk daya ne.  Da fatan ka gamsu.
Salaamun Alaikum Baban Sadik, ina da waya kirar Nokia 300, kullum sai ta rika nuna jone take da Intanet, kuma hakan kan cinye mini kudi ko da kuwa banyi komai ba, kuma na rasa yadda zan yi.  To ina mafita?  Na biyu kuma, wai shin, meye bambancin waya kirar Japan da kirar Sin (China)?  Domin na ga dalibai da yaran masu kudi ba su sayen waya kirar Sin (China) sai kirar Japan; duk da kirar Japan tana dauke ne da SIM daya, ita kuma kirar Sin (China) na zuwa ne da SIM biyu ko uku a ciki.  –  Abdulwahhab Haladu, Zarma Hinna: 07060417970
Wa alaikumus salam, Malam Abdulwahhab wannan ba wata doguwar matsala ba ce.  Ka je “Settings”, ka shiga “Phone Settings”, sai ka gangara “Connection”, ka shiga “Packet Data” ka matsa, za ka ga inda ake saita wayar, sai ka canza daga “When Abailable” ko “Always” zuwa “When Needed.”  Duk da cewa Nokia 300 na dauke da babbar manhajar Asha ne, amma ba za a samu wani bambanci mai nisa a tsakanin abin da na kwatanta maka ba, don wayar Nokia ce, kuma wannan shi ne galibin tsarinsu wajen saita tsarin jona wayar salula da Intanet.  
Dangane da tambayarka ta biyu kuma, ya danganci wadanda ka gani da wayar, da irin zabinsu. Amma kamar yadda akwai wayoyi masu inganci daga kasar Japan, haka akwai wayoyi masu inganci daga kasar Sin.  Me yasa wasu ke son na Japan amma ba son na kasar Sin?  Wannan kuma ya danganci zabi.  A baya galibin wayoyin da ke zuwa daga kasar Sin kanana ne, masu matsalar batir, kuma ba a cika samun kayayyakin gyararu ba idan suka lalace. Amma yanzu wannan yanayi ya canza musamman da bayyanar kamfanin TECNO, wanda ke kera wayoyi masu inganci kuma masu dauke da babbar manhajar Android, kamar yadda bayani ya gabata a sama.  Da fatan ka gamsu.
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, hakika ni bako ne wajen aiko da sako a wannan fili, amma kuma na dade ina amfanuwa da bayananka a wannan fili.  Don Allah wasu wayoyi ne masu ingantaccen batiri?  Wadanda za a iya amfani da fasahar Intanet na lokaci mai tsawo a kullum, amma batirin bai kare ba; ta yi kamar kwanaki biyu ko uku ana bugawa.  Allah Ya saka maka da alheri, amin.  –  Idris Muhammad, Funtua, Katsina: 08094286416
Wa alaikumus salam, Malam Idris samun wayar salula irin wannan siffar a wannan zamani zai yi wahala.  Na farko dai yana da kyau ka san cewa shi tsarin Intanet a wayar salula yana amfani ne da masarrafai da dama a lokaci daya, wadanda ke tilasta wa wayar aiwatar da ayyuka masu yawa cikin lokacin da ake mu’amala da shafukan Intanet din. Misali, idan ka budo shafin Intanet a wayarka, akwai masarrafar lilo (Phone Browser), wadda ita ce za ta yi ta hakilon nemo maka bayanan, da kokarin bayyanasu a shafin wayar, da budo maka duk shafin da ka bukata a kowane lokaci.  Wannan ba karamin aiki ba ne.  Shi yasa a duk sa’adda kake mu’amala da fasahar Intanet a wayar salula, za ka ji wayar tana daukar zafi daga baya ko gefenta, daidai inda batiri ko kundun wayar (Processor) yake.  Bayan haka, wannan masarrafa da ke budo maka shafin Intanet, tana amfani ne da yanayin sadarwa (Network), wanda shi kanshi karin aiki ne ga wayar.  Domin a duk sadda waya ke amfani da yanayin sadarwa (wajen kira ko amsa kira, ko neman balas, ko aika sakonnin tes da karbarsu, ko mu’amala da fasahar Intanet), to, yanayin kuzarinta na karuwa, wanda hakan wani karin lodi ne a kan batir, domin shi ne makamashin da wayar ke amfani da shi.  
Don haka, abin da ya fi komai cin batir a wayar salula shi ne mu’amala da fasahar Intanet na tsawon lokaci, domin wayar na amfani da masarrafa ne, tare da yanayin sadarwa a lokaci guda.  Sai kuma kira, da amsa kira, da aika sakonnin tes, da kallon hoton bidiyo.  kari a kan haka, ya danganci tsarin gini ko kirar wayar. Idan mai shafaffen fuska ce (Touchscreen), mara maballin shigar da bayanai (Keypad), nan ma wani karin aiki ne. A takaice dai, iya gwargwadon yawan kyale-kyale da cikar waya wajen gini da kintsi da kira, iya gwargwadon yadda za ta ci makamashin batir. Don haka, sai ka duba; me kake tunanin za ka fi yi da wayar salula idan ka saya?  Wannan shi zai baka damar samun wacce take da inganci wajen aiwatar da irin wannan aikin.  Daga nan sai ka san yadda za ka tsara wa kanka hanyar tafiyar da ita, musamman wajen manejin batirinta.  Da fatan ka gamsu.