Search
Subscribe
Amsoshin sakonnin masu karatu ta imel da tes (1)

Amsoshin sakonnin masu karatu ta imel da tes (1)

A makon jiya ne (11 Maris, 2020) wadansu barayi suka balle makullin motata a nan Abuja, inda suka dauke jakar da ke dauke da kwamfutata da ma’adanan bayanai manya (edternal hard dribes) da sauran kayayyaki da takardu masu amfani da ba zan iya tantance su ba har yanzu. Wannan ya sa na rasa galibin abubuwan da nake dogaro da su wajen gudanar da bincike kan makalolin da nake rubutawa a wannan shafi. Don haka zan dakatar da rubutu kan ‘Ci Gaban Kimiyya da Kere-kere ga Al’adu da Dabi’ar dan Adam,’ wanda na faro cikin watan da ya gabata, sai nan gaba idan na gama kintsawa.  A yau, insha Allahu zan leka taskar sakonninku ne, don amsa wasu daga cikin tambayoyi ko tsokacin da kuka yi.  A gafarce ni kan wannan tsaiko da aka samu.  Ina godiya matuka da goyon bayan da nake samu daga gare ku baki daya:

———

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka dai.  Don Allah ina son a bambance mini tsakanin wadannan kalmomi: “Factory Reset” da kuma “Flashing” a fannin kimiyya da fasahar wayar salula.  Da fatar zan samu gamsassun amsoshi daga gare ka.  Na gode.  Aliyu Nasiru, Kano: alinasir30@gmail.com

Wa alaikumus salam. Barka dai Malam Aliyu. Lallai akwai bambanci tsakaninsu, kamar yadda a zahirin haruffansu ma da bambanci. Da farko dai, zai dace Malam Aliyu ya san cewa bayan kera wayar salula, wadanda suka kera ta su sun san cewa a wani lokaci na rayuwarsu, muddin ana amfani da ita, to, akwai nau’o’in matsaloli ko kalubale da za su rika cin karo da su.  Ire-iren wadannan matsaloli na iya zuwa ta hanyar mai amfani da su, ko ta hanyar wata wayar da suke aiwatar da sadarwa da su, ko ta kuma a ita karan-kanta wayar; haka kawai tana iya haduwa da matsala, koda babu wanda ya taba ta, muddin ana amfani da ita.  Don haka, sai suka samar da hanyoyin warware wadannan matsaloli. Wadannan hanyoyi dai mataki-mataki ne, kamar yadda su ma matsalolin hawa-hawa ne.

Kafin bayanin dalilan da kan sa wayar salula ta shiga halin da za ta bukaci wadancan hanyoyin waraka, wadanda ka zayyana biyu kadai daga cikinsu, yana da kyau mu san cewa, a duk sa’ar da ka kunna waya, ka yi amfani da ita na dan wani lokaci ko kwanaki tana kunne, akwai inda take tattara wasu bayanai na musamman wadanda idan ta tashi bukatar aiwatar da wani aiki irin wanda ta yi a baya, ba sai ta maimaita matakan da ta bi ba, kawai za ta koma kan wadancan bayanai ne don aiwatar da aikin. Wadannan bayanai su ake kira: “Cache.” Kuma wayar salula kan taskance bayanai kan dukkan ayyukan da take aiwatarwa-daga kiran waya, zuwa hawa Intanet da sauraron sauti ko kallon bidiyo. Dukkan wadannan ayyuka idan kana yin su ta hanyar wayar salula, tana aiwatar da umarnin da kake ba ta wajen yin su ta hanyar komawa kan bayanan da ta taskance a baya kan aiki, ba sai ta maimaita su a aikace daga farko zuwa karshe ba.

To amma kasancewar wayar salula na’ura ce, akwai sa’ar da wadannan bayanai da take taskancewa masu suna: “Cache” kan gurbace.  Shi ya sa a wasu lokuta idan ka bukaci aiwatar da wasu abubuwan da ka saba yin su da wayarka, sai ka samu cikas. Musamman wadanda suke da alaka da wayar kai-tsaye, ba na kira ko amsa kira ba. Wannan ya sa aka tanadi wadannan hanyoyi don magance ire-iren wadannan matsaloli.

Matsaloli

Wadannan matsaloli dai sun shafi ruhin wayar salula ne, wato babbar manhajarta ko kuma masarrafar da mai waya ke loda mata don amfanin kansa; wato: “Hardware Related Issues” ke nan, kamar yadda yake a fannin kimiyyar sadarwa. Ire-iren wadannan matsaloli dai sun hada da matsalar yanayin sadarwa (Network) da matsalar sauti da matsalar bidiyo da matsalar tes da matsalar sarrafa bayanai da matsalar aiwatar da kira ko amsa kira da matsalar aika sakonnin Imel, ko hawa Intanet da dai sauransu. Alamun da ke tabbatar da samuwar wadannan matsaloli a lokuta daban-daban dai su ne, kasa kira ko amsa kira da yawan cijewar waya idan ana amfani da ita da yawan sumewa (hanging) lokaci zuwa lokaci da sauran alamu makamantansu. A wasu lokuta kuma wadansu kan so sanya wa wayar salula wasu siffofi da hanyoyin gudanar da abubuwa irin wadanda asalin kamfanin bai yarda a dora wa wayar ba. Haka kuma, a wasu lokuta mutum na iya mance kalmar sirrin wayarsa, ya kasa sarrafa ta. Wannan kan sa dole a bi ta bayan fage don shawo kanta.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin