✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da i-mel

Assalaamu alaikum, Allah saka da alheri.  Shawarata game da dukkan kasidun da aka gabatar a baya tsawon shekaru goma shi ne, a tara su a…

Assalaamu alaikum, Allah saka da alheri.  Shawarata game da dukkan kasidun da aka gabatar a baya tsawon shekaru goma shi ne, a tara su a mayar da su littafi a siyar. Kuma a dora a Intanet.  –  Babangida Kano: 08064821597

Wa alaikumus salaam, Malam Babangida barka ka dai. Wannan shawara taka abin dubawa ce.  Akwai wadanda suka bayar da shawara makamanciyar wannan a shekaru ko lokutan baya. Kamar yadda ka sani, rubuta littafi ba shi ne matsalar ba. Tallata shi, da kuma yada shi yadda kowa zai samu, ta hanya mafi inganci da sauki, shi ne babban aikin. Wannan ba karamin lamari ba ne ga wanda bai taba shiga harkar ta’alifi ba iri na. Zan cigaba dai da tara wadannan kasidu, zuwa wani lokaci mu ga abin da Allah Zai yi. Amma a halin yanzu na gina shafin Intanet dai na zuba su, kamar yadda na sanar shekaru uku da suka gabata.  Za a iya samun su a adireshin shafin Taskar Baban Sadik dake: https://www.babansadik.com.  Na gode matuka da wannan shawara.

Assalaamu alaikum, Don Allah Baban Sadik a mini bayani; a Intanet idan nazo saukar da wani bayani, sai in ga manhajojin sun sha bamban, kamar haka, wani: “jar,” wani “jad,” wani “ede,” wani kuma “pdf.”  Mene ne ma’anarsu?  –  Mu’azzam Suleiman, Kano: 08179705299

Wa alaikumus salaam, Malam Mu’azzam ai wadannan ramzozi ko sunaye da kake gani, sunaye ne da ke ishara zuwa ga nau’ukan jakunkunan bayanai (File Types) da kwamfuta ko wayar salula ke iya mu’amala dasu wajen budewa ko karbar su, idan manhajoji ne ko masarrafai. Idan ka ga “.jar” da “.jad”, to wadannan nau’ukan jakunkunan bayanai ne masu dauke da dafaffiyar manhajar wayar salula (Mobile Phone Application), wanda idan ka saukar, za ka iya loda wa wayar salularka, iya gwargwadon yadda za ta iya dauka, idan yanayinta ya dace da tsarin manhajar.  Manhaja mai wannan ramzi an gina ta ne da dabarun gina manhajar kwamfuta (Programming Language) na Jaba.  Idan kuma ka ga jakar bayanai ta kare da “.ede”, to wannan kuma dafaffiyar manhajar kwamfuta ce, wato: “System Application.” Ita wannan manhaja da sunanta ke karewa da wannan ramzi, a kwamfuta kadai ake iya loda ta, don amfanuwa da abin da ta kunsa.  Ramzin “.ede” na nufin “Edecutable” kenan.  Idan kuma ka ga “.pdf” nau’in jakar bayanai ne mai dauke da tsagwaron bayanai da aka taskance da manhajar “Portable Document Format,” cikakken ma’anar ramzin “.pdf” kenan.  Kamfanin “Adobe” ne ke da wannan manhaja. Da fatan ka gamsu.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, me yasa idan na tura sakon waya sai in ga “Delibered Report”, da wani suna daban ba sunan wanda na tura masa sakon ba?  Kuma shin, wannan ke nuna wanda ya sakon yaje wajensa ya karanta kenan?  Domin wanda na tura masa sakon ya kance bai gani ba.  Shin yaya abin yake ne?  –  Usman Muazu Funtua: 08106067660

Wa alaikumus salaam, Malam Usman wannan lamari naka da ban mamaki yake. Abin da zan iya cewa shi ne: ta la’akari da ka’idojin sadarwa daga kan kwamfuta har zuwa wayar salula, ta yiwu wanda ka ga sakon ya je wajensa ne ka tura masa. Watakila ka yi kuskure wajen zaben sunan wanda za ka tura masa sadda kake kokarin zakulo sunansa da lambarsa.  A ka’ida, duk wanda ka tura masa sako, idan kamfanin waya ya isar da sakon lafiya kalau, dole ya zama da sunansa ko lambarsa za a sanar da kai, ba ka tura wa wani sako amma kuma a sanar da kai cewa wani aka tura wa ba. In har wanda ka tura masa yace bai ga sakon da ka tura masa ba, to alama ce da ke nuna cewa lallai lambar wani ka zaba ba nashi ba. Sai ka rika lura, ko ka sake dubawa.  Allah sa a dace, amin.

Salaamun alaikum Baban Sadik, don Allah ina son karin bayani a kan wayar HTC Windows 7.  Na ga ka ambaci manyan wayoyi amma baka ambace ta ba.  Ko karamar waya ce?  –  Mai Kawo: 08050321406

Wa alaikumus salaam, barka ka dai. Ai “HTC” sunan kamfanin waya ne, wanda ke kera wayoyi nau’uka daban-daban, masu dauke da babbar manhaja kala-kala. Daga cikin manyan manhajojin da wayoyin HTC ke dauke dasu akwai “Windows 7 Mobile”, wanda kake magana.  Su kansu wadannan din ba guda daya bane, ban san wanda kake nufi ba. A takaice dai, duk wayar salula mai dauke da babbar manhajar “Windows Mobile” ba karamar waya bace. A lokacin da nake ambaton nau’ukan manyan wayoyi na kawo misalai ne da guda biyu, ba wai iyakansu ba kenan. Da fatan ka fahimta.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, wai me ke sa idan na shiga shafin Facebook wani lokaci ina son inyi tsokaci (Comment), amma ban ganin filin yin hakan?  –  Aliyu Ibrahim Zawiyya, Gusau: 08067784588

Wa alaikumus salaam, wannan alama ce dake nuna cewa babu abota a tsakaninku da mai jawabin da kake son yin tsokaci akai. Domin sai wanda yake abokinka ne kadai za ka iya yin tsokaci kan abin da ya rubuta a Dandalin Facebook.  Idan kana bukatar karantawa tare da yin tsokaci kan jawaban jama’a a Facebook, sai ka nemi abota tsakaninka da su. Allah sa a dace.