✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da i-mel

Salaamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya.  Don Allah wane tsawon lokaci ne batirin wayar salula zai iya dauka yana ajiye bai…

Salaamun alaikum Baban Sadik, da fatan kana cikin koshin lafiya.  Don Allah wane tsawon lokaci ne batirin wayar salula zai iya dauka yana ajiye bai lalace ba?  Sannan kana iya ajiye shi a cikin na’urar caji na tsawon lokaci don ya cika sosai?  –  Husseini M. Binanchi da Isa Kwafsi Ba Ka Soyayya, Unguwar Magajin garin Sakkwato: 08087436699

 

Wa alaikumus salaam, da fatan kuna cikin koshin lafiya. A gaskiya babu wani lokaci na musamman da aka kayyade cewa idan batirin wayar salula ya kai a ajiye ba a amfani da shi zai lalace. Abin da na sani dai shi ne, idan aka yi cajin batiri ya cika, ba a yi amfani da shi ba, to a hankali zai sance, saboda sinadaran da ke cikinsa za su yi rauni, har su zagwanye. Bayan haka, abin da aka fi so shi ne, da zarar batir ya cika a caji, a yi maza a cire shi, domin idan har aka dauke wuta yana like da cajin, muddin a kashe wayar salular take, to cajin na iya zukewa. Sai a kiyaye. Da fatan kun gamsu.

 

Salaamun alaikumu, ina fatan kana cikin koshin lafiya tare da iyali.  Ina daya daga cikin masu yabawa da kuma farin ciki da shafinka na kimiyya da kere-kere (shafi na 32) a jaridar AMINIYA.  Ina amfana matuka da dumbin iliminka da baiwarka, a matsayina na dalibin harshen Hausa kuma mai sha’awar ilimin fasahar sadarwa ta zamani.  Tabbas!  Shafin ya dade da zama makarantar kimiyya da kere-keren AMINIYA ga Amintattun Daliban Hausa da Masu sha’awar Hausa da kimiyya da kere-kere.  Allah ya kara sani da daukaka, amin.  –  Aminu M. B. Umar, birnin Zariya: 08081224683

 

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Aminu. Na gode matuka da wannan sako naka. Kuma ina farin ciki matuka da ya zama abin da nake yi yana yin tasiri ta hanyoyi da wuraren da ban taba tunani ba. Bayan wannan tabbaci naka, a baya na samu sakonni da dama makamantan wannan. Akwai daliban harshen Hausa dake wasu daga cikin manyan Jami’o’in arewacin Najeriya da suka bukaci kusan dukkan kasidun da na rubuta a baya kan wasu fannoni, don amfani dasu cikin rubuce-rubucensu na karasa karatu. Allah Ya sa mu dace baki daya, ya kuma amfanar damu abin da muke karantawa a dukkan fannonin ilimi, amin. Na gode matuka.

Assalaamu alaikum, da fatan alheri, da kuma fatan samun babban rabo duniya da lahira.  Don Allah ina son sanin yadda ake neman bayanai ta Intanet; idan naje Google ko Wikipedia misali, zan shigar da Kalmar da nake neman bayani ne ko kuwa akwai wani tsari ne da ake bi?  – Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Tunshama Kuarters, Kano: 0809558832

 

Wa alaikumus salaam, barka ka dai Malam Yahuza. Lallai neman bayanai a Intanet yana da tsari na musamman.  Abu na farko kuwa shi ne ka san me ka ke nema? Me ka ke so?  Wasu irin bayanai ka ke nema? Wasu kalmomi za ka yi amfani dasu don samun fa’ida kan haka?  Sannan a ina za ka samu manhajar da za ta saukake maka neman wadannan bayanai?  Dukkan wadannan tambayoyi suna bukatar amsa gamsasshiya, domin da zarar ka kuskure su, tun nan za ka rasa abin da ka ke so. Da farko dai, bayan ka haddade nau’in bayanan da ka ke nema, sai ka doshi gidan yanar sadarwa na musamman da aka tanada don neman bayanai. Wannan gidan yanar sadarwa yana dauke ne da manhajar neman bayanai cikin sauki, wadda ke iya fahimtar irin abin da ka ke nema ta hanyar kalmomi ko lambobi ko alamun da kayi amfani da su ko ka shigar. Shahararre daga cikin ire-iren wadannan gidajen yanar sadarwar neman bayanai kuwa kamar yadda ka sani, shi ne gidan yanar sadarwar Matambayi Ba Ya Bata na kamfanin google, wato: Google Search Engine. Idan ka shiga sai ka sa kalma, ko kalmomi, ko jumlar da ke dauke da irin bayanan da kake so. A kiyaye, kada kayi amfani da doguwar jumla, domin ba za ka samu fa’ida ba. Haka idan shafin Babban Kamus din Intanet ka shiga, wato Wikipedia, za ka ga inda aka tanadi hanyar shigar da kalma ko kalmomi don tambayar irin bayanan da ka ke so. Sai ka shigar a wurin, ka matsa maballin “Enter” da ke jikin allon shigar da bayanan kwamfutarka, nan take za ka samu amsa. Allah sa a dace.

 

Assalaamu alaikum, barka da warhaka.  Allah ya taimaka.  Don Allah ina so a taimaka a turo mini bayani kan “Samuwar Bacci da Mafarki a Mahangar Kimiyya.”  Ga adireshin Imel di na: [email protected] <mailto:[email protected]>  –  08037156498

Wa alaikumus salaam, barka da warhaka. Sai ka/ki duba jakar Imel dinka/ki, na tura tuni. Allah sa a dace, ya kuma amfanar damu abin da ke mu ke karantawa. Na gode.

 

Assalaamu Alaikum Baban Sadik, Allah ya albarkaci zuriya da karin basira.  Rokona shi ne: da fatan za ka tattara dukkan kasidun da ka gabatar a kundin littafi na musamman don amfanin masu karatu.  – Jamilu Aliyu, Lafiya, Nassarawa: 08036927722

Wa alaikumusam, Malam Jamilu na gode da addu’o’i, Allah saka da alheri. A halin yanzu dai akwai kundin dukkan kasidun a shafinmu da ke Intanet, wanda adireshinsa ke saman wannan shafi. Allah sa mu dace baki daya, amin.