Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da imel

Assalamu alaikum Baban Sadik, barka da warhaka.  Me ake nufi da “Serber” da kuma “Client”?  Shin, akwai bambanci a tsakanin wadannan kalmomi ne ko dai duk abu daya ne ake nufi?  Domin a wani lokaci sai inji an ambace su a lokaci daya.  Ka huta lafiya.  –  Uncle Bash, Jimeta-Yola: 0703713338

Wa alaikumus salam Uncle Bash.  Wadannan kalmomi dai suna da alaka mai girman gaske a tsakaninsu, duk da cewa sun sha bamban wajen ma’ana.  Da farko dai, kalmar “Serber” a ilimin sadarwa ta kwamfuta tana nufin wata masarrafa ce ko na’urar kwamfuta ko sadarwa mai dauke da tsarin mika bayanai tsakaninta da wata na’ura ’yar uwarta.  A daya bangaren kuma, kalmar “Client” tana ishara ce ga wata masarrafar kwamfuta ko na’urar sadarwa mai iya nemowa ko karbo bayanai daga wata masarrafar kwamfuta ko na’urar sadarwa mai dauke da masarrafar mika bayanai mai suna “Serber” da ma’anarta ta gabata.  Kalmar farko ita ce muke kira da suna “Uwar-garke” a Hausar zamani na bangaren sadarwa. Mun kira ta “Uwar-garke” ce saboda yanayin aikinta. Kamar yadda ka san saniya uwar-garke ke bai wa ’ya’yanta mama, a duk sa’ar da suka bukata.  Haka wannan masarrafa ta “Serber” ke bai wa duk kwamfuta ko masarrafar da ta bukaci wani bayani daga gare ta.  Asali, “Uwar-garke” kwamfuta ce da ke dauke da shafukan Intanet (Web Pages) ko bayanai a gajere ko dogon zangon sadarwa, wadda ke iya fahimtar sakon bukatar bayanai (Rekuests) daga wata masarrafa ko kwamfuta ’yar uwarta. Ita wannan kwamfuta ba ta bukata sai dai kawai a bukata daga gare ta.

Duk sa’ar da sakon bukata ya iso gare ta, takan yi amfani da wasu ka’idojin sadarwa (Communication Protocols) wajen tantance ingancin sakon da kuma tambayar wadda ta turo sakon harshe irin na sadarwa. Da zarar ta gamsu da jawaban da ta samu, nan take sai ta bayar da bayanan da aka bukata daga gare ta.  Ita kuma mai nema, ita ce “Client.” Tana iya zama kwamfuta ce ko wayar salula, ko na’urar sarrafa bayanai (irin su iPad ko Samsung Galady Note, ko Galady Tab, ko Google Nedus).  Har wa yau, ana iya samun kwamfutoci masu bukatar bayanai (Clients) sama da goma su diro kan Uwar-garke guda daya a lokaci daya, kuma duk tana iya amsa musu nan take.  Dukkan wannan al’amari kan faru ne cikin kankanen lokacin da bai wuce dakika (seconds) 10 ko 20 ba, iya gwargwadon ingancin yanayin sadarwar da ke tsakanin mai nema da wadda ake nema daga gare ta.   Wannan yanayi ko tsari shi ake kira “Client-Serber Model” a ilimin kimiyyar sadarwar zamani.

Assalaamu alaikum Baban Sadik, hakika ni bako ne wajen aiko da sako a wannan fili, amma kuma na dade ina amfanuwa da bayananka a wannan fili. Don Allah wasu wayoyi ne masu ingantaccen batiri?  Wadanda za a iya amfani da fasahar Intanet na lokaci mai tsawo a kullum amma batirin bai kare ba; ta yi kamar kwana biyu ko uku ana bugawa.  Allah Ya saka maka da alheri, amin.  –  Idris Muhammad, Funtuwa, Katsina: 08094286416

Wa alaikumus salam, Malam Idris samun wayar salula irin wannan a wannan zamani zai yi wahala. Na farko dai yana da kyau ka san cewa shi tsarin Intanet a wayar salula yana amfani ne da masarrafai da dama a lokaci daya, wadanda ke tilasta wa wayar aiwatar da ayyuka masu yawa cikin lokacin da ake mu’amala da shafukan Intanet din. Misali, idan ka budo shafin Intanet a wayarka, akwai masarrafar lilo (Phone Browser), wadda ita ce za ta yi ta hakilon nemo maka bayanan da kokarin bayyana su a shafin wayar da budo maka duk shafin da ka bukata a kowane lokaci. Wannan ba karamin aiki ba ne. Shi ya sa a duk sa’ar da kake mu’amala da Intanet a wayar salula, za ka ji wayar tana daukar zafi daga baya ko gefenta, daidai inda batiri ko kundun wayar (Processor) yake.  Bayan haka, wannan masarrafa da ke budo maka shafin Intanet, tana amfani ne da yanayin sadarwa (Network), wanda shi kansa karin aiki ne ga wayar. Domin a duk saa’r da waya ke amfani da yanayin sadarwa (wajen kira ko amsa kira, ko neman balas, ko aika sakonnin tes da karbarsu, ko mu’amala da fasahar Intanet), to, yanayin kuzarinta na karuwa, wanda hakan wani karin lodi ne a kan batir, domin shi ne makamashin da wayar ke amfani da shi.

ADVERTISEMENT

Don haka, abin da ya fi komai cin batir a wayar salula shi ne mu’amala da fasahar Intanet na tsawon lokaci, domin wayar na amfani da masarrafa ce, tare da yanayin sadarwa a lokaci guda. Sai kuma kira da amsa kira da aika sakonnin tes da kallon bidiyo.  Kari a kan haka, ya danganci tsarin gini ko kirar wayar. Idan mai shafaffiyar fuska ce (Touchscreen), mara maballin shigar da bayanai (Keypad), nan ma wani karin aiki ne. A takaice dai, iya gwargwadon yawan kyale-kyale da cikar waya wajen gini da kintsi da kira, iya gwargwadon yadda za ta ci makamashin batir. Don haka, sai ka duba; me kake tunanin za ka fi yi da wayar salula idan ka saya?  Wannan shi zai ba ka damar samun wacce take da inganci wajen aiwatar da irin wannan aiki. Daga nan sai ka san yadda za ka tsara wa kanka hanyar tafiyar da ita, musamman wajen manejin batirinta.  Da fata ka gamsu.