✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi

Matata takan yi wata uku zuwa hudu babu al’ada. Bayan wadannan watanni kawai lokaci guda sai ya zo, ba shiri. Ko matsala ce wannan? Daga…

Matata takan yi wata uku zuwa hudu babu al’ada. Bayan wadannan watanni kawai lokaci guda sai ya zo, ba shiri. Ko matsala ce wannan?

Daga Mijin Maidamuwa

Amsa: kwarai kuwa matsala ce wannan. An tsara jikin kowace mace in dai babba ce kuma in dai ba ta kai lokacin daina al’ada ba, to al’ada ta zo mata a kalla sau daya a duk wata (wata a nan ana nufin tsakanin mako uku zuwa biyar, amma kada ya wuce haka). Don haka duk matar da takan kai har wata uku ba ta ga komai ba, to ba ta da lafiya, abin da muke cewa amenorrhea, wanda abubuwa da dama ne ke kawo shi, kuma sai an je an binciki a ina ne matsalar take. Amma tun kafin nan, idan tana shan wasu magunguna kamar na gargajiya ko na asibiti za su iya sa mata matsalar, ta tsayar kafin ta ga likita, haka nan damuwa ko zullumi, kamar ta gida ko ta karatun makaranta misali, idan tana da damuwa ko zullumi idan ta rage su za a iya dacewa. Amma idan abu ya ci tura to fa sai ta ga likita dole.

Ni kuma maidakina idan ta zo al’ada sai ta yi ta fama da ciwon mara. Kuma na ji an ce irin wannan yana hana mace haihuwa?

Daga Abban Sadeek

Amsa: A’a babu wani kanshin gaskiya a wannan zance cewa ciwon mara lokacin al’ada kan iya hana daukar ciki. Idan mace mai samun ciwon mara duk al’ada ta kasa daukar ciki ba ruwan ciwon al’ada, wani abu ne daban wanda sai ta je asibiti an nemo dalili. Shi ciwon marar na wannan lokaci motsin e kawai da mahaifa kan yi yayin al’ada, kuma magungunan kashe zogi kawai ake sha sai ya lafa. 

Ni kuma ina da juna biyu wanda ya kai wata takwas, to sai dai ban yawan cin abinci. Ko hakan zai iya kawo min matsala?

Daga Fatima M., Kano

Amsa: Ba wata matala tunda kin ce kina ci amma ba sosai ba, ganin kin riga kin wuce watannin da cikin ke cikin hadari. Kusan idan mace ta shiga watan takwas ba a cika ji mata wani tsoro ba sosai. Sai dai kawai ki kara himma musamman wajen ’yan dabarun da muka sha bayyanawa a nan game da cimakar masu juna biyu

A dan kara yi mini bayani a kan alamomin da zan gane yaro ya kamu da ciwon numoniya.

Daga Hashimu, Jos

Amsa: To akwai tari da zazzabi da kasala da kuma sarkewar numfashi sama-sama, a ga kirji ko hakarkarin yaro na shigewa ciki. To idan an ga irin wadannan alamu tabbas alamu ne da za a iya alakantawa da ciwon hakarkari na numoniya. Abin da kuma ke nufin cewa sai an kai yaro asibiti dole kafin su tabbatar ko hakan ne.