✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi

Shin babu laifi mace ta sha magungunan karin jini alhalin ba a ce tana da karancin jini ba, kawai don ta kara lafiya? Daga Khadijatul…

Shin babu laifi mace ta sha magungunan karin jini alhalin ba a ce tana da karancin jini ba, kawai don ta kara lafiya?

Daga Khadijatul Kubra

Amsa: Duk da cewa mata suna yawan samun matsalar karancin jini ba a son yawan shaye-shayen magunguna a tsarinmu na kiwon lafiya. Duk wadda kika ga an ba kwayoyi ko allurai ko ruwan magunguna kamawa ta yi, wato ya zama dole ne (kamar a mace mai juna biyu wadda komai cin ta ba za ta iya cin abin da zai ishe ta ita da jaririn da ke cikinta ba). Ko a asibiti idan ana fadakarwa kafin a shiga ganin likita za ki ji ma’aikatan lafiya kamar a bangaren yara da wuraren awo suna cewa yara kanana da mata masu juna biyu wadanda suka fi kowa samun karancin jini, su rika yawan cin abinci mai kara jini, ba su rika shan kwayoyi masu kara jini ba. Saboda me ake cewa haka? Saboda sinadaran da akan samu a abinci masu kara jini irin su sinadarin karfe wato iron, sinadarai ne da Allah Ya halitta a cikin abinci musamman domin lafiyarmu. Wato sinadarai ne na ainihi, su kuma sinadaran karfe na cikin kwayoyin magani a dakin binciken kimiyya fa aka kera su, wato kwaikwayon na cikin abincin aka yi aka hada sinadaran. To idan za a tambaye ki ke a ganinki wane ne zai fi inganci? Abinci masu dauke da sinadaran karin jini kuma ba sai an tuna miki ba, za ki iya lissafo goma ma na sani.

 

Idan matar mutum tana da ciwon asma mijin zai iya kamuwa?

Daga Suraj A. Legas

Amsa: A’a, lallai Malam Suraj kai bako ne a wannan shafi, tunda mun sha zayyana irin cututtukan da za a iya kwasa daga wani a dalilin zaman tare, amma ciwon asma ba ya ciki. Yawanci cututtukan da akan iya kwasa daga wani zuwa wani kwayoyin cuta ne ke yada su. Kuma asma ba kwayoyin cuta ne ke kawo ta ba.

 

Matata ce ta haihu sai fatar gaban cikinta ta yi baki. Ko hakan matsala ce?

Daga Aliyu A.

Amsa: A’a, wannan ba matsala ba ce, wasu sinadarai ne da mahaifa kan samar suke sa mata masu juna biyu da ma wadanda suka riga suka haihu fatarsu yin baki. Ba a ciki kadai ba domin wadansu har a fuskarsu ma ana gani. Bayan watanni da haihuwa kuma bakin yakan baje da kansa. Don haka ba wani abin damuwa ba ne.