✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi

Wai shin da gaske ne yara ba sa samun karaya kamar ta manya saboda kashinsu bai yi kwari ba?   Daga Umar M.K Amsa: Eh,…

Wai shin da gaske ne yara ba sa samun karaya kamar ta manya saboda kashinsu bai yi kwari ba?

 

Daga Umar M.K

Amsa: Eh, to kusan haka ne tunda kashinsu ba irin na manya ba ne, bai yi kwari ya kuma bushe sosai ba. Sukan samu amma dai a iya cewa akwai bambancin karaya a yara da kuma manya. Maimakon karaya bas kamar yadda na babba kan iya samu, yawanci su yara sai dai a ga tsaga ba karaya bas ba. A yara kasa da shekara 15 karshen kasusuwa ba sa karyewa, tunda wannan wuri na karshen kashi a yara guntsi ne da shi bai riga ya zama kashi ba. Idan aka ce karshen kashi ana nufin kan gaba, wato wurin da wani kashi ya hadu da wani. Manya kuma suna karyewa a karshen kashi.

Idan aka zo ga maganar waraka, kasusuwan yara nan da nan cikin ’yan makonni suke warkewa idan suka karye saboda dama kashin girma yake. Amma a manya sai an yi lissafin watanni.

 

A wadanne kwanaki ne ko shekaru ya kamata a yi wa yara shayi a kimiyyance?

Daga Maimuna Aminu

Amsa: Eh, to saboda a irin wannan yanayi da ke karatowa na sanyi ne akan sha yara, za a iya cewa ba wani tsayayyen lokaci tun daga haihuwar yaro har shekara bakwai koma takwas. Yawanci mu a likitance saboda bambancin al’ada da addini da ra’ayi ba ma fada wa iyaye ga lokacin da ya dace sai dai idan su suka tambaya akan ce musu a kowane lokaci suka shirya za a iya yi daga makon haihuwa har shekara bakwai. Mu a likitance akwai binciken kimiyya da ya tabbatar mana da cewa an fi so a yi idan yaro na kasa da shekara guda saboda jinya ta fi sauki kuma a lokacin allurar barci da magungunan kashe zogi suna tasiri, ba kamar yadda sai sun girma ba.

Kawai dai idan aka samu matsalar halitta ce a wasu yaran kamar irin matsalar hudar wurin fitsari, shi ne za a iya ganin cewa mukan ce a jinkirta sai yaro ya yi kwari, wato kada a yi shayi sai fatar wurin ta rika don a gyara wurin a hada da shayin duka.