Search
Subscribe
Amsoshin tambayoyi

Amsoshin tambayoyi

Ko akwai maganin warkarwa na farfadiya ba na sha kullum ba? Domin su wadannan magungunan asibitin idan aka bar sha na ’yan kwanaki sai farfadiyar ta dawo.

Daga Lawal Yawale

Amsa: A likitance akwai nau’in ciwon farfadiya kashi-kashi, akwai nau’in da idan ta samu yaro yana girma ciwon na tafiya, akwai kuma nau’uka masu karfin da ba sa tafiya ko yaro ya girma, wanda ke nan wannan nau’i magunguna ne kadai ke iya hana tashin ciwon komi girman mutum. Da ya tsayar da magani matsalar za ta dawo. To watakila irin wannan ne nau’i. Don haka ke nan ga masu irin wannan dole sai sun rungumi magani kamar abinci.

 

Yarinya ce ba ta cin abinci sai rama, idan aka takura ta aka ba ta sai ta amayo shi. Shi ne muke neman shawara.

Daga Maman Safwan

Amsa: Yawanci yara abin da kan hana su cin abinci shi ne kawai rashin sha’awa. In dai ba ciwo ne da yaro ba to tabbas akwai abinda ya fi sha’awa. Don haka in dai kin san abincin da ta fi sha’awa dole ne a rika daurewa jefi-jefi ana nemowa. Idan kuma ba ta da sha’awar kowane nau’i na abinci da kika sani to akwai matsala, watakila akwai alamun wani ciwo a jikinta. Domin akwai cututtukan da a cikin alamominsu har da rashin sha’awar kowane irin abinci da amayarwa idan an bayar da kuma rama. Don haka idan wannan ne halin da take ciki to sai kun je asibiti an gano ko akwai ciwo, kada ciwon yunwa na tamowa ya zo kuma ya shige ta.

 

Da gaske ne irin ciwon hakorin nan da yara kan yi yana iya kawo ciwon kunne?

Daga Aliyu Abdullahi Nguru

Amsa: E, ko a manya ma idan hakora na ciwo kunne zai iya amsawa, amma ba wai haka na nufin kunnen ya kamu da wani ciwo ba ne, a’a amo ne daga hakoran zuwa kunne, saboda ita jijiyar laka ta fuska kamar tsintsiya take, ta bazu har kusa da kunne da kumatu da saman ido da wajen baki, don haka ne idan wani ciwo ya shafi tsinke daya na jijiyar za a iya jin amshin zogi a wani wuri daban da inda asalin ciwon yake. Don haka da an yi maganin ciwon hakorin zogin kunnen zai tafi da kanshi.

 

Wane magani zan sha da zai mayar min da fatar jikina luwai-luwai?

Daga Mikidat Ayomide, Abuja

Amsa: A’a haba, ’yan Abuja ai ba sai sun sha wasu magunguna ba fatarsu take kyau da sheki. Tun da kwanciyar hankali, da cin mai kyau, da shan mai kyau, da kwanciya a wuri mai kyau, da wanka da sabulu mai kyau, da shafa mai mai kyau, su kadai sun isa su gyara maki fata ba sai kin nemi wasu kwayoyi ba, kuma da dama ’yan Abuja ana musu zaton suna samun wannan gatan.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin