✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

AMSOSHIN TAMBAYOYI

Ni abin da ke damuna shi ne yawan faduwar gaba ko kuma kirjina ya yi ta mini zafi, sai na ke amfani da maganin basoprin.…

Ni abin da ke damuna shi ne yawan faduwar gaba ko kuma kirjina ya yi ta mini zafi, sai na ke amfani da maganin basoprin. Ko hakan ya dace?

Daga Bala Iddo, Lagos

 

Amsa: Idan an tantance matsalarka a Asibiti ne aka ba ka wannan magani shi ke nan, amma idan da ka kake shan sa to a’a sam hakan bai dace ba in dai ba a tantance mene ne takamaimai matsalarka ba ka fara shan maganin.

 

Ni ma ina shan wasu magungunan kashe zogi saboda matsanancin ciwon hakori. To ina yawan jin zafin kirji. Ko hakan matsala ce? Ina mafita?

Daga S. I. Danjanku

 

Amsa: E, yana daga cikin illolin shan magungunan kashe zogi samun ciwon kirji, wanda ke nufin idan ba a yi hankali ba zai iya kai wa a samu ciwon gyambon ciki. Mafita ita ce a nemi Likitan hakori ya yi ciko ko ya cire hakorin ko ya ba da shawarar abin da ya kamata.

 

Wai me ke kawo cikina ya rika kugi da kuka kulululu haka?

Daga Murjana A.

 

Amsa: Cikin kowa yakan yi kugi da kuka jefi-jefi, alama ce ta cewa hanjin na aiki sosai, kuma na wasu ya fi na wasu, domin wasu sai na kusa sun ji karar, a wasu kuma sai dai su kadai su ji. Don haka ba wata damuwa in dai gudawa da kullewar ciki ba su biyo bayan kugin ba. Idan kuma gudawa ko ciwon ciki na biyo baya to lallai akwai matsala sai an dangana ga asibiti.

 

A tashar ‘Youtube’ na ga an nuna cewa dakakken tattasai idan aka sha a ruwa yana maganin ciwon daji. To idan mutum ya dangwala kosai a ciki ya ci hakan ya yi ko sai dole a ruwan? Kuma mene ne amfanin kayan miya ne ma takamaimai a jikin dan Adam?

Daga Hassan Shehu Aliyu, Zaria

 

Amsa: Ba fa komai aka gani a yanar gizo ake yadda da shi ba. Kamata ya yi ka tambayi sahihancin bayanin ba ka yarda da shi ba, har ka fara tunanin yadda za a gwada. Watakila kuma ba ka fahimci abin da suka fada sosai ba. Domin babu kanshin gaskiya a maganar cewa kayan miya za su iya maganin ciwon daji. Idan ta riga ta kama mutum magungunan da aka sani na warkar da ita ko a Asibiti ma wahala suke ballantana a gari. Watakila cewa suka yi za a iya kiyaye kamuwa daga ciwon daji idan ana yawan cin kayan miya irinsu tattasai saboda watakila suna da sinadaran kariya, ba na waraka ba.

 

Na kasance idan na zauna a wuri na dade kafata takan rike ta rika ciwo na kasa tafiya. Mutane sun ce mini sanyi ne. Wace hanya ya kamata na bi wajen magance ko kiyaye wannan matsala?

Daga Muhammad Maishanu, Lagos

 

Amsa: Da farko dai yana da kyau ka san cewa kowa zai iya samun rikewar kafafu idan ya zauna a wuri ya dade fiye da awa bai motsa ba. Don haka ne ma muke ba da shawara akan rage yawan zama a wuri daya a dade ba a tashi an dan taka ba, domin hakan ba ciwon kafa ba har bugun jini a huhu, abin da mu ke kira pulmonary embolism zai iya kawowa musamman a mutane masu kiba. Za ka ji a tafiyar Jirgi ko a tafiyar Mota mai tsawo wasu ana ce masu ka da su zauna su dade sosai na fiye da awa biyu ba su motsa kafa ko sun tashi sun zagaya ba, domin kiyaye irin wannan matsala.

Don haka watakila ba ciwon sanyin kashi ba ne, dadewar da kake yi a wurin zama ne ke jawo maka wannan matsala. Yawan motsa jiki da rashin dadewa wajen wurin zama kenan zai iya kiyaye irin wannan matsala da kake samu. Akwai motsa jiki irin na zaune da dama da za ka iya koya idan dole zaman zaune ya kama ka na tsawon awoyi.

 

Wai shin mene ne yake kawo ciwon tsara? Tsara na ke ciwo da dadewa na je Asibiti amma ba sauki.

Daga Nura Bodinga

 

Amsa: Ku a Sakkwatanci tsara na nufin tsakar gadon baya ko? To idan haka ne akwai abubuwa da dama masu kawo matsalar ciwon baya, tun daga rashin wasu sinadarai da kashi kan bukata irinsu bitaman na rukunin D da B da sinadarin calcium da sauransu. Wasu lokuta kuma matsalar zamewa ko gocewar kashin gadon baya ne, kamar idan an samu faduwa ko buguwa a hadari. Wani lokaci ma kiba na iya sa wa. Ko kuma haka kawai kashin ya lauye ya yi gefe ko ya yi ciki. Wasu kwayoyin cutuka ma irinsu kwayar tarin TB sukan iya shiga kashi, haka nan ma masu ciwon sikila sukan iya samun yawan ciwon tsara.

Don haka idan ka samu Likitan kashi a babban Asibiti ka masa bayani zai duba ka ya bukaci gwaje-gwaje da hotuna domin gano dalili. Kusan ya kamata ka san cewa duk Asibitin da ka ga ka je matsala na cinka amma sun kasa gano dalili duk da an yi bincike to da sauransu wurin kayan aiki.

 

Wai shin cin kwaron nan na gwazarma da wasu ke yi yana da wata fa’ida ga lafiya? Wai da gaske magani ce?

Daga Mustapha Habeeb, Kano

 

Amsa: Idan ma magani ce to ba a likitancin kimiyya ba, sai dai ko a likitancin wasu garuruwan kamar na irin kasar Sin, su suke magani da ita. Gwazarma ‘ya’yan wasu kwari ne irinsu Buzuzu da kungurguma wadanda idan suka kyankyashe daga kwai suke zama gwazarma kafin su zama manyan kwari. Ko a kasar nan wasu al’adu ma ai suna cin kwari ko? Don haka idan suka ci ‘ya’yan kwari ba mamaki.