✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi: A shekara  nawa ake daina tsawo?

A shekara nawa mutum yake daina tsayi? Domin ni ina matukar so in ga na kara tsayi Daga Abdulmumin Y. Tarauni Amsa: Wannan yana danganta ne…

A shekara nawa mutum yake daina tsayi? Domin ni ina matukar so in ga na kara tsayi

Daga Abdulmumin Y. Tarauni

Amsa: Wannan yana danganta ne da abubuwa uku, wato gado, nau’in abinci da muhalli. Yara na girma da kara tsayi daga kwasusuwansu ne daidai da kwayoyin halittu na gado na iyaye da kakanni da cimaka da kuma yanayi da muhallin da aka samu tasowa cikinsa. Bincike ya nuna yara masu iyaye masu tsayi sukan yi tsayi su ma sosai, wadanda ma akan ba su cimaka mai dauke da sinadaran abinci masu gina jiki wato protein, su ma sukan yi tsayi sosai. Haka nan wadanda suka taso a wuri mai ni’ima da rashin tashin hankali su ma suna tsayi sosai. To a wadanne shekaru ne tsayin ke tsayawa?

Komai gadon mutum, komain cin abincinsa, kuma ko a wane irin yanayi ya taso cikinsa akwai lokacin da shekaru za su zo a daina tsayi. Bincike daban-daban na masana ya nuna cewa yawanci a maza daga shekara 18 zuwa 21 ne. A mata kuma daga 16 zuwa 19 sun gama tsayinsu. Duk wani girman jiki da za a samu bayan wannan lokaci a fadi ne ba a tsayi ba. Ba za a iya cewa kowa na duniya haka zai kasance ba, akwai daidaiku da za su iya wuce haka, wato bayan wadannan shekaru su kara tsayi, musamman ma idan jikinsu na sakin sinadarin growth hormone ba bisa ka’ida ba, amma dai kamar yadda aka ce, sai sa’a.

Don haka ke nan idan ka riga ka kai shekara 21 kusan ba abin da za a iya maka. Idan kuma ba kai kai shekara 21 ba, to yana da kyau ka dage da cin abinci mai gina jiki na protein da yawan motsa jiki da kuma yawan samun kwanciyar hankali. Idan kana haka za ka ga tsayinka yana saurin karuwa. Wannan haka yake in dai kana da gadon tsayi. Amma idan ka fi gadon gajarta fiye da tsayi, kada ka sa rai za ka kara tsayi sosai.

 

Ko buguwa a gwiwa sakamakon hadari zai iya hana mutum tsayi?

Daga Abdullahi Muhammad, Darmanawa

Amsa: Eh, kwarai wanda ya samu buguwa ko karaya a kashi a kuruciya zai iya samun nakasu a wurin cikar tsayinsa. Kai ko da ma da girmansa aka samu buguwar. Ai a wasu lokuta za ka ga idan mutum ya karye ko an dora shi sai an yi masa takalmi na musamman a kafar da ya karye domin ta kamo daya mai lafiyar.

 

Ni ma ciwon kafa ne da ni tunda na tashi nake da shi. To har yanzu yakan tashi ya rika yi mini zafi domin ko tabawa ba na so a yi. Zan iya shan maganin rage zogi? Likita ya ce sai an yi mini aiki. Ina neman karin bayani

Daga Maryam Usman Mahmoud

Amsa: Eh, ki yarda a yi aikin domin da alama kwayoyin cuta sun shiga cikin kashin, sai an yi aiki an wanke inda suke kafin ta warke gaba daya, kada kamar wasa karamar magana ta zama babba, wato kafa ta zo ta rube.

 

Me ya sa aka fi takura wa masu magungunan kyamis fiye da masu magungunan gargajiya? Ko me ya sa aka fi sa ido a kan masu kyamis?

Daga Hassan Ibrahim Warji

Amsa: Ka san ai kasarmu har yanzu ba mu ci gaba ba sosai. Shi ya sa har yanzu ake sa mu cikin jerin kasashe masu tasowa. Hukumar da wannan abu ya shafa ita ce Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC). An kirkiri wannan hukuma ce a matsayin kwaikwayo daga irinta ta kasar Amurka (FDA). To su a can Amurka, ba sa bari duk irin wadannan magunguna na gargajiya su shiga kasuwa ba tare da an kayyade an tabbatar da illa ko alfanunsu ba ga jama’a. To mu a nan kamar yadda ka lura kusan haka ne, an fi sa ido a kan magungunan kyamis na nasara fiye da na gargajiya, watakila ko domin har yanzu hukumar ba ta da isassun ma’aikatan da za su hada dukan ayyukan ne, oho.

 

Shi samun yawan shassheka matsala ce?

Daga Ahmed B.G.W

Amsa: Eh, idan na fahimce ka shassheka kamar karshen kuka ke nan ko? Domin idan yara suka gama kuka suna shassheka, amma idan babba yana yi ba tare da wani dalili na kuka ko bakin ciki ba, za a iya alakanta shi da shakuwa, kuma mu yawan shakuwa a likitance matsala ce. Don haka a takaice dai zai iya zama matsala yana da kyau a tuntubi likita ido-da-ido

 

Me ya sa a wasu lokuta nake jin zafi a kirjina da awazona? Kamar ana sukana?

Daga I. Khalifa Kwantagora

Amsa: Da alama akwai matsala a kirjin. Sai ka samu likita ya duba ka ya tabbatar

 

Me ke kawo a rika ganin baki-baki a kwayar idon mutum wajen farin?

Daga Garzali Ibrahim Darmanawa

Amsa: A’ a wannan in dai babu alamu na rashi ko canjin yanayin ganin mutum za a iya cewa ba komai saboda kusan ba wanda za a ce idanunsa fari tar suke. Akwai digo kwayoyin halittu masu sa fata duhu da magudanan jini da jijiyoyi da ma watakila kura da sauransu. Mun fi alakanta matsalar da ciwo idan suka yi ja ko ruwan dorawa

 

Me ke sa mutum tara miyau ko hadiyarsa idan ya ga abinci a gabansa?

Daga Dantanin Yalwa

Amsa: Kwakwalwa ce ke raya wa wata ’yar halitta da ke samar da miyau wadda ke baki da ake kira salibary gland, cewa a saki miyau da yawa ga abinci ya sauka. Shi yakan sa wadansu sakin miyau da yawan  hadiyarsa tun kafin ma a sauke. Wadansu ma kanshin abincin kawai za su ji kwakwalwar tasu ta raya musu haka su fara sarrafawa da hadiyar miyau.

 

Ko shan lemon tsami na da matsala ga mai ciwon suga?

Daga A.B.M

Amsa: Masu suga suka ma sha lemon zaki ballantana na tsami. Ba wata matsala in dai yana shan magungunansa yadda ya kamata, kuma sugarsa idan an auna tana daidai ba ta sama sosai. Shi lemon tsami ai ba suga a ciki sosai kamar na lemon zaki.