✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi: Cututtukan da takardun kudi kan iya yadawa

Likita shin akwai wasu cututtuka da za mu iya dauka a jikin takardun kudade? Daga Nasiru Kainuwa Hadeja Amsa: Eh, kwarai kuwa akwai. Kudin da…

Likita shin akwai wasu cututtuka da za mu iya dauka a jikin takardun kudade?

Daga Nasiru Kainuwa Hadeja

Amsa: Eh, kwarai kuwa akwai. Kudin da mukan yi amfani da su za su iya kasancewa kunshe da wasu kwayoyin cututtuka (na bakteriya da fungus da birus) masu iya yaduwa a cikin al’umma, wadanda ba a iya ganinsu da ido sai da tabarau na kimiyya. Wadannan kwayoyi da yawansu sukan hau su mutu amma wasu za su iya zama a kansu su dade ta yadda za su yi ta yawo a tsakanin mutanen da suka yi mu’amala da kudaden, wato wannan ya taba ya kwasa ya ba wancan, wancan ya sa wa wancan, duk kuma asalinsu daga jikin takardar kudi ko kwandala aka kwasa. Kai bincike ma ya nuna cewa wasu takardun kudin yadda ka san bakin shadda haka suke da kazanta tunda kowa zai iya taba su tun daga mai ba da kudi a banki har zuwa mabaraci, zuwa mai kwasar shara, kuma ba wankesu ake ba.

 

Ta yaya ake yada kwayoyin cututtukan? Mutum ne zai zaga ya fito bai wanke hannaye ba, ko ya yi tari da atishawa cikin hannunsa bai wanke ba, kawai sai ya je sayen wani abu ya zaro kudi da kazamin hannunsa ya shafa a jikin takardar (ta hanyar kirgawa). Daga nan sai mai sayar da abubuwa wanda aka ba kudin ya karba, shi ma sai ya kirga, a wasu lokuta ma yana kirgawa yana sa dan yatsar da yake kirga takardun a baki, wai shi yana jika su domin su yi dadin kirge, bai sani ba cewa wannan kai hannu bakin da ya yi ya zuba kwayoyin cuta a baki, kuma hadiye su zai yi nan take. Wadanda bai sa a bakinsa ba, sai dai ya yaba a kan wasu kudaden ya jefa a akurki ko aljihu. Bincike ya nuna cewa wadannan kwayoyin cuta sukan iya daukar akalla kwana uku, ko wata biyu  a mafi tsawon lokaci, suna nan a kan takardar kudi ba su mutu ba. Ta haka ake yada su. Bincike ya kara nuna kananan takardun kudi (kamar Naira biyar zuwa hamsin) da tsoffin kudi su suka fi kwasa da yada wadannan kwayoyi.

Kwayoyin cututtukan da za a iya kwasa daga jikin kudi (wadanda aka gani kuru-kuru a jikin kudaden) sun hada da kwayoyi masu sa tari da mura da masu sa amai da gudawa da masu sa kuraje ko maruru da masu sa cutar zafin fitsari da masu sa tarin TB da masu sa ciwon sankarau da masu sa ciwon gyambon ciki da sauransu. Su kuma a kasashe irin su Amurka da Ingila, ban da wadannan kwayoyin an gano kusan kashi 90 cikin 100 na kowace takardar kudadensu suna dauke da birbishin hodar Iblis, wadda za ta iya kunsa ta kuma yada kwayar cuta mai sa ciwon hanta na hepatitis C.

Hanyoyin da za a bi a kare kai daga kwasar wadannan cututtuka sun hada da:

1. Yawan wanke hannaye da ruwa da sabulu idan yi amfani da makewayi

2. Yawan wanke hannaye da ruwa da sabulu idan aka yi atishawa ko tari ko aka face majina

3. Yawan wanke hannaye da ruwa da sabulu idan aka yi mu’amala da takardun kudi

4. Wuraren da ake sayar da abinci dole su ware mai aikin karbar kudi daban wanda ba ya taba abinci ko kwanukan abinci sai dai kudi kawai. Al’adar nan ta cewa mai zuba abinci ita/shi ne kuma da karbar kudi ya kamata ta kau.

5. Za a ga masu yawan mu’amala da takardun kudi na banki sai sun lullube hannayensu da safa, sun kuma rufe hancinsu da takunkumi domin kada su kwashi wadannan cutuka. Don haka ke nan masu aikin kirga kudi a kasuwanni da shaguna kusan su ma suna bukatar daukar irin wannan mataki.

6. Rage amfani da takardun kudi ta hanyar yin amfani da katin biya na banki zai sa mutum ya rage kwasar wadannan kwayoyin cuta. Duk da haka idan aka lura a wurin biya na na’ura wato POS akan bukaci mutum ya danna lambobin sirri. To a wurin danna lambobin nan ma ana iya kwasar kwayoyin cuta, ta yadda idan aka gama yana da kyau a tsabtace hannaye

7. Bincike ya nuna cewa yin amfani da takardun kudi na roba, ba na takarda ba, kamar yadda aka yi a kwanakin baya aka canja wasu takardu zuwa takardun roba, shi ma yakan hana kwayoyin cuta makalewa a jikin kudi.

8. A kasa kamar Japan an ruwaito cewa wasu na’urorin ba da kudade na ATM suna tsabtace kudi kafin su sake su. Wata hanya ce aka fito da ita a jikin wannan nau’ra ta yadda sai ta gasa takardun kudi sosai sun huce kafin ta sakar wa mutane. Wannan gashi yakan kashe kwayoyin cutar da ke jikin kudin

 

Ko me ke kawo ciwon diddige? Yanzu mako uku ke nan ina fama da ciwon kuma karuwa yake

Daga A’isha Batsari da Auwal Shu’aibu

Amsa: Akan samu ciwon diddige tafin kafa a manya, wanda a likitance muke kira (plantar fascitis) daga lokaci zuwa lokaci. Haka kawai tafin kafa ta can wajen duga-dugi zai fara zogi musamman da safe, sai da rana ya lafa. Wadansu masana suna ganin nauyin jiki da yawan gurzar kafa a wajen tafiyar kafa ke sa mayanin fatar wurin ta rika ciwo.

’Yan magungunan kashe zogi na sha da na shafawa za su taimaka na dan wani lokaci. Amma idan suka ki aiki sai an je an ba da magunguna masu karfi, an kuma yi gwaje-gwaje an tabbatar ba ciwon sanyin kashi ba ne.

 

Shin yin wanka da sabulu mai zuma a ciki zai iya yin illa? Domin na ga kamar yana sa ni fari

Daga Abdulkarim Muhammad, Zamfara

Amsa: A’a in dai zuma ce kadai babu kayan bleaching a jiki ba komai, domin ai zuma magani ne sosai ko a likitancin Nasara. Amma idan ka duba takardar maganin ka ga cewa ban da zuma akwai wasu sinadarai da ba ka yarda da su ba, to na bogi ne sabulun. Sinadarai irin su mercury da hydrokuinone da irin masu karewa da -one ko -iol.