✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin Tambayoyi Daban-Daban

Na ji ka ce yawan shan magunguna na tsawon lokaci na iya bata wa mutum koda ko hanta. To masu matsalar ciwon zamani fa su…

Na ji ka ce yawan shan magunguna na tsawon lokaci na iya bata wa mutum koda ko hanta. To masu matsalar ciwon zamani fa su ma magungunansu kan iya jawo haka?

Daga Sulaiman Sabon Layi

 

Amsa: Eh, ai a rubutun an fada cewa duk masu wani ciwo na tsawon lokaci da kuma suke shan magani na tsawon lokaci suna cikin hadarin samun bacin koda ko hanta daga magungunan, inda muka kawo misali da masu hawan jini da masu ciwon suga da ke kan magani na mutu-ka-raba. Ba su kadai ba duk magungunan cututtuka da akan sha na tsawon lokaci suna iya kawo haka. Abin da akan yi a asibiti domin kiyaye hakan muka ce shi ne yawan awon lafiyar hanta da ta koda duk bayan ’yan watanni. Da an ga alamun matsala sai a duba a ga magungunan da za su iya sa wannan matsala sai a tsayar da su a canja da wasu. Shi ya sa za a ga ana yawan rubuta wa masu shan magunguna na tsawon lokaci awo duk bayan ’yan watanni. Ba bata kudin marar lafiya ba ne, binciken lafiyar muhimman sassan jiki ake.

 

Ko shan baure yana da amfani ga lafiya, ko ba ya da matsala misali idan mutum yana yawan shansa a kullum?

Daga Nura Mai Apple Gusau

 

Amsa: Baure yana da amfani ga lafiya, akwai sinadarai na ma’adinai da na bitaman da dama a cikinsa. Amma da alama kai bako ne a wannan fili domin da za ka san ba a son a ce an nace wa wani abinci a ce kullum sai an ci ko an sha, ba tsarin kiwon lafiya ba ne. Babu abinci ko abin sha ko ’ya’yan itatuwa guda daya mai kunshe da dukanin sinadarai da bitaman da jiki ke bukata, don haka ne ake son cancanjawa. Yau idan ka ci baure, gobe ka ci tuffa, gata ka ci dabino misali. Haka ake yi a samu albarkacin sinadaran cikin kowane.

Fatar jikina ce ke tattarewa take kankamewa kamar ta tsoffi kuma ba wasu shekaru ne da ni ba. Me ya kamata in yi?

Daga Mustapha A.A

 

Amsa: To ko ba ka samun abinci da kayan marmari hadaddu masu gina jiki ne sosai (balanced diet)? Domin idan mutum na cin abinci da ’ya’yan itatuwa iri-iri kullum ba sai ya bata lokacinsa a neman kayan shafe-shafe ba. Sinadaran abinci da suka fi gina fata wato suka fi amfani ga fata su ne sinadarin protein da bitamin na ajin C. Sinadarin protein shi ne ya fi tsada kuma ya fi wahalar samu a irin kasashenmu, domin mutum idan ba hali ne da shi ba ba zai iya samun sinadaran protein isassshe a abincinsa ba a rana.

 

Shin shafa zuma a fuska da wasu sukan yi ko yana da wata fa’ida ce?

Daga Hassana Mika’il, Kaduna

 

Amsa: Eh, wadansu sun ce tana gyara fata, saboda wasu sinadaran da ke cikinta masu tsane datti da tsane tsofaffin halittun fata da kuma taimakawa wajen rage wa fatar tattarewa yadda zai rage nuna saurin tsufa. Amma dai duka aikin zuma ba zai kai irin na sindarin protein da ke cikin abinci ba, wanda shi ke samar da ainihin gundarin sinadarin hada fatar, wato sinadarin collagen.

 

Ko yawan cire dattin kunne ba zai yi illa ga kunnen ba?

Daga Aliyu Danbirni, Zariya

 

Amsa: In dai ba an leka an ce maka tabbas kunnenka fal yake da datti ba, to yawan cirewar zai iya jawo illa. Amma ya kamata ka san bambanci tsakanin dattin kunne da kuma man da fatar kunne kan samar domin tsane dattin. Wato akwai bambanci. Shi man kunne za a gan shi launin lemo, wanda in dai ba ya damunka ka kyale shi ya yi aikinsa, amma idan man ya hadu da datti za a ga ya yi duhu ya dawo ruwan kasa-kasa.

To ba laifi idan wannan mai ya zama ruwan kasa-kasa, ya kuma jawo yawan kaikayi da ciwon kunnen a goge shi, domin a sarrafa wani sabo ya sake tsane wani dattin. Amma dai in an zo gogewar, bakin kunnen kawai ake gogewa, misali idan an zo wanka a dan murza sabulu a yatsa a sa bakin kunnen kawai a wanko, a dauraye, kada a shiga da wani abu kamar tsinken auduga ya je ya jawo matsala. Idan kuma ta kama sai an goge can ciki, wato kaikayin ko zafin a can ciki ne, an fi so a je wurin likita ya duba ya ga ko maganin digawa na tsane datti zai bayar, ko kuwa a’a dattin ya taru ya yi yawa ya toshe kunnen sai an kai ga aikin saka kayan aiki an ciro.

 

Na ji wani masani yana cewa idan aka fito daga bayan gida idan ba a sa kasa ko sabulu mai kashe kwayoyin cuta irin su datal aka wanke hannu ba, to kwayoyin cuta a hannaye ba za su mutu ba. Shi ne nake tambaya ko akwai wani sabulu da ke da irin wadannan sinadarai na kashe kwayoyin cuta?

Daga Musa A.B

 

Amsa: Eh, ai da ma ba wai manufar a kashe dukan kwayoyin cuta da ke hannaye ba ne, a’a manufar ita ce a rage yawansu. Ba kuma dole ne sai an kashe su ba, idan aka wanke da sabulu to su kwayoyin cuta suna bin kumfar su kwaranye. Abin da kawai ake bukata ke nan su ragu. Ba yadda za ka iya wanke ko kashe duka kwayoyin cutar hannayenka, tun da akwai wadanda da’iman suna nan, wadanda ake kira normal flora, wadanda su ba su kawo mana cututtuka.