✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi daban-daban a kiwon lafiya

Na ga rubutunka game da kwari masu illa a lafiya, shin da gaske ne ban da cututtukan da ka lissafa, sauro ma na iya sa…

Na ga rubutunka game da kwari masu illa a lafiya, shin da gaske ne ban da cututtukan da ka lissafa, sauro ma na iya sa ciwon tundurmi na Elephantiasis?

Daga Saleh M Bala Joda

Amsa: Kwarai, ban da kwaron filfilwa na Blackfly mai sa ciwon tundurmi na Filariasis, sauro ma kan iya sa ciwon tundurmi na Elephantiasis. Wato duka matsalar kusan iri daya ce, sai dai kwayoyin cutar ne daban-daban, kamar dai yadda kwayoyin cuta daban-daban kan sa gudawa iri daya.

Sauron ne ke dauko kwayar filaria shi kuma kwaron filfilwa ke dauko kwayar Onchocerca. Amma ka san sauro nau’i-nau’i ne akwai Culed akwai Anopheles, akwai Aedes da sauransu. Shi Culed shi ne mai dauka da yada kwayar ciwon tundurmi, shi kuma Aedes shi ne yake dauka ya yada cutar shawara ta Yellow Fever. Shi kuma Anopheles shi ne mai yada kwayar cutar da ke sa zazzavin cizon sauro ta Malaria. Kai an ma tava samun wani dan gudun hijira da ya je Amurka daga kasar Saliyo mai dauke da duka kwayoyin cuta na Malaria da Filaria da Onchocerca duka ukun a jininsa, wato duka kwarin nan sun ciccije shi ke nan a can kasar da ya baro.

Shi kwaron filfilwa a gefen kogi mai gudu aka fi ganinsa. Yana kama da sauro amma shi baki ne kamar kuda. Shi ya sa ake son mutane masu yawan zuwa bakin rafi su rika shafa man kiyaye cizon kwari don kada su rika kwasar irin wadannan cututtuka.

Ni ina so a kara mini bayani ne a kan alamomin ciwon suga.

Daga Atama Anthony, Nassarawa

Amsa: Alamomin ciwon suga su ne rama da yawan fitsari da yawan shan ruwa. Ita rama dalilinta shi ne saboda jiki yana kona maiko maimakon suga, wato ga sugan a jini amma jiki ba ya iya amfani da shi sai dai maiko da sinadarin Protein. Yawan shan ruwa saboda yawan fitsari ne. Yawan fitsari dalilinsa shi ne suga ya shiga koda, wanda idan hakan ta faru koda za ta yi ta fitar da shi tare da fitsari. Yawan fitsari a kimiyyance na nufin fitsari fiye da lita 3 a rana amma ana iya kwatanta shi da cewa mutumin da ke fitsari da rana sau hudu ya dawo yana yi sau takwas ko goma, wato ya nunka, da dare kuma idan mutum na fitsari sau daya a dare ya dawo yana yi sau biyu ko uku. A mafi yawan lokuta amma ba wasu alamu da mutum zai ji sai an je an auna jini ko fitsari kawai a ga suga.

 

Ko me ke sa fitsarin jini da zafin fitsari?

Daga Hafizu M.

Amsa: Su kuma wadannan alamu sun fi nuni da shigar kwayoyin cuta mafitsara. Mai samun irin alamun ke nan sai ya je an bincika ko hakan ne.

 

Ni an mini aune-aunen jini an ga maiko ya yi yawa an ce in rage abinci mai maiko. To na fara ragewa amma har yanzu dai ina fargaba. Ko me ya kamata na yi?

Daga Mustapha KGS

Amsa: To fargabar me kuma tun da an ce ka rage kuma ka rage? Idan dai da hali yana da kyau ba ragewa kadai ba, ka canza man da ake maka girki da shi zuwa marasa nauyi kamar man zaitun da man fulawar Sunflower ko man Canola da man ridi da man fiya da sauransu.

 

Ni kuma ina yawan kin cin abinci domin tumbina ya ragu. Ko hakan zai iya sa mini matsala?

Daga Ahmadu Ibrahim

Amsa: A’a, ba wata matsala. Ai kamar mai azumi ne irin na jefi-jefi din nan, ga lada ga lafiya.

 

Ko shin da gaske ne iskar gas da ke cikin lemon kwalba na iya sa katon tumbi?

Daga Ibrahim Hibban

Amsa: A’a, iskar gas ta lemon kwalba ba za ta sa tumbi ba sai dai ta kumbura ciki, amma da an yi gyatsa ake fitar da gas din. Shi ya sa ake yawan gyatsa idan aka sha lemon kwalba mai gas.

 

Shin yawan shan madara a kullum ba shi da wata matsala?

Daga Yusuf A.

Amsa: Wannan tambaya ai mun yi maganarta a kwanan baya, inda muka ce idan madarar sabuwa ce wato fresh ba matsala idan ana sha kullum ko da kofi daya ne, amma idan sarrafaffiya ce ta kamfani, ba kullum ya kamata a sha ba.

 

Ni kuma na cika yin barcin rana ne, domin a kullum sai na yi shi. Shin hakan na da matsala?

Daga Musa M.K

Amsa: A’a, ba matsala in dai ba wai ka mai da barcin ranar naka ya fi na dare yawa ba.

 

Ni kuma wuya ne ke yawan kagewa sai na jijjiga yake saki, ina mafita?

Daga Saleh Aliyu Kankiya

Amsa: Sai ka rika yawan motsa jiki, domin yawan motsa jikin zai iya sakin duk wasu jijiyoyi na jikin mutum da ke yawan rikewa.

 

Ni ma tun ina yaro hannayena ke yawan kumburi lokutan zafi amma ba wani ciwo suke ba, ko wata matsala ce?

Daga Adamu Dankwambo.

Amsa: E, to sai an ga irin kumburin a tabbatar ko mai illa ne ko maras illa. Amma dai da alama ba wata matsala ba ce sosai tun da ka ce tun kana karami abin yake. Da akwai wata matsala da tuni ta bayyana tare da kumburin. Duk da haka dai yana da kyau likita ya duba hannayen.

 

Ina fama da ciwon olsa har ba na barci. Shin ciwon olsa na iya hana barci dama?

Daga Mujittaba Ibrahim

Amsa: Kwarai kuwa, zogin ciki da ciwon olsa ke kawowa yana hana barci sosai ma, domin a lokuta da dama ya ma fi tashi da dare. Amma da ka je asibiti an duba an tabbatar olsar ce aka ba ka magunguna ka fara sha, a daren za ka fara jin canji, wato a daren za ka fara samun lafiyayyen barci.